← Book details Kuruciyar Minal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 80

Sashe 45

Kuruciyar Minal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cilli tayi da wayar kamin tayi ruf da ciki ta fashe da kuka yanzu zakiyya da ke ta bata hope itama abubuwa sun cabe mata kai maza ba tabbas.

(kaji irinta ai wannan babban matsalan mata ne basusan me ake kira uziri da Daga kafa ba)

Abangaren minal kuwa daukanta yazeed yayi ya kaita dakinta bayan ya shafa kan safwan tare da Pecking dinshi yace yaje wurin mommy dinsu. shi kuma ya kira doctor Muhammad ya sanar dashi abinda ya faru. Bayan wasu mintina sai gashi yazo gyara akayi wa minal sannan aka bata magunguna. Dr Muhammad yace Toh yanzu zan barku da nurse zatayi mata allura. Kalmar allura ce ta fada carat a kunnen minal hakan yasa ta bude idonta war ba tareda ta Shirya ba. Hawayene ya fara sauko mata bawai Dan zafin ciwo ba sai Dan batada kafan gudu. Yazeed ne ya zauna a gefenta yace haba yar minal dina so kiji. Rungumota yayi cikin muryan kuka tace wayo zakamin ko? Girgiza kai yayi yace ni na isa ai Saide kiyimin wayo amma ke ai babu Wanda ya kaiki sense ga nutsuwa,ga tarbiyya,ga kyau,ga sanin ya kamata ko yar inna? Tace eh amma ni yar inna da baba ne. Yace Toh yar inna da baba zaki iya sakeni an gama tace me? Yace allurar. Zaro ido tayi aiko nurse ta gani tana kokarin yar da sirinjin . tace har Anyi Wai yace eh har an gama shirin kuka tayi tace dams Nasan wayo zakamin yace to ai gashi an wuce gurin ko tace emm. Yazeed yace yadai naji kin sake jikinki? nurse tace allurar danayi mata can lead to bacci though ba na bacci bane. Aiko koda ya kalli fuskan minal har tayi bacci gyara mata kwanciya yayi sannan ya fito domin ya raka Dr Muhammad dadi lokacin su mom suka shigo.

Gaisawa sukayi da Dr Muhammad mom na farin Muhammad Dan albarka zaka wuce kenan yace Insha Allah tace to ba damuwa Allah ya taimaka.

Fiki yazeed ya janyota tare da rugumeta sosai tace kai Dan sakanni kadan karka tatsemin hanji. Dariya suka fashe dashi nan suka gaggaisa mom tace ina matan naka? Yace Suna daki yanzu ma karamar ta Dan sule taji ciwo a kafa shiyasa ma kikaga Dr yazo. Mom tace subhanallahi muje in ganta. Yazeed yace ai bacci takeyi.

Jamal yace my guy ka fadi Gaskiya Baja ragawa yar mutane ko ? Sauri mom tayi ta dale sama tana farin ni kunga tafiyata yayinda yazeed ya harari Jamal yace matsalata dakai bakasan lokacin wasa ba. Jamal yace sorry abokina.

Bayan 10 minutes mom ta sauko ta sami yazeed da Jamal Suna kallo a parlour tace kai Jamal tashi muje mu karya kumallo.

Juya kanta tayi wajan da YAZEED yake zaune taga wayam tace ha'a ina kuma yayi? Jamal ma kallon wajen yayi abin Kamar tafi basuga sanda ya tashi ba balle yahau sama. Tace baki jamal yayi yace kika bibiya yaje ya damu yar mutane ne amma mu Duba jikinta zamuyi ance batada lafiya. Mom tace kaide ka Shiga uku,Ni babu ruwana.

Abinda basu saniba kuwa mom tana fara maganan abinci yazeed ya mike da Sauri Kamar zai tashi sama ya nufi dinning ya dau plate ya ajiye a gabansa tare da rike suka da fork su mom kawai yake kira.

Mom Suna shigowa ya sauke ajiyan ajiyan zuciya mom tace yazeed?maza ara huna(me nake gani anan) Yunwarce? Daga yanda take magana zakaji tsuran mamaki a muryarta.

Washe baki yazeed yayi ba tare da yayi magana ba. Yazeed yace bari in kira su tala suyi serving mom tace bari kawai zanyi kasan a can bana motsa jiki kwata kwata.

Bude flasks din tayi taga alala tace yanzu ne gida ya zama gida. Sauko gida daya tayi sawa Jamal sannan ta saka masa sauce yayinda jamal ke fadin Gaskiya amarya ta iya reno mom kin lura da yadda wannan abin yayi kina kuwa?yazeed yace nine Abu?mom tace zaku fara kenan ko? Su kace sorry a tare. Kwalli biyu tasa a plate dinta sannan ta rude flask din Sauri yazeed yayi ya riko hannunta yace mom ban gan ganeba. Tace kamarya ?yace nifa? Tace kai me yace abincin....

Jamal Wanda ya kurbi kunu sanda ya kware yana tari yace WHAT? Abincinnan zakaci alala ne fa. Yace babu ruwanka. Mom Kamar an zuba mata ruwa a jiki ta bude ta yanko rabi'u tasaka masa.
Murmushi yayi ya karbi serving spoon din ya zaunar da ita.

Gida 4 ya zuba tunda na gwangwami ne. Mom batasan sanda cokalin ta ya fadi ba.

Adan tsorace ta taba goshin sa amma lafiya lau yake shikam jamal dama ya bar Komai ya ninke yana binsu da idanu.

Murmushi yazeed yayi yace sweetheart zauna lafiya na kalau.
Zama tayi ta fara cin abincin Adan tsorace yazeed ya cika mug dinsa da kunu sannan ya fara harba loma kan kace me ya tada alale guda 2.

Sanda ya cinye Tass ya shanye kununsa ya kalli su mom yaga Jamal ko canja position dinshi baiyiba balle yaci abincin mom ko tayi tagumi ta saki baki.

Knocking table din yayi  mom sai alokacin ta lura da tagumin da tayi gira ya Daga musu alamar yadai ?
Mom ta girgiza kai yayinda Jamal yafi gaba dacin abincinsa.

Shikam yazeed alale guda 2 ya dauka ya nufi dakin minal domin ya tasheta taci abinci dukda sama allurar da akayi mata ba'a bukatan aci abinci.

🌹🍀🌹🍀🌹🍀

Zakiyya ko kuka take rizga sosai sahir yace ki rabu dasu momy Daga yau bazan kara kula brother safwan ba. Girgiza kai zakiyya tayi tace don't say that kaji he is your brother I will talk to him okay? Yace Okay. But...... Tace no buts.

🌹🍀🌹🍀............

Zaune take kan kujera ta mimmike kafafu wayanta akan kunnanta tace GET READY FOR THE NEXT PLAN....

WAITING FOR YOUR COMMENTS👁👁

Bari naga comment din waye yafi dadi in masa kyauta me girma.....

Takuce karamarsu babbarsu miss untho...

*my apology FANS bana celebrating new year so karkuce ban muku wish ba.*

mzz_untichlobanty💕

1 January, 2020.

*??KURUCIYAR MINAL??*

?by miss untichlobanty
?

*?CHAPTER 61?*

Make sure kunyishi ba tareda wani kuskure ba!
Ta dayan Abangaren akace yes ma an gama.
??

Ayush ne ta Shiga dakin zakiyya tace sister zakiyya tace yes kina bukatan wani Abu ne?

Still idonta Adan kumbure. Kamo hannun zakiyya ayush din tayi ta zaunar da ita a bakin gado tace sis nikam tunani na zauna Nayi naga Cewa tunda dai kishiyarki ta rusa miki gida nima an kwacemin saurayi why not muje mu nemi taimako.

Zakiyya tace taimako kuma? Wani irin taimako ? Gyara zama ayush tayi tace akwai wata kawata tacemin akwai wani malami aikinsa Kamar yankan wuka. Indai kikaje wajensa Toh matsalarki tazo karshe ga aikinsa babu wani tsada kuma ance.....

Zakiyya tace dakata! dakata!! dakata!!! Ke yanzu da ilminki da wayewarki zaki dinga yarda da irin abubuwannan ?kuma wa yace miki malamine? Boka ne shi babu wani malanta fakewa kawai yake a inuwar malantaka.
Yanzu ke akan abin duniya kikeson Nayi shirka? Toh bankai nan ba bari kiji tun wuri gara ki cire wannan Abu a ranki ku ko a modern way ai that is madness ba class dinki bane please! Use your sense duk macuta ne malamannan.

Ajiyan zuciya ayush ta sauke tace kuma fa Gaskiya kike fadamin da na kusa In tafka babban kuskure amma na gode da kika fada min Gaskiya Allah ya saka da alkhairi.

Shafa kanta zakiyya tayi tace what are sisters for?Idan ban fada ma little sis dina Gaskiya ba wa zan Fadawa ? Dariya ayush tayi tace am not that little fah. Shekaru nawa ma kika bani ko 9 bai kai bafa.
Dungure kanta zakiyya tayi tace munji dai na girmekin Ashe.

Dan abin tausayi ayush Tayi tace sis Dan Allah Kuban key din motanki inaso inje in siyo wani abu. Zakiyya tace ki bayar a siyo miki mana yaushe muka iso garin ai akwai gajiya. Ayush tace abin is a little bit private kinga ne ai? Zakiyya tace okay bari in canja kaya muje tare mana nima dama inason inje shopping ayush tace yanzu fa kikace akwai hajiya ki bari gone sai mu fita ko? Zakiyya tace to kije dasu sahir mana kinsan birthday din sahir ya kusa he will be six years next month. Ayush tace nima ba dadewa zanyiba, gobe ba sai muyi Komai da Komai ba?

Zakiyya tace okay ba matsala amma karki Dade fa.
Ayush tace okay na wuce Toh saina dawo.

Fita tayi tana tafiya tadan kunna waka tana gyada kai abinta tana rausaya wa. Birki ta taka taji shiru kara takawa tayi still taji shiru ihu ta fara yi yayinda Motan ya fara kobo da ita akan titi.
Bata ankare ba motanta ya Shiga kasan wani trailer.

Mutane ne suka cika wajen makil ga hasken rana ya dallo wal bari yayi zafi Motan da ayush ke ciki bazaka dauka mutum zai fita ba saboda yanda Motan yayi raga raga ga ayush kwance agefe cikin jini atake akayi asibiti da ita.

Wayanta wani ya dauka wayar ma tayi raga raga. Cire sim din yayi yasa a wayarsa sweet sis ya gani Dan haka ya kira

Zakiyya zaune akan gado tana sulhu tsakanin sahir da safwan Cewa Idan suka raba Kansu kowa zai iya Shiga tsakanin su Wayanta yayi ringing ganin ayush ne yasa ta dauka da yar fara'arta amma labari da ya risketa shi ya gigitata tana kasa yin Komai.

Tashi tayi a zabure ta fice ta zauna dabas a parlour Kamar yar bori ta Cire wig dinma Ashe tanada gashi ba laifi rashin godiya wa Allah yasa ta yin karu ihu ta fara yi

Waiyo Allah na,na Shiga uku!YAZEED ka taimakamin yar mutane shikenan ta mutu !ta mutu waiyo ni Allah na.

????????

Yazeed zaune a gefen minal fuskannan babu alamun wasa hannunsa rikeda takalmi. Minal ma fuskannan babu fara'a sai zunburo baki take Wai saboda dance taci abinci kamin yaje wajen mom Idan ba haka ba tasha takalmi.

Ihu suka fara jiyo sama sama yazeed ya ajiye takalmin ya nufi kofa yana farin wannan Kamar muryan zakiyya minal ma dauko sandan ta tayi tana fadin aiko itace.
Chapter 45 · 0% Book details