← Book details Maaikaciyar Gomnati Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 57

Sashe 15

Maaikaciyar Gomnati Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tsorace ta karasa kusa dashi sir omar bacci ka kasa yi ne?harara ya watsa mata,ki daina zuwa wajena da dare ko ba komai sabo da gudun zargi,ba kya jin magana,ki daina sani magana fa tam,baki ta turo kai ya omar Allah baka San a ma gwaninta ba,me zanyi ma ina tunanin ko baka da lfy ne that's y na leko ka,OK tnx as u can see am fine sai ki tafi.

A shagwabe tana buga kafa to kayi bacci mana,dan ta tafi kawai sai omar ya kwanta a bed din,kafin ya mike kafarsa ta karasa ta hada leg nasa wuri daya ta mikar masa dasu,blanket taja ta rufa masa,a.c ta kara karfinta kana ta kashe masa light,ta fice zuwa dakinsu,da rarrafe ta shiga dan kar kaka taji tafiyarta, kwantawa tayi ta bar omar da tunaninta, yanda ta iya kula da mutum , wai bata ma auri mutum ba kenan ina ga ta aureshi.lallai mijinta ya more,sahar dinsa ya tuno wacce ko kallon arziki bata yi masa bare ta gyara masa kwanciya,wai a haka ta waye kuma yar boko,ga me talla nayin abinda ta gagara yi.

3days later omar yasa an kawowa suhaila sweet da snacks,wayoyinsa duka a flymode suke yana buga game a Palo,yayin da suhaila da ummi suka tafi kasuwa,iklas ta tafi kai kayan siyarwarsu makwafta,Omar bacci ne ya daukeshi a Palo,nan ya shiga mugayen mafarkansa kamar kullum,ya hada zufa,sai nishi yakeyi,iklas ce ta dawo da Sauri ta fada palon,tsugunawa tayi kasan kujerar da omar ke kwance,addua ta shiga tofa masa,falaq da nas,fatiha,ayatulkursiyyu,amanarrasulu,can taga ya daina mafarkin,dadi taji tace kai Ashe zan iya rukiyya ma in na dage,

Omar ne ya bude idonsa cike da bacci,tashi yayi zaune, a hankali ya bude idonsa tare da aza su kan kyakyawar fuskar iklas jinjina kai yayi,a ransa yana fadin wannan yarinya tana da nacin tsiya,ruwa ta dauko masa da sauri,a ransa yace ikon Allah kaga shishigi.

A gabansa ta tsugunaa tare da kallonsa cike da tausayawa, Jim kadan tace pls sir ka fada mana abinda ke damunka,inma baza ka fada min ba ka sanarwa ummi,in kuma baka son ummi ta sani ka fada min zan boye ma sirrinka,

Maybe zamu iya baka shawara,bai dace ka zauna haka ba,in kuma kaki to zan fadawa ummi mafarkan danaga kanayi da kuma time din Dana ganka a bakin shago,

Ido kawai ya zubamata yana kallonta har ta gama.Hannun iklas ya riko da hannu biyu ya zaunar da ita a kujera,kinyi alkawari in na fada miki baza ki fadawa kowa ba?da sauri iklas tace ae wlh sai in kai kace na fada,I mean sai da yardarka.Good muje tsakar gida to sai na fada miki,cike da zumudi tayi waje.

Farar kujera ta mika masa ya zauna itama haka,har sun dauki kusan 20mnt amma omar ya kasa bude baki yace komai,a zuciyarsa har ga Allah yana so ya fadawa wani matsalarsa ko zai bashi shawara amma ya kasa,daga lokacin da yayi niyyar sanarwa wani sai ya kasa furtawa.

Gajia iklas tayi da zama ta kirashi cike da sanyin murya,ya omar kayi shuru,kallonta ya kara yi ba tare da yace komai ba,sunyi wurin 30mnt amma yaki magana

Da kyar da sidin goshi ya cije ya furta bani da lfy a jikina,kamar ya?cewar iklas shuru yayi mata,haka ta hakura ta kyaleshi tunda ya kasa cewa komai,ita kuma bata gane me yake nufi ba.

Har ta mike zata wuce sai ta fasa ta dawo ta zauna inda ta tashi,tana zama ya zuba mata ido daga bisani yace zan fada miki next time not know,

Zuciyar omar kuwa ko ya yi niyyar fadi sai yaji a cikin ransa ana gargadinsa,zuciyarsa na tafarfasa,bakinsa yayi nauyi sai ya kasa fada.

Ya schl yanzu aji nawa kike?cewar omar dan kawai ya canja zance.suna hira su ummi suka dawo,ummi sai Murna takeyi ganin iklas tare da yaron kirki umaru.

Bangaren sahar kuwa duniya take tsikara da tsinke,babu ta inda bata cokalar duniya,ta manta ma da aure a kanta.
Mama da baffa sun yanke hukuncin zuwa gidan su sahar domin yin bikonta.

IKLAS na gidansu yau Sunday haka kawai taji yau ta tashi da masifa,ji tayi duniyar ta mata zafi,kamar ta kunnawa kanta wuta,kowa ta tsaneshi,magana kadan sai ta balbale mutum da masifa,

Ita kanta ta rasa dalili, mamakin kanta takeyi,omar na kallonta yanda takewa ummi da suhaila,da safe ma sai da ta Zane suhaila akan kallon film.iklas tana kwance ta baje a tabarma tsakar gida,omar na gyarawa suhaila farce yayinda ummi ke kitchen,haka kawai sukaji iklas a ta fashe da kuka wiwi. Kuka take sharba sosai tsakaninta da Allah,Har shidewa takeyi.

Kallonta omar yayi da sauri ke kumafa?lfy kikewa mutane kuka,da ganinta yasan akwai matsala,ummi kuwa fada ta kamayi me yasa zaka saurareta umaru tunda ta zama shashasha ba sai tayi ba,yarinyar nan tun safe take bala'i! haka kawai ki dauki halayyar banza da wofi,wlh bazan laminci iskanci ba.

Omar bai so fadan kaka ummi ba sai yaji haushi danme zatayiwa iklas fada,ai ruwa baya tsami banza tunda iklas tana da juria haka kawai baza tayi kuka ba

A fili yace ummi ki kyaleta maybe tana da damua ne,pls ya fada da kalar tausayi,hmm ai dama nasan kai umaru baka ganin laifinta biye mata kakeyi shi yasa take kara shagwaba.murmushi yayi ba tare da yace komai ba,sai gomnati da ya kafe da ido wacce take ta sheshekar kuka harma da jingina kanta ki?? Jikin bango tana ta yi.

Ranar haka ta kwana tana kunci da bakin ciki,washe gari Monday haka ma taje schl kowa cin ubansa takeyi ba mutunci...

11:30am dai dai suna class taji kamar danshi a kasanta ita kanta ji takeyi kamar acikin ruwa ta zauna,mikewa tayi tsaye ,Ai firgita tayi sosai,tabbas shine! jini ne,wato abinda takejin lbr period, ta fara itama,abin yazo kanta.

Kunya taji yau kam ba zaman schl dole ta tafi gida,hijab din wata Christian da bata sawa ta ara, ta daura saman rigarta ta rufe wurin daya bata mata uniform.

Omar zaune a Palo yana danna computer sanye cikin jallabiyya yar ubansu fara sai kamshi yakeyi,sumansa tayi yawa sosai sabo da ya jima baije an rage masa ita ba,sai ya kara kyau musamman da baya fita sai ya kara haske da sheki.

Ummi na gefensa suna ta labari,iklas ce ta shigo ko sallama babu ta wuce su ummi da omar fuuuuuuuu kamar zata tashi sama,su har sun tsoratama suna tunanin ko lfy.

Minti 2 tsakani ta kara fitowa daga room dinsu wannan karan har gudu ta hada dashi,waje tayi kofar gida wani shago ta shiga,pad ta siyo ta kara dawowa ta wuce su ummi,sai gata ta fito da Riga,da wasu tarkace a Leda,toilet ta fada karaf...... kararaf ta rufe kofar,suna jinta tana ta kwaramniya da botiki da ruwa.

Asmabaffa
[27/03, 17:48] Hassan Atk: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

35-40

By
Asmahbaffa

Ta kai wurin 1hr a toilet sannan ta fito,mikewa omar yayi ya leka ta window ya hango iklas tana shanya kaya,daure take da zani da hijab a jikinta,

Omar ganin iklas ta wanke uniform dinta ya sashi nazari ko lfy?amma dole sai ya tambayeta yaji meke faruwa da ita, Shanyar ta gama ta shigo palon da sallama, kaka ummi ce ta amsa tare da kallon iklas sama da kasa,ke kuma lfy?me ya sameki?

Kunya ce ta lullube iklas sai take ganin kamar kowa ya gane halin da take ciki,sai wani matse kafafu takeyi,su ummi fa sun kasa ganewa,wai me ya sameki ne iklas?ni yar nan na shigesu,

Umaru tayani figa uwar kishiya ta zama kaza,iklas kuwa daki tayi wucewarta ta bar ummi na sallallami,shiryawa tayi cikin dangalalliyar sabuwar doguwar rigarta fara me digon ja,rigar ma da kadan ta wuce gwiwarta,irin kayan da iklas tafi so kenan,

Turare ta shafa yau sosai a jikinta kamshi kawai takeyi ta ko ina,batayiwa kowa magana ba ta wuce kitchen,tea ta hada me kauri ta dawo Palo kusa da omar ta zauna a 3seater da yake zaune yana danna system.

Iklas Sam ta kasa zama,sai taji kamar period zai bata mata kayanta,shi yasa minti biyu uku sai ta mike tsaye ta waiga ta kalli bayanta,sai ta wayance kamar za tayi mika,

Omar ta gefen ido yake kallonta,ya kasa gano matsalar iklas yau,ummi kuwa tun tana masifa har ta kyale iklas.tsakar gida ta koma ta zauna a farar kujera ita kadai,wai nufinta ko da zata baci to ita kadai zata gani,

Ta kasa sakewa Sam ta takure waje daya yau ko akwalar wayarta ta kasa dauka bare tayi danne danne,Ummi ce ta kalli omar....umaru dan Allah jeka wurin yarinyar can kaji meke damunta,tunda naga ni baza ta fada min ba, watakil in anyi dace kai ta fada maka,

Sai da omar ya dauki 5mnt sannan ya fito waje ya nufi inda iklas ke zaune,ta hada kai da gwiwa sai hawaye takeyi tare da kallon gabas ta daga kai sama tana addua,fadi takeyi Allah ka yayemin wannan abun daya sameni,

Idan taji zubowar period zuuuuuu sai tace wayyyoooo Allah na,ta kara daga hannu tana ta zuba addua kan Allah ya yaye mata.tsawa omar ya daka mata! lfy kiki dami mutane,shuru tayi tana kwalla idonta yayi jajir,dake fa nake karki bari raina ya baci..

Kallonsa tayi amma kunya ta hanata fada masa meke damunta,kujera shima ya jawo ya zauna,suna zaune kowa yayi shuru,omar sai latsa wayarsa yakeyi,sun kai kusan 2hrs iklas ta mike ta shiga daki,fitowa tayi dauke da bakar Leda da abubuwa a ciki ta shige toilet,

Nan ma ta Dade sannan ta fito,ledace kulle a hannunta zata jefa a dustbin,fisge ledar omar yayi yana kokarin dubawa,ai iklas kukan kura tayi hade da kurma ihu ta makalkale omar,wayoo ledata dan girman Allah kar ka bude min,dan Allah kayi hakuri,gani tayi da gaske budewa zaiyi,kuka ta sa masa sosai tana rokonsa,pls ya omar karka bude min,

Omar kam ko kulata baiyi ba sai bala'in da ta haddasa masa a cikin jikinsa sanadiyyar Makalkaleshi da iklas tayi,amma ya rantse sai ya gani me take boye musu,ledar ya bude pad din da iklas ta cire ya gani,ai da Sauri ya rufe idonsa ya jefa mata ledar da sauri,

Iklas kam fashewa tayi da kukan takaici tare da zabgawa omar harara,4eye sukayi yaga yanda iklas ke harararsa,kallonta yayi ya saki shu'umin murmushin sa me rikita yan mata,
Chapter 15 · 0% Book details