← Book details Kuruciyar Minal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 80

Sashe 8

Kuruciyar Minal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tabawa dukkan maids da securities din gidan tausayi hatta sojojin domin duk rashin imanin wasu daga cikinsu sunsan Cewa minal ta horu

What so ever her fault is?

They all look at her pitifully, how young she is,yet going through all these sort of troubles

First was her hiding inside the Booth,

Then passing out due to lack of oxygen,

Then woken up by a chilled bottle water !

Then fear of being in an army's house as an offender!

Then the blood cascading from her hand making her clothes look like.........

Then the looks and presence of those horrible and terrifying,wicked dogs

The dogs chasing her is the biggest fear of her life

Her falling into the pool.
That one is called helplessness....................

Wata maid me suna tala (mai shara)ce ta sa'a tsumman a ruwan zafin ta matse sannan ta fara goge ma fiskanta

Wani nifashi taja kan ta sauke hawayen wahala suka fara zarya a idonta yadda kasan ruwan sama

Cikin 2 min harta jika hijabinta ta fara jika pillow da hawaye

Maid uku ne Dama a dakin da take daya da first aid,daya bowl din warm water,daya kuma tea and toasted bread

Dukkansu idonsu ya ciko da kwalla musamman da suka ga yadda minal take kuka

Wani mahaukacin atishawan data watsa ne ya dawo dasu saga duniyar da suka fada na halin da take ciki

Katrina wacce take baturiya itace first aider na gidan

First aid box din ta bude sannan ta ciro su cotton,dettol,spirit,iodine,and Bandage.

Treating ciwon ta fara aiko ana fara goge jinin minal tafara yarfa hannu
(nace tabdi tun ba'a saka alhaji dettol da oga iodine)

Yamutsa fiska take yadda kasan mai nakuda

Dettol aka saka domin ayi disinfecting aiko wani kara ta sake ta mike a take tana Cewa

Dan Allah Kiyi hakuri,wallahi ni Ba mai lafi nace karki min mugunta

Itadai Katrina ganin bats gane Ba sai ta kalli sauran with a questioning look

Fassara mata sukayi kamin tace oh sai tacewa minal din

No no my dear am gonna harm you,impact am being gentle with you

Minal dai anzo gurin domin bata gane ko Abu daya data ce Ba

Hasali ma banda harm babu abinda taji sai ta dauka Cewa tayi me yasa ta Tara gashin hammata yana damunta da wari

Nuna kanta tayi da yatsa cike da takaici tace yanxu bayan cinzarafin da oganku yamin,da iriyar muguntan da kike mini shine harda cin fiska?

Ina ruwanki da gashin hammatana?

Tala ne tace Kamar ya?

Minal tace inba wulakanci Ba shine zatace hammata na yana wari Wai na tara gashi.

Tala ta dan dara kamim tace kai da abin dariya kike wallahi ai Ba haka take nufi Cewa tayi..................

Kara kai minal tayi alamun gamsuwa tace kiyi hakuri.

Katrina ta gane me tace domin zama a cikin su tala.
Dukda Cewa dakinsu daban amma ta Dan Koyi wani Abu a Hausa
suma dai su tala dasu maimuna dasu Rabi a primary suka tsaya zama da irinsu Katrina dasu Susan yasa suka koyi English

Sai tace is okay

Cigaba tayi da treating ciwon Inda minal keta tsala ihu tana raki

Lokacin da ta gama minal ta Dade da wanka da ruwan majina da hawaye

Zata fita ne ta tana fiskanta domin tace mata take care amma me zataji zafi radau Kamar garwashi.

Atake tace oh my god your temperature is so high I must give you an injection

Dan! Dan!! Dan!!!........

Minal tasan sunan allura ta English gashi matsoraciyar allura ne
Aiko zazzare ido ta fara kama mushriki yaga mala'ikan mutuwa.

(Wasu they prefer injection but to me that's a total and absolute NO. )

Ciro allura Katrina tayi ta soma jan ruwa. Wani wawan tsalle minal ta daka daga kan gadon Wanda yasa ta fado kasa tare da kwale kafanta ihu ta kurma.
Ta diba a guje binta sukayi aiko ta fada bandaki ta masa key sannan ta zare

Bubbuga kofar suka fara itako Cewa take wallahi ko su baba basu iya sawa ayi mini allura .
Ko agida har saman bishiya nake hawa har Katanga nake haurawa Dan na tsira sai nan da yakeda wurin buya masu yawa? juyawa tayi domin taga Inda ta Shiga

Sink ta fara daura idonta akai wanda ya mata Kamar tasan abin amma ba'a haka tasan shi Ba
Jacuzzi ta kalla sai tace laa irin bahon gidan aunty fauziyya amma na masu kudi

Toilet din ta kalla tace la wannan ma irin salgan bayinta Saide shima na masu kudi ne
Yasin gwanin kyau bayin Kamar kayi bacci a ciki.
Bude kofar bayin da akayi yasa ta juya Katrina ta gani da allurarta ta a hannu tare da tala,da Rabi.

Wani mahaukacin ihun data kwalla yasa su murja, atine, meramu, safiya, Hauwa, Jenifer,Susan,Emma,rabecca,sanjana,suyunjin and others shigowa dakin domin in kaji ihun zaka rantse yankata akayi

Yazeed's pov

Yana kwance a gadonshi yana nazari har bacci ya kwasheshi.
Sama sama cikin baccinsa Kamar a mafarki yakejin ihu hakan yasa nauyin baccin ya fara saukowa daga kanshi amma bai tashi Ba

Ihun da ta kwalla yasa yayi wani mugun zabura yana zazzare ido yana muzurai domin shi ya dauka wani abin ne ya faru har ya zama ready to fight.

sai ya sake jin an kwalla wani kara,iska yaja yace ya Allah wannan wata iriyar yarinya ce haka
ta mayar min da gida Kamar mental asylum

Fita yayi ranshi a bace jijiyan kanshi duk sun tashi

Minal kuwa lokacin ta nuna Kamar tayi surrender ta fito saboda ta fahimci basuda imani zasu iya matseta karfi da yaji a danna mata karfe a jika

Rabi ne tace ko ba ke Ba fah kinga lafiya zaki samu Indian Anyi allurar

Kuma sir yace kije ki sameshi gashin bayason jira danma yasan asume kike

Katrina ce ta matso da allurar zata mata domin har ta fara gajiya da wannan hali irin na minal

supan data watsa izuwa kan gado tare da kwala ihu yayi daidai da shigowar yazeed

Fuskar nan murtuke babu annuri ko kadan yanda kasan bai tana dariya tunda aka haifeshi

Ihu daya bazo mata shi yayi sanadiyar makalewar tata sauran ihun

Shiga dakin yayi sannan ya fincikota daga kan gadon yayi wajen da ita janta yake..............

Finally!

thank you so much for bearing with me
Good night

17 June 2019

Your sweetheart

Mzz untichlobanty💕
[1/11, 1:47 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

By miss untichlobanty

*CHAPTER 13*

Janta yake tana turjewa "Dan Allah oga sir kayi hakuri ka rabu dani wallahi bazan kara ba, na tuba,na tuba!"

Abinda taketa fada kenan tana kokarin zare hannunta daga nasa domin tasan idan ya kaita Inda sai kaita bazataga da kyau Ba.

Store room yayi niyyan kaita.
Atish!aaaaatiiiish!!aatish!
Atishawan da take sirnanowa yasa ya fasa kaita domin yasan ta fada ruwa sanyi ya kamata ga kuran store kuma?
Maybe ma she is asthmatic. Hakan yasa juya ya canja hanya zuwa side dinshi.
Ihu take tana bashi hakuri amma Allah cikin ikonsa wannan Karen ma hawaye sun dauke kafa

(Nace kekam minal kinga ta kanki sanda ake bukatar hawaye sai su kafe sanda ba'a bukatarsu kuwa yanda kasan ruwan sama me saka ambaliya)

Bakin wata kofa wacce take barin dama da dakinshi kuma next to it ya bude. Wulla ta ciki yayi ta fada kasa sannan shima ya Shiga.
Bakin gado ya nema ya daba mazaunansa sannan ya kalleta yace knee down!babu bata lokaci tayi Kamar yadda ya umarta jiki na rawa

Sai alokacin yakalleta da kyau yarinyace sosai.
Sama da kasa yamata aranshi yace kwailace ma amma she has the guts to..........iska ya fesar a bayyane yanaci gaba da kallonta.

Itako ganin ya tsare da ido yana mata kallon tsana yasa jikinta yayi sanyi Ashe bazata kara ganin innarta da baba Ba? gashi ya Abubakar ma ya kusa dawowa nanda wata shida shima bazata gansa Ba?

Gashi dije ma takusa dawowa saga boarding Ashe bazasuga juna Ba?

Ashe ajalinta ne ya fito da ita?dama mafarkin mutuwa da taga tayi Ashe zai zamto Gaskiya?

Maganar da yazeed yayi yasa ta dawo daya tunanin da take.
Ke?kin iya up and down?
Harara ta banka mai yasin bazanyi Ba

Kallonta yayi da mamaki da kuma takaici Wai ita bakinta baya mutuwa ne?shi tunda yake banda zakiyya babu mai iya kallon idonta ma tamasa magana balle tsiwa ko zakiyya ma tasan lokacin da take haukanta. hmm zaiyi maganin yarinyarnan da alamu kanta yana rawa.

Hannu yasa ya dalle Bakin Wanda yayi sanadiyar fitar jini kamin yace
Mike ki fara up and down!
Jikinta na rawa ta fara kwanciya yayi ya rufe idonsa fuskarsa na kallon sama.

Sanda tayi kusan na Minti Biyar alokacin ta gama had a gumi sannan ta dubeshi tace oga sir kayi min rai
Wallahi bani kara maka rashin kunya jin shiru ba'a amsa mata Ba yasa ta tsaya da punishment din ta sansado ta leka fiskarsa ganin idonsa a rufe yasa tace
Kutma lallai ma mutuminnan Dan rainin hankali ne.
wato ga inji ko?inyita aiki shi yana bacci,wallahi Allah ya isa na.

Sanda takeyi harta iso Bakin kofa zata fita taji yace
Da izinin zaki aikata hakan?kuma Waye Dan rainin hankalin?

Juyowa tayi a zabure tana zare ido dama Ba bacci yake Ba?
Wayyo Allah bakinta yaja mata.
Zama yayi yace dawo ki zauna.
A hankali take takowa Kamar kazar da kawai ya fashewa a ciki harta tsuguna

Gabansa ya Muna mata ta matso tana zare idanu harta rame Kamar Ba ita ba.
Yazeed yace dago kanki dagowa tayi amma idonta a kasa.
Yace Nayi kama da sa'anki? Ta girgiza kai.
Yace kinada matsalar kwakwalwa ne?ta sake girgiza kai. Tsawo ya saka mata yace use your fucking mouth !

Itadai bata gane ba saboda accent dinsa ya mata tsauri amma sai tayi shahada wajen Cewa kayi hakuri.

Yace kintaba ziyartar gidan mahaukata ne?domin kinyi kama dasu

A ranta tace kutma wallahi ni banyi kama da mahaukata ba Saide kai ne mahaukacin.
Chapter 8 · 0% Book details