← Book details Kuruciyar Minal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 80

Sashe 2

Kuruciyar Minal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana isowa kofar gidan sa, basheer mai shago yace baban kowa ina wuni,Lpy klau basheeru ya shagon?basheer yace Alhamdullah baban kowa yace masha dafatan dai yauma minal bata taba kowa Ba Dan yau da safe tace Mani Wai tun jiya akace suje su karbo sakamakonsu. Basheer yace Gaskiya baban kowa yau minal bata yi hayaniya da kowa Ba hasalima ko fitowanta bangani wadda nima abin ya bani mamaki da alamu dai kawattamu ta natsu(haka basheer din ke kiranta domin ya kasance abokin ya abubakar ne tun yarinta shiyasa ma yayiwa baban kowan karya Dan kar yasa wa ransa damuwa sosai)
Baban kowa yace to Masha Allah haka akeso ai ni bara in Shiga Daga ciki ko? Allah yayi albarka basheer yace amin.

Minal na zaune tana yanka kubewa taji sallamar mahaifinta hantar cikinta ne ya kada da gudu ta mike har tana tuntube a 360 ta fada daki,garin sauri ta barar da yakuwar da take yankawa innace ta haba er lele lafiyarki kuwa zaki barar mani da......

Bata ida maganar ba baban kowa ya shigo yana cewa inata sallamma Baku amsa ba Kamar ba kowa a gidan inna tace yi hakuri malam sannu da dawowa Wlh wannan yarinyarnance ta fada daki da gudu har tayi Mani bari banjika ba yi hakuri bara na kawo ma ruwa
Takalmin sa ya cire ya zauna a tabarmar dake shinfide a tsakar gidan yana Cewa halan wayanta aka kira take wannan gudu , inna dake shirin bude randa domin sachet watern su ya kare tace anya kuwa?hira fa muke daga jin sallamarka ta rusa da gudu Kamar taga aljani,baban kowa najin haka jikin sa yayi sanyi bayason irin faduwsrnan da yarda keyi a makaranta domin Hanson tayi karatu ta inganta rayuwarta

Yace takarbo sakamakon jarabawar tasu kuwa inna tace eh ta karbo dazu gasucan yana kan yana kan taaga(window),tashi yayi jiki babu kwari ya dauko ya Duba aiko Kamar yadda yace ne ankuma na 48 tazo acikin su 52 a Dan fusace yaje kofar dakin yace aminatu me kikeyi acikin dakin nan,minal tace Riga make canjawa yace inba so kike na Shiga Ba maza ki fito tace baba aradu Babu Riga ajikina wanka make shirin yi yace Kamar da haske rabon da Kiyi wanka keda kanji Ba tare da dance Kiyi Ba yanzu shekaru 6 kenan amma shikenan ni bara in dubo sakona waje.

Oya show some love
By voting,
liking,
sharing
and
commenting

Tnxs for reading

26th April, 2019

Mzz untichlobanty💕
[1/11, 1:09 AM] Mzz_Untichlobanty💞:

*🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆*

🌹by mzz_untichlobanty🌹

*🍀CHAPTER 3🍀*

Sanda ta kara kusan 5min sannan ta leko da kanta duk ta hada gumi saboda rashin gaskiya

Saukan rankwashin da tajine yasa ta sankare a wurin na wani sakanni.

Durkushewa tayi a wurin tana tutturo baki kamar zai taba kofa.
Baba ne yace rufi min baki kamin in kara miki,maza tashi.

Mikewa yayi tana zuzzunburewa tace haba baba ko Dan wannan rankwashin da kake samani kamar abinci Ba dole na KASA kokari Ba kana taba min CPU na bakasan Cewa itace masarrafin Dan Adam ba?

yace yimin shiru kamin in da'da maki wani yar kaniya kawai,me kwakwalwar kifi Allah dai ya bude maki wannan toshesshiyar kwakwalwar taki.

kuka ta fara yi tana buga kafa ni Gaskiya baba kwakwalwata ba a toshetake baaa😭 inna tace ni yimin shiru karki taramin makwabta ehe.

Murya ta kara baba yace bari kiga ikon Allah mikewa yayi ya dauko sanda.
yanda Kasan Anyi ruwan sama an dauke tsit ta shanye kukan da takeyi tana tsitstsilla idanu tare da sheshsheka baba yace banson jin sheshekar nan. Ki natsu bari inga tsiyar da kika shukowa mutane wannan karan.

Mutum bashida aiki sai fada ni Nayi mamaki ma yau kusan sati 2 ba'a kawo kararki Ba.
Turo baki tayi duk yasha mai sai yalki take tace yo ai dannayi mafarkin na mutu ne kuma ko yanxu ma Ba fasawa nayi Ba.

Kallonta baba yake har ta ida maganan ta already ya Ciro takalmi Dan haka ya lafta mata.

papers din ya fara dubawa yaga  subjects 2 ne takeda A amma saura Wai sai a slow saide rubutun nan war inka gani zaka dauka wata Dr ce tayishi sai ka karantawane kaji Kamar kayi kuka.

takaicin rashin kokari na diyartasa abar kaunarsa ne ya taso mai.

Kansa  kawai yake girgizawa saboda takaici bazai musaba Idan akace masa Dan primary five ma yafi yar tasa kokari.

Tsawa ya daka mata ke zonan !
Simi simi taje ya kalleta sannan yace yanxu ke ahakan zaki tafi makarantar gaba?ki Duba fa gododuwar banza da wofi. Murmushi tayi
inna tace Allah zanci mutuncinki ana miki fada kina dariya saboda kin daina mutane ko? Tace Toh Toh Toh ni inna me Nayi ? Dakuwa inna ta mata tace kaniyarki kikayi

tace to yi hakuri bazan kara Ba shikenan aiko?yauwa inata Dan Allah ki siyan awara?harara inna ta banks mata tace ba'a siya dinba
Baba dake jinsu  ya tattare takardun yana cewa ace mutum anmai repeat har sau biyu amma bai gyara ba nasan duk ajin keda zaliha kun fisu girma amma kanku Kamar kifi har gara ita akanke.
antara dakikai biyu a aji daya bakuda aiki sai ciye ciye kuma da kunada kokarinku tunda kuka fara Hulda da wannan fatiman shikenan lamuranku ya tabarbare.

tace toh Ba kai kake Bani kuddin Ba? Kuma ai fatimamma sun Koma kano.

Yace au haka zakice?

Inna tace kaga malam rabu da ita kar hawan jininka ya tashi
Mika ma innatakardun yayi yace jeki ajiye min adakin ki Dan in ina ganinsu takaici ne zai kasheni

ni inanan ina fafitikar biya miki WAEC kan arufe amma naga alama asara zanyi

Zama kusa dashi tayi ta Washe baki tace baba kawai ka barni in fara aiki a gidan abinci Dan Gaskiya ni karatun bokonnan sai a hakali bazan maka karya in batama lokaci da dukiya ba yasin dakyar in zan hada ko credit 4 me kyau a wannan WAYES din
Yasin Gaskiya kake fadi kwakwalwartawa a to she take nakifinne maganarka Ba karya.

Abin yaso bashi dariya amma sai ya Girgiza kai

yace ai ga irintanan ana WAEC kina WAYES dubaki ko ajikinki Yan ajinku zasu makarantar gaba amma ke oho ko ?kinacewa inbarki Kiyi aiki a gidan abinci

Bakiji abinda ya faru da salma Ba ko 'yar gidan malam ado ?tana gidan ubanta ma ba'abarta Ba balleke budurwa kin tallata kanki a gidan abinci
Nan ya labarta musu abinda ya samu salma sannan yace Suma suje suyi ta'aziya.
Inna kam salati take harda kwalla tace kai duniyar nan Ba imani.

Minal ko mikewa tayi tana bubbuga kafa tace Toni baba idan ma bazaka iya barina inyo aikin Ba kawai kamin aure ka huta
Ai da gudu sukayo kanta ba shiri tayi waje tare da Jan mayafi akan igiya.
Baba yace da shegiyar kazanta ma wa zai soki?ja'ira yar kwal uba
Inna tace abita da addu'a da fata na gari kawai.

🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀

Wakarta takeyi tana tafiya ta hango murtala da wani abokinsa mai kawo masa ziyara babba yake kowa?waishi a dole Santa yaje. Zukar sigari suke Suna busa abarsu.

Tsayuwa tayi a wajensu tace anya murtala kanada hankali kuwa kullum kayita busawa 'ya'yan hanjin ka hayaki Kana biyewa wannan sha katafin?

Dariya ya bushe dashi kamin yace minal kenan ai na Fiki  hankali ma. Babba yace ke yar shila karki kawao mana raini Anan fa ko kinga sa'anki ananne?

Bata kulashiba taci gaba da yiwa murtala magana da tayi:
Dalla tafi can wallahi baka isa ba kayi kadan.

Kaikuma ta nuna babba da yarda kama daina nuna ka sanniwata kila ma sanadinka ne samari basa kulani to ka kiyaye ni.

Babba ne ya bushe da dariya Hahaha sannan yace kinfaiyi kwantai babu mai sonki sai yawo a unguwa

Dariyar takaici ta kyalkyale dashi kamin tace kaji banza botorami, yo da na Sauri miji irinka a gara na zauna Ba aure sha katafi kawai. Kuma in mijin agidan uban mutum ake rabawa sai ya hanani.
Murtala yace Ke yarinyannan zanyi maganinki fa, abokin bawa kuke fadawa maganar banza?

Minal tace da wacce itaciyar zakayi magani na? Kasan ni annobace da banida magani. Nan gani nan bari dumamen mayya in fada ma.

Murtala yace  kinci darajar babanki mutumin kirki ne kuma banason rigima yau da kinga yadda ake balla kafar yarinya. Tace yo inba tsoro Ba kamaso mana wallahi kaga yadda na fito dinnan babu mutunci.... Mtsw ni banma da lokacin Dan shaye.

Tafiya tayi abunta,babba Wanda ya tsaya yana kallonta sai alokacin yace kai murtala babe dinnan tayi aradu. Kaga jiki me kyau kuwa........

Tsaki murtala yaja kamin ya tashi yabar wajen yana gunaguni akan irin yadda babban ya nuna halin ko in kula gameda abinda minal din tamai.

Show some by
Sharing
And
Commenting...

27th April, 2019.

Mzz untichlobanty💕
[1/11, 1:12 AM] Mzz_Untichlobanty💞:

*🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆*

🌹by mzz_untichlobanty🌹

*🍀CHAPTER 4🍀*

*UNGUWAN SARKI,KADUNA STATE.*

Unguwa ne hadadde da manya manyan mutanen Nigeria masu matsayi da kudi ke zama,unguwa ne na wadanda sukakai a dama dasu.
Wani mansion ne dankararre Wanda yaji kayan alatu na duniya

Wasu mutane ne ke zagaye da gidan sanye da uniform daga ganinsu kuratan sojoji ne irin masu gadin gidajen oganninsu nan gaban gidan faranni ne of different colours and nature sunyi das das dasu sun kawata gidan
Wani katafaren gate nagani black with a touch of golden ta gefe naga an rubuta JEEDMAR on golden plate

The house has single side but classified into 3 which contain 12 fully furnitured bedrooms
with bathrooms in each containing fully jaccuzis and all other necessary things,3 parlours with cotton softened chairs,beautifully decorated dining room with a 10 people dining table,mordern kitchen,fully equipt gym room,sports field,3 swimming pools of different shape,size and designs,fully flowered and fruited garden,office dinshi,car parks with the most latest and expensive cars parked in,securities' side,workers'(helpers') side.

Motoci ne guda 11 suka shigo gidan sunyi convoy dukan su bakake ne banda na tsakiya Wanda yake fari wani kurtun sojane yazo ya bude motar
Wani kyakkyawa,dogo,fari,mai saje,ga diri tabarakallah masha Allah Kamar balarabe ne naga ya fito sanya yake cikin kayan sojoji fuskannan a daure babu alamun wasa ko kadan dukka sojojinne suka Sara masa a tare baiko kulasu Ba ya shige ciki abinsa.
Chapter 2 · 0% Book details