← Book details Kuruciyar Minal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 80

Sashe 59

Kuruciyar Minal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiri suketa yi yayinda minal da zaliha keta yin fada akan lallai sai minal tayi kwalliya yayinda ta dage cewa bazata yi ba.
Zaliha tace kinsan Allah idan dai bazakiyi kwalliyar nan ba zamuyi fada ? Bakisan cewa za'a dauke ki a camera bane ga yan jaridu da gidan talabijin dukzasu zo minal tace tunda ba gasar kyau za'aje ba bazanyi ba kuma ai miji akewa kwalliya ba ?artin banza dawofi ba. Kuma ni ance miki zanje ne dan adaukeni? Zanje ne Dan mijina. Dauko gyalen da zatayi rolling tayi Dan kayan da tasa baya bukatar hijab ta dau Jakarta ta fice dan zaliha ta bata haushi.

?

A bakin kofan side dinta tayi kicibus da yazeed ciccibarta yayi yana fadin wa ya tabamin baby na? Dauke kai tai tana kumbura yace my minal fishing harda ni ne? Sharesa tayi bai dirar da ita ko ina ba sai dakinsa, dakyar yashanyo kanta suka sha romance ganin yana neman zurfafawa yasata guduwa.

Haka akayi bikin Karin matsayi akayi su pictures kowa na farin ciki aka watsesaide kash basusan cewa nanne farin matsalar su ba.
Yazeed kwance kan cinya minal a parlour suna kallon wani Indian series tsabar abin tausayi minal batasan sanda ta fashe da kuka ba dariya yazeed keta Ma ta wai ta jona Shaun asararru masu yiwa film kuka sai turo kanshi take tana ya tashi tunda abin hakane daidai lokacin luku ya tsindumo babu ko sallama sai haki yake da alamu gudu yayi. Yace ina wayarka inara kiranka baka daga ba? Yazeed yace ba wannan yafi muhimmanci ba, wa ya baka izinin diro min cikin bangare ba ko sallama. Tsaki lukman yaja cikin haki yace kai dalla share wannan bakas....... bai karashe ba yazeed yakai masa naushi tsabar kishi. Minal tayi saurin rikeshi tare da kallon luku tace ya akayi? Yace government tasa an rufe gaba daya account din yazeed saboda ana zargin wai ya hada baki da yan siyasa anacin kudin kasa sannan bazai iya sayar da kadarorinsa ba ma atakaice de har company yanzu duk NASA ne amma suna under government so he does not have a say a kansu har nanda 3 months? Abu daya aka barma daga gidannan sai ka zabi mota daya. Yanzu haka EFCC suna bin cike kuma you can't use your passport kamar kasan ba kuma baza'a baka Visa bama koda emergency har sai 3 months ya cika.

Yazeed ya zama shock ma dan shi baya ko irin kai wa yan siyasa ziyara da akeyi balle ya saci kudi daga jin magana akwai tuggu a ciki. Bakinsa na rawa yace menene hadin companies din mahaifi na da za'a saka a ciki ? Luku yace saboda idan ta tabbata gaskiya zai zama na gwamnati wai shine hukuncin ka.

Yace ya batun Wanda na bayar dasu ga families Dina? Luku yace eh wannan basu da harka dashi tunda yanzu ba naka bane ajiyan zuciya ya sauke tace atleast munada yadda zamuci abinci maza ka hada meeting da uncles Dina baki daya on Saturday, Luku yace sure kamin ya fice.
Gumi ke tsattsafowa yazeed domin ba dukiya daya rasa bane ta dameshi yadda aka bata masa suna bai ji ba bai gani ba. Rungume sa minal tayi tare da kwantar dashi a kirjinta tace yazzy baby karka damu komai zai wuce is part of kaddarar mu.

Haka yaci gaba da basa baki har yayi bacci a kirjinta sai alaokacin ta lura da yadda hawayensa ya kika Mata Riga. Ajiyan zuciya ta sauke kamin tayi nata kukan Dan ta daure ne kar ta karya masa guiwa.

?????????

?Darius take shekawa abinta tare da cewa kai nifa shegiyace duk wadda ya taboni toh shida kwanciyan hankali sun raba kafa kamar aljanna da wuta.
Mummunin Alhajin da take zaune a cinyarsa ne ya sheke da dariya yace kaji shegiya wai dama kinsan akwai wuta da aljanna kike wannan tsiyar? Hade rai yayi Tace me kake nufi? Daidai lokacin wayanta yayi ringing ta dauka tace ya akayi ta dayan bangaren akace gaskiya fa madam mugu(bokanta) yana korafi cewa idan dai bazaki dinga zuwa yana biyan bukatar sa ba to saide ko dinga aiko da jarirai uku idan ba haka ba ku ?a?e. Tsaki Taja tace ni rabani da jarabarsa ban iyawa ga warin da yake zan karo ma 500k a samo Karin jaririn akai masa. Ta dayan bangaren akace hakan ma yayi.
Daga nan ta kashe wayan Alhaji yace amma baby wai me suka miki hakane kika tsanesu da kike kashe irin wannan kudi? Murmushin rashin imani tayi tace hmm bazata gane ba. Yace ada na barsu ganin abokin hamaiyar tawa ya mutu amma yanzu Dana hadu dake sai naji dole ma in ga kayansu musamman yanda dan ke nema yafi uban yin nasara.

Sauka tayi daga cinyarsa tare da fara safa da marwa a dakin tace kiyaiyar danake musu tafi Wanda kafirai keyiwa annabi na samesu fiye da yadda na tsani mutuwa ta kai Alhaji bari kaji idan har zanga sun kaskanta sun wahalu a duniya toh wallahi babu ja in ja na yarda in shiga wutar jahannama indai sun wahala. Banida matsala koda kuwa za'a ha?a ni da shedan a wuta a matsayin roommates.

Jinjina kai yayi kamin ya tattaro ya harhado tumbinsa ya Mike yaje ya rungume ta ta baya yace yanzu ne na ha? da macen data dace wacce bata tsoron ta baci indai saurinta zai cika gaskiya wannan jawabi naki ya kara sa min kaunarki a zuciyata.

Juyawa tayi tace Allah Alhaji na? Yace kwarai ma kuwa yanzu yadda zamuyi dasu Dan nima a shirye nake tsanani dai ace wuta za'a samu toh ni ALHAJI TUKUR GADON ?AYA na bada ticket din aljanna ta Dan in kuntata ma ahalin ALHAJI ABDULMAJEED UMAR. Dariya suka fashe dashi tace kaga mu hanzarta domin na koma gida daga nan suka shiga aikata ashararancin su.

WANENE ALHAJI TUKUR GADON KAYA? WANI ATTAJIRIN MAI KUDI NE WANDA SUKAYI TASHE TAREDA ABDULMAJEED WATO BABAN YAZEED INDA YAKE DAUKE DA MUGUN HASSADA MA ABDULMAJEED SABODA YA FISHI YIN NASARA.
DA FARI JEEDMAR A BAUCHI SUKE DA ZAMA TAKURAR DA TUKUR GADON KAYA YA MUSU YASA SUKA KOMA GOMBE NAN MA YA BISU,SUKA LULA ADAMAWA,YA BISU SUKAYI KANO, YA BISU SUKAYI, SOKOTO LOKACIN AN HAIFI YAZEED AMMA YA BISU NAN MA SAI SUKA KOMA ABUJA TOH ANAN NE SUKA ZAUNA NA SHEKARA 4 KAMIN YA SAKE BIYOSU SUKA KOMA KADUNA ANAN NE AKAYITA TA KARE TUNDA ABDULMAJEED DIN YA MUTU BA SHIKENAN BA? TOH ASHE
DAI BAI HAKURA BA GASHI KUMA YA SAMU WACCE TA FISHJ DAUKAN ZAFI LAMARIN SAI YADDA ALLAH YAYI.

Ina mai lallashin ku na rashin jina da kuka yi abubuwa ne suka Dan taso min da fatan za'a min uziri?

Shin me zaku iya cewa gameda batun Alhaji TUKUR GADON KAYA? Ya kuke ganin lamarin nan zai kaya a tsakanjn su ?

Shin in karar da littafinnan da wuri ko kuma acid gaba da gashi?

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU wato

Miss_untichlobanty ?

14th February, 2020

*??KURUCIYAR MINAL??*

?by miss_untichlobanty ?

*?CHAPTER 75?*

Sauri minal keta yi tana tsallake steps da bibbiyu saboda lattin da sukayi domin yau jirginsu zai daga zuwa Abuja inda zasuje baban jeedmar group kuma anan ne za'ayi meeting din tallafawa yazeed kamin government ta wankesa.

Bude Mata kofa kurtu yayi ta shige luku ya finciki mota. Ba bata lokaci jirginsu ya daga sai federal capital territory of Nigeria.
Koda suka isa yazeed bai tsaya isa gida ba direct jeedmar group ya nufa. Sunayin parking ya fito cikin kwarjini da haiba yana? takunsa mai daukan hankali gwanin ban sha'awa. Dukda cewa a cikin damuwa yake hakan bai hana kyawunsa fitowa ba.

Ezekiel da lukman kawai aka bar masa a matsayi escorts dinsa sai masu gadin gidansa shima an rage wasu daga cikin su. Haka masu yin hidima duk an rage masa kuma duk munafurcin Alhaji tukur gadon kaya ne.
Tun daga bakin kofa ake gaishe sa tare da bada buda hanya yana zuwa bakin kofan shiga kofan yace "new individual detected please wait ......" scanning iris dinsa yayi kamin yace "welcome president it was nice you visit kindly put your thumb"
Saka thumb din nasa yayi take kofar ta bude masa gaba daya directors sun jeru Dan haka yana shigowa suka bi bayansa.?
Files suka fara miko masa ya daga musu hannu. Suna shiga gaba daya uncles din nasa suka Mike Yana zama suma suka zazzauna. Yace good day to you all ! As we already know we are here to discuss........ nan ya musu bayani ya sanar dasu duk abinda yake wakana sannan yace zasuyi signing contract before abubuwa su wartsake masa zasu dinga bashi 10% percent na eibar da suka samu idan companies dinsa suka dawo zai biya su.

Abinda ya basa mamaki shine yanda sukayi caaa! Sukace Sam Sam basusan wannan labarin ba. Daga karshe ma watsewa sukayi ba'a gama meeting din ba hakan yasa ran yazeed ya baci kuma ya tabbatar da cewa hatta dan uwanka zai iya cutarka sannan sai ka shiga matsala zaka gane masu sonka.? Fita yayi suka tafi ainihin family house dinsu dake central area, hmm ba'a cewa komai domin yafi na Kaduna kyau masha Allah tabarakallah.

A parlour ya samu minal ga abinci an kawo Mata amma ta kasa ci tayi jungum jungum. Umma hanifa dattijuwa ce kuma me aikin su yazeed ne tun suna Abuja ganin batada kowa na dangi sai Allah yasa koda zasu bar Abuja basu sallame ta ba, sai suka barta yaci gaba da zama a gidan tana gyarashi kuma ana biyanta kudinta har yau sannan ba ita kadai bane akwai maids guda goma.
Gaishesa sukayi kamin suka watse, gaisawa sukayi da umma hani kamin ta basu waje saboda ta fahimci yana bukatar hakan.

Riko hannun minal yayi zuwa daki duk ta kagu taji yadda aka kaya suna shiga tace da fatan komai lafiya? Ajiyan zuciya kawai yayi, hakan yasa ta fahimci me yake nufi baki ta basa kamin ta dauki musu abinci yace AI bazai ci yasani ko akwai poison ta masa pancake kawai aiko haka akayi.
Chapter 59 · 0% Book details