← Book details Kuruciyar Minal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 80

Sashe 3

Kuruciyar Minal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mahaifiyarsa ya Tarar zaune a parlour tana kallon news ga fruit a gefe tanasha hankali kwance cikin fara'a da walwalan ganin mahaifiyarsa abin kaunar sa yace mom! jin muryan Rabin ranta kuma danta wato CPT YAZEED ABDULMAJEED UMAR ta tashi yazo da sauri ya rungumeta tare da manna mata peck a kumatu yana fadin I missed u mom itama tace missed you too son

Dama tun dazu shi take jira domin tasan da dawowarsa
Tace son go and fresh up sai kazo kaci abinci ko smiling yayi yace okay mom tare da hayewa middle staircase coz shine nashi the one left for his wife zakiyya and the one on right for his mom.

Bathroom ya fada direct Ba tare da tinanin Komai Ba ya cika jacuzzi da ruwa yasa bathing soap and perfume ya shiga ciki ya rufe idonsa tinanin zakiyya ne ya fado mai,
shikam ya rasa yadda zaiyi da itA sai kace Ba auren soyayya sukayi Ba ace Sam batada time dinshi yauma da zai dawo daga tafiya she can't stay at home just for a day thank goodness he hasn't let her become a full-working wife as she wanted or else Hhhhhhh iska ya furzar domin abin ya fara isanshi Gaskiya saboda ko hakkinshi na aure yanxu da kyar yake karba agurinta.

Ganin tinananin bazai fisheshi Ba yasa ya gama wanka ya daura alwala, da Rigan wanka zai sa ya Fasa ya daura towel ya fito rike da karami yana goge silky,soft and dark hair dinshi he looking so sexy (Kamar yadda naji Yan mata na fadi danni haryau wannan shirmen baya birgeni amma danku sai na rubuta ko ya kukace? You are my first priority.)

CPT YAZEED ABDULMAJEED UMAR kenan! a 35years old son of late ALH. ABDULMAJEED UMAR

ALHAJI ABDULMAJEED UMAR is a multi millionaire international businessman with the organisations and companies namely jeedmar empire, jeedmar furnitures,jeedmar shoes and clothing,jeedmar oil company, jeedmar rice,jeedmar sugar,jeedmar cement,jeedmar orphanage and much more.
Asalinsa fulanin zamfara bayan ya gama karatu ya fara business ikon Allah cikin kankanin lokaci ya bunkasa har ya fara companies a different countries a yawon kasuwancinsa ne ya hadu da mom wacce take Nigerian-arabian wato babanta Dan Nigeria mamarta er riyad(saudi)amma a Dubai suke zaune.
Sun hadune ta sanadiyyar babanta saboda Suna kasuwanci tare sannan ya gaba da hankalinshi.
Haka dai sukayi aure kuma lokaci daya soyayya mai karfi ya Shiga tsakaninsu amma Abu daya suka rasa haihuwa haka sukayi shekara 12 Ba ko batan wata tukunna daga baya Allah ya dube su da idon rahama ya basu da namiji wadda suka samai YAZEED tun yana Yaro yakeson armies shi baya kallon cartoon irin na yara in ka Ganshi ya na kallo to sojoji ne har faint na dakin shi na sojoji ne. wata rana ALHAJI ABDULMAJEED ya tattari family dinshi gaba daya akan zasuje aikin hajji dukda Cewa wasu daga cikinsu sun sha zuwa amma wannan karon a tare yakeso suje saide mom bataje Ba itada YAZEED domin Ba tada Lpy sai akabarta tare da kakus Maman ALHAJI ABDULMAJEED.

Bayan sun sauke farali ahanyarsu ta dawowa sukayi hatsari a jirgi inda yawanci suka rarrasu wasu kuma suka sami matsalan haihuwa shi kuma ALHAJI ABDULMAJEED was paralysed. Alokacin YAZEED na shekara 13 saboda tsananin Sabon da yayi da mahaifinsa hakan yasa ya zama so moody rayuwarsa duk ta canja ya zama shiru shiru lokacin dayatafi makarantar sojoji at that tym he was 25 Anan aka aiko masa da rasuwar mahaifinsa yayi kuka har ya gaji tun daga lokacin aka dena gane kansa bayan ya kammala ya dawo anane ya saida some companies na dad dinshi to the some Arabian and British partners na dad din nasa wasu kuma ya rarrabawa family members marasa karfi sosai akan su kular mai da companies din,sai su dinga yin 50 50 atakaice de bai rike ko company daya Ba domin shi soja yakeson zama.

Alokacin da yaje wani mission a Washington Anan ne ya hadu da zaliha lokacin tana shekararta na karshe a university wasa wasa soyayya maikarfi ya Shiga tsakaninsu bayan ta kammala sukayi aure amma ita tace burinta aduniya shine ta zama businesswoman amma YAZEED yace shi bazai iya juran zama babu mace a kusa dashi Ba amma idan ta yarda zai bude mata boutique
Ganin da babu gara ba dadi yasa ta yarda plaza guda ya siya ya mayar mata boutique da office dinta aciki Dana wasu masu mukamai kadan daga cikin masu aikinta.
Amma duk da haka bai tsira Ba domin kullum batada aiki sai boutique da ka tabata boutique dinta kawai ko lokacin kanta batada shi.

Wannan kenan

Show some love by
Sharing,
And
Commenting.

Love you Lodi Lodi sweethearts

29th April 2019
Mzz untichlobanty💕
[1/11, 1:20 AM] Mzz_Untichlobanty💞:
🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹by mzz_untichlobanty🌹

*🍀CHAPTER 5🍀*
Bayan ganin tunani bazai fisheshi Ba yasa ya shafa mai ya saka 3quater irin na sojoji da farin T-shirt ya fito mahaifiyarsa ya Tatar a parlourn tace son sai yanxu?Sosa kai yayi yace sorry mom dina na I kept you waiting ko?

Tace is okay,come and eat your food coz na sanka idan ta kai ne zaka wuni bakaci abinci Ba gashi nan yanzu ulcer ta maka kamin kawo wuka

Yace haba mom ya isa mana zanci muje dining din haka ta kama hannunshi takaishi taja masa kujera ya zauna ta zuba mai abincin yace kai mom this is too much tace see you, wannan abincin a 5 years old child can eat it but you hmm you will never change
smiling kawai yayi yafara ci.

Baifi 6 spoons yayi bah yace ya koshi babu yadda mom batayi Ba yace Sam ya koshi haka ta rabu dashi yaje daki domin ya huta

11:59pm (night)

Suna zaune a parlour yana kan cinyarta tana shafa gashinsa Suna Dan hirar su na uwa da d'a zakiyya ce ta shigo taci wani suit na mata takalminnan dogo Kamar zai karye
kwas kwas kwas kakejin takun takalmin ta koda ta shigo ta gansu kawai hannun tadanyi using irin hii dinnan kamin tace wlcm baby tawuce abinta

Girgiza kai kawai mom tayi kamin ta juyo ta lura Cewa dan nata na matukar son yabi matarsa amma kunyan idonta yakeji hakan yasa tace kai dagani ka gani bacci nakeji Ba musu ya tashi tare da mata peck yace good night mom sannan yahau stair case din dazai Sada shi da side din da matarshi take.

ZAKIYYA'S POV

Tana shiga dakinta ta yarda jakanta ta fara cire takalminta kamin ta fara rage kayan jikinta tare da daukan ribbon tana kokarin daure Malaysian attached wig dake kanta Wanda yake red,blue and black in colour taji anyi hugging dinta ta baya

Tsaki tayi kamin tace look baby am soo tired,and am not in d mood so leave me alone pls shinshinan wuyanta ya farayi yana Cewa I missed you Bea tasan sarai me yae nufi hakan yasa tayi saurin tureshi tare da fadawa toilet.

Koda ta fito yana zaune a kan gado Kamar maye yana jiranta bata ko kalli Inda yake Ba taje ta daura hannunta akan wani Dan machine Wanda zaiyi detecting tomb print dinta Wardrobe dinta ne ya baiyyana yayi typing nighties sai daya daga cikin kofofin Wardrobe din suka bude ta dauka wani brown din nylon riga tasa iya guiwa tazo ta kwannta tare da Cewa switch off d light when you are done taja bargo tare da juyamai baya

Mamaki ne ya cikashi Wai dama batasonshi ne ta aureshi koko wani abinne ya sameta coz wata matace za'ace mijinta yayi tafiya ya dawo babu ko sannu da zuwan arziki balle ayi zancen su abinci. Duk da Cewa ya saba da irin halinnan NATA amma nayau is worse haka dai yayi ta sake sake daga karshe yaje ya kwanta a bayanta yana Dan tattabata bige hannunsa tayi yace baby pls Wallahi I need you kinji ?
yadda yayi maganar ya bata tausayi hakan yasa tarabu dashi amma sai mita take masa Wai tagaji hakan yasa bai sami wani biyan bukata sosaiba masu iya magana na cewa da babu gwara Ba dadi

Koda ya tashi da asuba ya tasheta he entered the toilet did all the necessary routine,came out and found her still sleeping ya sake tashinta sannan ya fita masallati ta koma ta kwanta abinta har sai 6 ta tashi Wai bazata iyayin sallahn Ba sai ta dawo(ehm araina nace inkin dawo kuma kice kin gaji Ba Allah sai ya kyauta).

Around 7 ya dawo direct dakinshi ya wuce ya kwanta itako lokacin harta shirya tasaka pink suit mai wandon pelazu ta sauko sai shan kamshi take, ta buga uban extension akai sai yarfeshi take
Mom ce zaune a falo tana kallon news ayayinda take shan coffee,hade rai tayi domin bataso ganin mom din a parlourn ba.

Tace good morning mom,mom tace morning
Zata wuce mom tace zonan zakiyya
Zuwa tayi ta tsaya tana Duba agogonta
Mom tace yanxu abinda kikeyi ya dace kenan ki Duba wani shigar yahudawa da kikeyi koni Balarabiya banyiba,kuma ki fita tun safe sai dare sannan baki ko girmama mijinki balle ni ai ko............
Bata karashe Ba zakiyya tace sorry mom inaso boutique dina ya tsaya dakafarsa sosaine kamin in Dan dinga samun time yanxu fai Ba wa'azi nakeso Ba ince de matsalarki bana girkine to me kikeso kici?ta fadi hakan cikin Sauri tana Duba agogonta domin tayi latti acewarta.

Mom ta girgiza kai tace zakiyya kenan so nake naci koko da kosai tace okay kitchen ta Shiga tabi wata kofa Wanda zai sada ta side din ma'aikata taje bangaren masu girki tace pop out
Cikin kankanin lokaci sukayi layi a gabanta sanda tagama zuba musu kallon raini sannan tace waya iya koko da kosai duk sukayi shiru domin Continental dish yawanci suka iya
tsawa ta daka musu Ba daku nakeba ?

Emm kwanna biyu ban tsokalo muku minal ba karkudamu yanxu Muka soma tafiya

Show love by.........
Kungane ai😉

Love you all

1st may 2019

Mzz untichlobanty💕
[1/11, 1:26 AM] Mzz_Untichlobanty💞:

🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

By miss untichlobanty

*🍀CHAPTER 6🍀*
Chapter 3 · 0% Book details