← Book details Kuruciyar Minal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 80

Sashe 44

Kuruciyar Minal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sanyin ASUBA bayan an sallamo su zakiya Dan dole ta dage sai ta kamo hanyan dawowa gida babu yadda mahaifiyarta batayi ba amma tace Sam dole sai ta tafi.
Ayush tace haba sister Kiyi hakuri mana jijinki ya gama wartsakewa. Hararanta tayi tace ni da ke Waye babba? Ayush tace Kece zakiyya tace to ki shiryamin yarana mu tafi.

Ayush tace Toh. zakiyya tace ina nufin harda ke zamu tafi. Tace me yasa harda ni? Zakiyya tace saboda ban gama warkewa ba kuma kema your heart is broken.

Mummy tace Toh kibar min su sahir din mana. Zakiyya tace sanda nace kar a kawo min su ba dagewa kikayi saina rikesu ba?so yanzu nima ina son abina.

Hakadai Daga karshe suka Koma gida karfi da yaji suka Shirya kaya tareda kamo hanyar Kaduna.

🌹🍀🌹🍀🌹🍀

Kai Jamal tashi Daga baccinnan Mun kusa sauka. Hade rai yayi yace mom bacci nakeji sosai tace Toh sai ka Fadawa pilot din ai ya jira ka gama Baccin kamin mu sauka Dan Allah ni tashi.

Daidai lokacin tayan jirginsu ya Dan gwali kwalta.

Suna saukowa mom ta cire wayanta a airplane mode zata kira yazeed.

Mummy ni yunwa nakeji
Hararan Jamal din tayi tace waikai meye matsalarka ne kwana biyu uhm? Ko kaima aure kakeson in maka.

Zaro ido yayi yace nii?na shafawa kaina ruwan sanyi ki rufamin asiri.....

Tace Toh shikenan dama maganar bata tsaya ba. Yace dakata kiji mana ai Idan kikamin din ma bata baci ba.

Rankwashinsa tayi tace ja'iri zama kayi magana ni rabani da sabgar aurenku yazeed din ma ya na jare dashi?

Daidai lokacin ta kara wayanta a kunne bayan ta fara Kiran yazeed.

🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹

Koda su yazeed suka tashi sukayi sallah minal tace bari tayi tattare tattare ta daura abinci tunda Shigan safiya su mom zasuyi yazeed yace besan wannan zance ba kawai ta dawo su kwanta.

Ta buga ta raya amma yazeed yayi kunnan uwar shegu Daga karshe tazo ta kwanta a can kuryan gado tare da juya masa baya.

Sunane ya kira ta shareshi ya sake Cewa baby? Ta kauda kai tareda Jan bargo. Riko bargon yayi tareda wantsalarwa sannan ya finciko minal din fuskannan a mutuke idon shi yayi jaa Kamar bai tana dariya. Minal ko ta tsorata amma saboda taurin kai ta tsare tareda fading ni ka cikani kara matse dantsen hannunta yayi yace karkiga Muna shiru da zaman lafiya ki nemi ki Rena min hankali. Dan iskanci ana miki magana shine zaki wani juyamin baya? Bakisan yadda na tsanin hakan ba ko?

Hararansa minal tayi da alamu rants ya fara back kuma tasan Idan tayi kokarin yin magana to Mara dadi zai fito hakan yasa ta hadiye yawu dakyar tareda fadin kayi hakuri sannan ta warce hannunta tayi gaba. Yazeed Kam mamaki da Bacin rai ya hanashi aikata Komai.

Komawa bacci yayi Dan yana rasa me zaiyi ya huce.

Minal Kamar kitchen ta nufa jikinta duk yayi sanyi son ta rasa Waye ma Mara Gaskiya a cikinsu. Kawai sai ta basar tunda ta bada hakuri ta fara tunanin me zata dafa. Can ta yanke shawaran Zata dafa alale da kunun gyada Dan haka ta fara aikinta babu bata lokaci bayan ta gama ta nufi dakin yazeed domin ta Shirya Dan lokacin 7 ma yayi.

A hankali ta shiga dakin ta hangosa ya rufu har ka. Zuwa tayi taja Bargon a hankali ta bude fuskarsa taga yana bacci ya hade rai tare da cuno baki dariya ta fara yi kasa kasa kamin ta dangwali hancinsa a hankali tace mutum sai shegen kafiya.

Tashi tayi ta Shiga bandaki abinta domin tayi wanka.
Yazeed ko tun sanda ta bude masa fuska ya tashi amma sai ya shareta dukda ko ya huce amma bazai nuna mata ba.

Yana cikin Yan nazarce nazarcen sa wayarsa ta fara ringing Kamar bazai sauka ba amma ya daure ya dauko. Dubawa yayi yaga mom ne a take ya dauka take cikin muryan bacci kasa-kasa yace
Assalamu alaiki ya ummi! Gyara muryan mom tayi tace wa'alaika Assalam son yace an tashi lafiya sweetheart? Tace Alhamdulillah ya naji muryanka haka ? Yace bacci nakeyi ne. Jinjina kai tayi tace da alamu ka manta Cewa yau zan dawo ko? Dan zaro ido yayi domin ya mantan dukda ko minal ta tuna masa yau da safe. Yace hakane fa sweetheart na shafa'a ne. Yanzu zamu tasone?Dariyan manya mom tayi tace ai Mun ido ma yace subhanallah ! Sweetheart naso ace dani za'a daukoki but kamin na Shirya it will take time and I don't wanna keep you waiting zan turo a dauko min ke. Tace ba damuwa sai Mun shigo yace okay sai kun Shigo din.

Muryan Jamal ya jiyo ta dayan ban gareb yana Cewa guy wallahi ka tanadi labarin duk abinda ya faru Dan ina zuwa zaka Samar dani. Harara yazeed yayi kamin yace mom wayan hands free yake ne? Tace uhm yace yaiwa kana ji na ko? Da wani farangan farangan din kunnanka Kamar antenna babu labari da zaka samu. Dariya suka fashe dashi kamin sukayi sallama.

Waya yazeed ya rambatsawa lukman yace yayi assigning ake a dauko mom with tight security.
Lukman yace okay amma fa Kazan in amaryata tazo bazaka na min irin haka ba ko?kira da sanyin safiya Yazeed yace wannan kai ka jiyota sannan ya kashe wayarsa. Tashi yayi yaje bakin kofar toilet daidai zaiyi knocking minal ta bude. Daure fuska yayi ya banka mata harara itama hade rai tayi ta hararesa. Ratsawa tayi zata wuce ta gefensa ya dungure mata kai. Dungure nasa tayi itama suka harari juna a tare suka wuce.

🌹🍀🌹🍀🌹🍀

Masifa inna Keta surfawa Wai a dole zaliha tasata tafiya ba tareda ta Shiga ba ita dai zaliha ba inna bace a gabanta Mazarin yadda zatayi taga ta zauna lafiya da mijinta takeyi dukda ko babu hada makwanci dashi a agendan ta.
Tuno yadda suka dinga daukin aurensu ita da Sulaiman tayi kawai sai ta fashe da kuka inna ko salati ta rafka tareda farin lallai yarnan yanzu Daga miki fada shine zaki fashe mini da kuka sannu langai yar safara'u.
In baki min shiru ba sai kin Rena kanki a motannan Yan Moran ne suka tsaya kallon inna da zaliha ganin kallon yayi yawa yasa inna Cewa ba kaza Muke ci ba. "Min husnil islami mar'i tarkuhu mâ lâ ya'anihi" tunda dai ba dokar Allah nake rabawa balle kuce ya shafeku ai sai Kuyi abinda ke gabanku ko?
Cikin hausansu na kanurai suka ce Allah ya baka hukuri yar uwa.
🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀
Minal ko Shiryawa tayi abinta cikin lace me kyau ta shafa powder da lip gloss ta fesa tirare ta fice tana cikin saukowa Daga stairs taji Karan mota amma bata wani bada hankalinta ba ta nufi kitchen ta fara dibo abubuwan da ta dafa tana jerawa akan dinning table. Bayan ta gama ta sake hawa stair case zata Koma part din yazeed taji an narko wata ashar Wanda tunda aka haifeta bata tabajin irinsa ba. Kamin ta juyo taji an fincikota ihu ta kwalla Allah ya taimaka steps uku ta taka hakan yasa ta fadi warwas a Kasa tare dayin targade a kafa kuma dai lokacin taji wani ya dauke wani da mari Daga nan Komai yayi mata duhu.

Nasan ba yawa chapter din kuma is boring amma amin afuwa.

Don't forget to comment

Duk wacce tayi commenting masoyiyar su yazeed ne

Bara yau ayi yar tike inga su Waye masoyan minal and yazeed👁👁

Comment nakeso ba Tnxs ba😉

Takuce karamarsu babbarsu

Miss untichlobanty💕

31st December,2019
[1/11, 5:13 PM] Mzz_Untichlobanty💞: *🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆*

🌹by miss untichlobanty🌹

*🍀CHAPTER 60🍀*

Wani wawan mari yazeed ya sake fallawa zakiyya wacce ke dafe da kumatu  cike da mamaki.

Zuciyarsa wani harbawa take domin ki yake Kamar hi aka jiwa ciwo dukda ko zakiyya matarsa ce bazai yadda da zalinci ba kuma dukda ba'ason suka a musulunci ita ta wuce Gina da irin Idan ta kasheta fa?

Masifa ya fara sarfowa Kamar makokoronsa zai fita yace haba zakiyya meye haka ? Kamar ba babba ba? Ko ance miki kishi hauka ne ? Yanzu Idan kin kashe yar mutane fa?

Idonta yayi jajir tace lallai yazeed banga laifinka ba ka sami yarinya danya yadda kakeso dole ka mareni!tukunnan ma uban Waye ya bata izinin Shiga bangarenka alhalin ban.....

Yazeed ne ya datseta ta hanyar Cewa kaji matsalar kenan Ku Daga an muku kishiya sai kuce ai Dan ba'a sanku ne ko Dan kun tsufa ko an sami yarinya wa ya mutu wa ya tashi. Ku bakwayin la'akari da Cewa ku ma canjawa mai gida kuke kuma ai dama in kida ta canja dole rawa ma ya sauya. Ki sani tun da inasonki kuma Dan na sake aurennan ba fasa sonki nayi ba. Da kike zancen wa ya bata izinin Shiga side dina, ni ba mijinta bane? Kinga ko right ta sameshi 100%.

Zakiyya tace namiji butulu,namiji ba Dan goyo bane amma ba Komai ba laifinka bane.

Ayush kam baki ta saka tana kallon ikon  Allah in ta kalli yazeed dake huci Kamar zaki Daga shi sai towel sai ta kalli zakiyya dake kwalla sai kuma ta kalli minal dake kwance a kasa.

Juyawa zakiyyan ma tayi ta bar wajen ta nufi dakin ta. Wani kallon tsana sahir ya watsawa yazeed da minal sannan yace you are a bad daddy I hate you! kasa momy na kuka sannan ya janyo hannun safwan domin subi bayan zakiyya. Wafce hannunshi yayi ya ruga da gudu ya rungume yazeed yace no! I wanna chtay wit daddy (no! I wanna stay with daddy)

Hararan safwan din sahir yayi kamin yace fuck you

Hade rai yayi yace fuck you ich a nejetiv(negative) word onyi babboys uses it.

Sahir yace I don't care sannan yayi flipping off zuwa dakin zakiyya ayush Kamar tana kasa magana illa yaushe da YAZEED da tayi ta wucewarta part din zakiyyan izuwa  room din da ta saba sauka since this is not her first time.

Kayanta ta ajiye ta sauke ajiyan zuciya kamin ta Shiga wanka bayan ta fito ta Shirya ta dauko wayanta ta fara kiran lukman amma bai dauka ba saboda yana hanyan airport.
Chapter 44 · 0% Book details