← Book details Kuruciyar Minal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 80

Sashe 77

Kuruciyar Minal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sigina summy ta Mata cikin tsokana yace wata ta kagu infita toh yanzu zan wuce. Tsaki minal taja tana dariya ta jefe ta da pillow tare da fadin ki rufe mana kofa de. Bayan ta fita jugum minal tayi yazeed ya riko hannunta? yace karki damu komai yazo karshe da izinin Allah wahalar ki ta kare zo kiga wani Abu ya fadi hakan yana janyota jikinsa..........

ABINDA ya faru kuwa shine tun a can baya lokacin da alama su minal munafurci kasa kasa yazeed ya soma bjncike kamar yadda kuka sani Wanda hakan yasa ya zargi goje cewa shi ya saka musu kayan Maye abin sha Dan basuda wani makiyi sai shi. Garin binciko ne ya gano cewa goje (Dan uwan lailai matar ya Abubakar wanda har yaso ya Mata fyade Allah ya sha da ita.) yana auren ayush kanwar zakiyya abin ya bashi mamaki sosai. Hakan yasa ya hada one plus one dinshi yadda akasa lukman ya auri zaliha maybe shiyasa take daukan fansa hakan yasa ya zurfafa bincike Dan ya tabbatar kar yayi kuskure toh amma yana bukatar Wanda zai shiga jikinta ana cikin haka har wata rana summy tazo neman aiki amma babu vacancy.

Marainiyace daga ita sai mahaifiyar ta mara lafiya hakan yasa ta hakura da zama babbar mace ta nemi aiki a companyn yazeed. Sosai ta bawa Jamal tausayi yake bawa yazeed labari nan yazeed yace ya nemota akwai aikin da zata mai.
Koda tazo yazeed ya sanar da ita yadda zatayi ta shiga jikin ayush har ayush ta yarda da ita ta dinga bata mission sannan ya Mata gargadin kisa idan tayi kuskure tunda lokacin ko tunanin retire baiyi ba. Ita kuwa abin nema ya samu dama yar karya karya ce amma ba yar lesbian ba. Ta zama yar lesbian ba karya ne duk a cikin shirin yazeed Wanda minal ce ta bada shawara.

Numbar ta ya karba sai yaga ashe ma yana da ita. Numbar da ke chatting da zakiyya ne lokacin da zatayi tafiya. Yace menene hadinta da zakiyya? Tace kawai ita burinta ta dinga shiga cikin manyan Mata hakan yasa duk group din da akwai manyan Mata toh sai tayi karya karya ta samu ta shiga anan ta samo numbar zakiyya yazeed yace matarsa ce zakiyyan Dan haka tayi hankali.

Ana cikin haka ne har ayush din tasa summy tayi kamar tayi zina da zakiyya da sauran duk abinda ta sata yayinda take surfowa su yazeed rahoto su kuma sunata tara shedan da zasu bawa zakiyya si nuna Mata cewa yar uwarta ba yar uwarta bace kuma ba mutumiyar arziki bace saide kash suna planning su tona Mata asiri idan minal ta haihu ranan suna a Mata tsamo tsamo amma kafin sukai ga yin haka tayi musu tsafi.

Bayan sun warke kuwa gani sukayi tunda batasha jibgar gidan suna ba dole su Rama abinda ta musu kamin su Dan ka ta hannun yan sanda ayi kasheta tunda itama ta kashe jarirai.

Acikin gaba daya tafiyar rayuwar sun nan akwai muhimmin Abu da suka fahimta. KAYI KOMAI AKAN LOKACIN DA KAKE DA SHI DAN BAKASAN YA GABA ZATA KAYA BA KARKACE ZAKA JIRA WANI ABU, SANNAN DUK WAYONKA BAKA IYA TSALLAKE TSAUTSAYI DA AJALIN KA.

Abinda summy ta fahimta kuwa shine DUK LOKACIN DA KA DAGE SAI KA SAMU ABU TOH WAHALAR BANZA ZAKACI KO KA SAMU BE ANFANE KA BA KO BAZAKA SAMU BA. LOKACIN DA KA KOMA GA ALLAH KUWA IDAN YAGA DAMA YA BAKA ABINDA KAKE NEMAN A DUNIYAN KUMA YA KARA MAKA DA ALKHAIRI A LAHIRA. Matar da ta taimakawa mom tabar gidan mahaukata kuwa ba kowa bace illa mahaifiyar summy wayo sumaiya. Yazeed ya biya Mata kudin magani ta warke har ya nema Mata aiki amma bayan wasu shekaru ta rasu.

CIGABAN LABARI

safina asararriyar matar yazeed tana baccinta me dadi take jiyo hayaniya sama sama har ta farka jin mommy ce yasata yin tsaki tace tsohuwar nan zan Mata wulakanci wallahi bazar bazar ta shigo dakin mummy ta sameta shaman cikin fitsari tana mazari tsabar tsoro.

Tace tsohuwar munafuka ya akayi mummy tace kinga yar albarka safina taimaka ku ciro ni. Safina tace jibgegiya dake saide in jaki mummy tace nide cireni daga bayin nan kinji matar kirki. Tace badan halinki ba kawo hannunki. Sannan ta taimaka Mata gyara jikinta tayi sannan suka zauna a bakin gado yadda kasan shiri sukeyi tun da.

Cikin son jin labari safina tace wai ya akayi ina aishar? Mummy tace ke bar batun yar iskan nan ai yau na leko barzahu na dawo. Safina tace ban gane ba labarin tass mummy ta tsara Mata ta nutsu ta shanye tas sanda mommy ta gama tace kuma sai akace miki zan yarda? Kai mummy kin iya hado ta mummy tace nima ban yarda da ayush ba sanda na gani.

Yin duniya mummy tayi safina bata yarda ba daga karshe ma dariya ta sheke dashi ta koma dakinta. Ta kwanta tare da kashe wuta ahankali ahankali iska ke kadawa a jikin labule yana kara karfi kofofi da da taga ne suka fara kara ga bakin kura yana kadawa hajaran majaran. Ruwa mai karfi ne ya tsinke tare da cida daidai lokacin kuma yazeed ya sumbaci minal yayinda safina............

???BANCEWA KOMAI KAWAI KAR KU MANTA DA VOTING, COMMENTING TARE DA SANAR DA KAWAYEN KU SUMA SU KARANTA.

ALLAH TA VAR JAUNA SANNAN YA KARBI IBADUN MU BAKI DAYA.

Miss untichlobanty ?

17th may, 2020.

? *CHAPTER 95*?

Yin duniya mummy tayi safina bata yarda ba daga karshe ma dariya ta sheke dashi ta koma dakinta. Ta kwanta tare da kashe wuta ahankali ahankali iska ke kadawa a jikin labule yana kara karfi kofofi da da taga ne suka fara kara ga bakin kura yana kadawa hajaran majaran. Ruwa mai karfi ne ya tsinke tare da cida daidai lokacin kuma yazeed ya sumbaci minal yayinda safina............

A bangaren ayush kuwa aljanin nan daureta yayi kullum zaizo ya sha jininta bayan azaba da yake Mata da wuta tare da bata tafashasshen ruwan diwa mai jini da azabar wari. Gashi bata ganin komai sai jarirai. Kullum tamabayar ta me tayi masa? Ganin ta dameshi yasa yace ke saurara kiji, nine aljanin da aka tura na mantar da kowa da sharadin duk randa suka sake yin aure zan rasa nawa auren ba wannan kadai ba matar tawa ni zan kashe da hannuna.
Dan haka yanzu na rasa matata, amarya ta a sanadin ki shiyasa ya zama dole ki zauna da ni.

Kuka ta fara yi tana bashi hakuri shikam ko ajikinsa. A kwana a tashi babu wuya har wata daya ya shude. Su minal sunje sunyi ma ummu amina godiya sosai na yadda ta kula da minal inda yazeed ya dauki main aikin da za'a Mata. Anan suka samu sabi'u wagon sabi ya makance. Ummu amina ke sanar dasu AI tun randa minal tasa kafarta tabar gidan yake kuka ashe yana sonta kawai haushin mijin da ya AURETA sannan ya wulakanta? ta ahalin tana dauke juna biyu yakeji. Hakan yasa yake sauke haushin akan yaran.

Talauchi da yanayin rayuwa tasa yake dabanci amma deep down can cikin zuciyarsa mutumin kwarai ne. Yayi kuka har ya gaji har ya kasa controlling hawayen sa. Hakan yayi sanadiyyar makancewar sa cikin shekaru 4.

A yau ne ta kasance an bawa su zayya hutu zata dawo gida yayinda sahla kuwa dama day takeyi Dan haka kullum zuwa taje ta dawo ne amma dai tare akayi hutun Dan makaranta daya ne.

Kuma a yau dinne LUKMAN da matar sa kuma aminiyar minal ZALIHA zasu dawo kasarsu ta gado wato NIGERIA.? Saide su Allah da daya ya basu dukda cewa karami ne shekarun sa bakwai. Amma har yau fa jiya I yau ne kullum sai sunyi rigimar nan dai tasu.

Minal an cakare anci ado sai walwali take tana ta zirya tsakanin kitchen da dinning room zakiyya ce ta shigo da abun koyar tafiyanta Dan shekara 15 a zaune ba wasa bane. Mashkur yace suma gode Allah akwai hope zata iya taka kasa Dan yanzu leave shima ya dauka yazo zai Dan zauna da su yazeed a sake karfafa zumunta da shakuwa.

Hira suka fara ita da minal suna jimamin ko? ina ayush ta shiga? Zakiyya? tace ke ni bar banza AI wallahi ma taje Allah kiyaye hanya. Minal tace uhm uhm fa idan kuma taje ta bata rayuwar wasu yanda taso yi wa namu fa? Zakiyya tace? kuma fa maganarki gaskiya ce toh amma... bata karashe ba sanadiyyar Umma hani da ta shigo da saurin ta tana? fadin uwar daki akwai matsala banga hajiya ba. Minal tace ai hajiyoyin maki yawa garesu wacce ? Tace hajiya babba mana na duba...... hayaniyar da suka jiyo ta window din kitchen yasa ta yin shiru kamin suka fita.

Aikuwa mummy ce ta tattare zani tana sharar gudu kamar mota sharon.kai kace standby generator aka jona Mata ga security da masu aiki sunyi ca sai binta suke amma ta file musu.
Waje ta fice ta ari titi suna bin ta a baya.?? Ba komai take fadi ba sai kai jama'a ga mutuwa ga yan boko haram, ku gudu.

Irin yan acabar nan sun taru dama kawai sukaga Mata cikin kaya mai tsada harda sarkin gwal tana gudu tana fadin ga mutuwa shiyasa kafa me naci ban baki ba? Gudu suma suka fara, wasu nayi adungure su diro daga machine din suyi kolin koli su kwalu da kasa sannan su Mike su cijewa rigar su iska. Irin stop stop dinnan na yan napep suka wuce shugaban wajen sunan shi dogo me babban Riga.

Ana cikin cakwakiya da shi akan kudi ya sakami mai napep kenan zai nana da kasa yaga taron mutane ana gudu cuceshi kawai ake wani fiwt ! Fiwt ! Kakeji abinda akee fada yaji aiko ya sako mai napep din dam a kasa ya fita da gudu shine a gaba gashi yafi kowa tsayi rigar iska ta cikata ji kake fafar? fafar baka ganin komai se babbar rigarsa yayinda yake sambado gudu zundum zundum.

Inyamurai masu saida doya sukazo wucew inyamurar ka bajin hausa suke ba amma sunji Boko haram take suka bi ta Kan doya yayin da mamar su tsohuwa kafa ya hau mazari ji kake curr ta saki fitsari.
Chapter 77 · 0% Book details