Sashe 70
Kuruciyar Minal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hankalinta ne ya iyo kan minal saboda ihun data tsala nan fa ummu tasa ya Kira Mata uwani sukasa minal a daki. Yanda sukaga yini haka suka ga dare, daidai an fara kiran sallan asuba Allah ya albarkace su da........
Yan biyu Mata yan cukul cukul gwanin sha'awa,dadi ummu ta dinga ji kamar jikokinta na gaske kankace me makota da munafukai da yan tsurku anata shigowa domin ganin yara. Kowa na tofa albarkacin bakinshi. Saide an fara tuka tsiya da minal ne lokacin da akazo wankan jego tace ai Sam batasan da zance ba saide tayi da kanta haka aka hakura aka barta tunda ba halin ayi Mata karfa karfa.
Sati na kewayo wa aka sha suna daidai gwargwado, inda aka samu sahla da zayyana.
Kuma a wan an rana ne aka daura auren ango yazeed da amaryarsa safina. Har yan kawo amarya suka gaji suka watse ango shiru. Su sahir ne suka shigo suna murna suja rungumeta suna fadin mommyn mu, sannu da zuwa. Yake tayi musu tana Dan tutturesu a dabarance yayinda a ranta take cewa kai indai yarannan kamannin uban su suja dauko toh lalle na jefi tsuntsu biyu da dutse daya.
Dalewa tsakiyar gadon sukayi suna tsalle ta daka musu tsawa tsirata sukayi ta nuna musu kofa sidif sidif suka fice suna kallon juna. Bayan sun fita Safwan yace mommyn nan batada kirki. Sahir yace maybe kawayenta ne suka bata Mata rai. Rugawa sukayi da gudu abinsu ko a jikinsu.
Shiru shiru yazeed bai shigo ba har bacci ya dauki amarya a wajen. Mutuminku ko tun da aka daura aure ya shige dakinsa ya kwanta Baku kara jin duriyar sa ba yanaji aka kawo amarya aka gama bidiri aka wuce tsaki yaja tare da kwanciya haka kawai yakejin haushin kowa dake tare dashi a lokacin ji yake kamar ba shi ba.
Minal kuwa tsakar dare zayyana ta tashi ta fara musu kuka aka bata mama anyi yin duniya amma sai kuka basu suka rintsa ba sai bayan asuba yayinda sahla ta dinga bacci kamar gawa.
BAYAN SHEKARU 8
Dauke shi da Mari safina tayi tare da cewa wallahi sahir idan baka fice mun a daki ba zaka Rena kanka idan ba rainin hankali ba da ban yini ba zaka ganni ne? Tsabar munafurci zaka wani zo wai gaisheni? Kuma saura inji ka fadawa wa ubanku ni da kai ne mangajesa tayi tare da fita ta kunna TV a parlourn sama tare da kure murya kamar cinema.
Mummy ne ta fito tare da cewa haba safina irin wannan murya sukace cinema? Ki rage muryar tv din mana. Tafiya mummy taci gaba dayi amma me ? Sai safina taja tsaki juyowa mummy tayi tace je safina karkiga ina daga miki kafa ko nemi ki kawomin hauka a gida kinaji na ko toh wallahi idan baki kiyayeni ba zaki sani aikin banza da wofi. Mikewa tayi tare da cewa ke tsohuwa dakata kiji..... mummy ne ta datse ta ta hanyar cewa uwarki ne tsohuwa.
Daga hannu tayi zata wanke mummy da Mari ayush tayi caraf ta rike hannunta sannan ta yanka Mata Marin. Dariya ta sheke dashi kamin ta tattare zanyi nanfa suka zage dantse suka casu suns zagin juna ayush na fadin dama a karuwancinki na barki kikayi yayinda safina ke fadin ai yafimin zama da wannan Dan wahalar Wanda tunda mukayi aure sau daya ya rike hannuna.
Mummy ne tayi kokarin rabasu aka mangaje ta, ta doke kai da gini ashar ta danna tare da cewa yasin babu abinda zai hana Dana sakinki. Dariya safina tayi tace wai danki, ke bakiji kunya ba ? AI shekarata 2 a gidannan na gano ba danki bane. Kuma da kike zancen saki AI gara zawarci da aurennan saide babu inda zani yadda na wahala na shekaru 8 wallahi kuma bazakuji dadi ba. Kuma wata shegiya tace zata fada masa taga ikon Allah komawa tayi ta zauna akan kujera sai haki take sanadin fadar da sukayi tare da turo Dankwali gaban kai.
Cikin tsoro mummy da ayush ke kallo juna jamin sukayi wuf sula shige daki tare da yin kuskus.
??
Abangaren su minal kuwa ta auri sabi saide dukan yau daban na gobe daban ga ummu amina bata da lafiya wannan dalilin kadai yasa minal bata gudu da daga gidan ba.
Zayyana da sahla ne a kofar gida, sahla na yar carafke yayinda zayyana ke yar gala gala akan hanya. Yaran anguwa babu Wanda ya isa ya taka idan zaka taka kuma ka wuce toh dole ta mareka haka yara ke kin zuwa aike saboda ta kasa ta tsare tijararta yafi na mahaifiyar ta.
Da daddare minal da sabi sukayi wani fadan hakan yasa ya zaro wuka zai kokuwa suka fara yi har suka bige lantarkin su. Hankadesa tayi ya fada aiko akayi rashin sa'a ya fada akan wukar ihu ya saki hankan ya tsoratar da minal sosai babu shiri ta dauki sahla wacce take shiru shiru kuma batada kuzari tare da tashin zayyana cijewa ta fara yi minal tace idan baki Mike mun tafi ba gobe zaki mutu babu shiri tarigasu isa bakin kofa tafiya sukayi sosai cikin daren wajajen karfe 3 jiri ya dauke minal ta suma tsabar tashin hankali ga tsoron kisa, ga daukar yarinya gashi yanayin da tabar jikin ummu Anya kuwa ta Mata adalci, iya ta dauketa lokacin da batada kowa kamar nata tayi Mata komai amma da abinda zata saka mata dashi kenan? Kai amma yaranta fa tunda dukda ba ita ta kashe sabi ba ita za'a daurawa balle ansan basa jituwa. Ga ummu kuna rai a hannun Allah hawan jini ya addabe ta.
Jijjigata suka fara yi suna wani ya haskosu da tocila tare da cewa kai! Su waye a wajen ne? Matsowa kusa yayi ganin kamar yara ne. Haska Fuskar minal yayi cikin rawar baki yace *YAR UWA? KECE?*
*KO SHIN WANENE WANNAN MUTUMIN? TAMBAYAR MAI SAUKI CE AMMA DUK WANDA YA ANSA TA TO CHAPTER BIYU NA GABA DUK NASHI NE SHI DAYA*
*TEASER/CIKIN CHAPTER NA GABA: minal zata hadu da yazeed.........*
MASHA ALLAH, AYI MIN AFUWA JIYA KUN JINI SHIRU,? SAFGOGI NE SUKA SHIGEMIN GABA.
DEDICATED TO @MYFANS.
GOODNEWS: their will be another update today by 5pm insha Allah stay tune.
DON'T FORGET TO COMMENT.
ONE LOVE FROM
Miss untichlobanty ?
10 April, 2020.
?? *KURUCIYAR MINAL* ??
? _by miss Untichlobanty_ ?
? *CHAPTER 82* ?
*RECAP*
Jijjigata suka fara yi suna kuka suna kiran sunanta wani ya haskosu da tocila tare da cewa kai! Su waye a wajen ne? Matsowa kusa yayi ganin kamar yara ne. Haska Fuskar minal yayi cikin rawar baki yace YAR UWA?.... KECE?
*CONTINUATION*
Gumi ne ya fara tsatstsafo masa cikin tashin hankali ya sake furta yar uwa? Ashe rai kanga rai? Daukarta yayi tare da cewa yaran su biyosa. Zayyana tace ka San mu ne? Ina zaka kai mana ummin mu? Bai kulata ba har suka iso gidansu dakin mahaifiyar sa ya kaita.
Ummu sabir tana cin goronta taga ya fado da mace da yara tace kai dannan, me zan gani haka? Yace ummu nasan bazakiso ba amma ki daure ki danne zuciya kinga matata ma tabar gidannan ne sandiyyar ki. Kwata kwata bana iya zama da mace saboda ke ki daure kibar wannan baiwar Allah ta zauna ko na lokaci kadan ne tsaki taja tace kar ka fice da wadannan Ababa a daki kaima sai in tsine ma. Hawaye ne suka cika masa idanu jiki a sanyaye ya juya ya fita tareda kaisu dakin matarsa. Kwantar da minal yayi sannan ya yaiyafa Mata ruwa. A hankali tace ruwa, ruwa.
Ruwa ya dauko ya ba ma zayyana yace ta bata sannan ya fita ko zai samo abinci. Garzayawa yayi ya koma gidan da yake gadi ya sanar dasu abinda ya faru, nan suka bashi abinci da wasu surutu sukace yakai ma minal din.
Koda ya dawo minal har ta Dan ware nan ya basu tare da ficewa sallar asuba.
Bayan ya dawo minal tayi masa godiya harda hawaye kamin yace niko kamar na sanka. Murmushi yayi yace Dan uwa ne fa. Shiru tayi ta gama nazari bata gano wani Dan uwa ba. Nan sabir ya labarta Mata yadda akayi? aiko ta dinga yi masa godiya.
Dakin mahaifiyar sa ya leka ya sanar da ita zai koma bakin aikinsa. Dauke kai tayi tare da fadin da fatan tare zaku tafi? Yace haba baba kiyi hakuri mana zasu bar gidannan amma yanzu ki daga musu kafa. Naji kawai tace hakan yasa shi sauke ajiyan zuciya harda godiya sannan ya fice.
A hanyarsa ko tunanin halin mahaifiyar sa yake ita indai harka ba ta kudi bane to baza'ayi da ita ba. Tunda ya rasa aikinsa ya kasa gane kanta. Haka ya isa gurin aiki hankalinsa ba a kwance ba.
Samu yayi gidan anata shirye shirye ya tambayi me bayin flower me ke faruwa ne ? Me bayin flower yace bakasan cewa yau diyar Alhaji na biyu zata dawo ba? Sabir yace ikon Allah gaskiya naji dadi. Mai bayin flower yace cab lallai an barka a baya kace kaji dadi? Wannan yarinyar bata ganin kowa da gashi a tsakiyar ka. Sabir yace kaga malam, ni banason gulma. Sannan ya koma bakin aikinsa.
A gida kuwa sabir yana fita mamar sa ta fito ta samu sahla da zayyana a bakin rijiya runa dibar ruwa. Warce gugar tayi tace Dan...... wa ya Baku izinin shan ruwa a gidannan? Zayyana tace ishi mukeji. Tace kinci ..... sahla cikin muryarta na abin tausayi tace kiyi hakuri. Idonta sun ciko da hawaye .
Minal ce ta fito tana kokarin bada hakuri kawai ummu sabir ta adungure kan sahla kan kace tak ta fada rijiyar. Wani irin kara ta saki ta fara ihun neman taimako mutane ne suka shigo aka cirota kamar gawa kokarin ceto ta samarin sukeyi amma minal gani take kamar kasheta zasuyi hakan yasa ta karbi yarta ta wuce suka fice a gidan Allah wadai mutane sukayi da irin halin ummu sabir sannan suka fice.
Tana tafe batasan inda take wulla kafarta ba Dan ji take kamar tana dauke da gawar yarta ne duba da yanayin sahlan. Zayyana ne taja hannunta ta zaunar da a bakin wani gini tace ummi ku zauna anan bara in kawo mana ruwa.