← Book details Kuruciyar Minal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 80

Sashe 64

Kuruciyar Minal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A bangaren su yazeed kuwa bayan an cirewa minal bullet din ta farfado yazeed yana bata shayi sukaji hayaniya a hall din asibiti,saukowa minal ke kokarin yi daga bed dinta yazeed ya kwantar da ita kuka ta fara masa wai tanason ta gani dan haka ya dauketa suka fito Dan sandan nanne suke cakwakiya da sojoji zasu tafi dashi Dan ya harbi matar oga yayinda yake kuka yana fadin bashi ya harbeta ba. Yazeed yace a dakata. Tsit kowa ya yi yazeed ya iso gaban shi yace :kace ba kai ka harbeta ba? Da sauri gyada kai yazeed yace idan na gano kai ka harbeta wani hukunci zan maka yace a tsire ni.

Yazeed yace a kai bullet din da aka harbeta da kuma bullet din bingigarsa a duba su shi kuma kar a tafi dashi a mayar dashi daki aci gaba da kula dashi.
Koda aka Dubo bullet din ba na bindigar sa bane nan yazeed ya fara tunanin yadda zai gano na waye tunda yan sanda ke duba wannan kuma yan sandan ba mutuwa dashi sukeyi ba.

A kwana a tashi minal ta warke yau aka sallamo su kuma basu fadawa kowa abinda ya faru ba especially mom saboda kar hankalin ta ya tashi.
Marhaba umma hani tayi musu tare da sauran masu aikin inda sukayi musu jaje. Su nason minal sosai saboda kirkin ta.
Washe gari zabe? dan haka yazeed yace wannan shekara bazasuyi Zane ba saboda tsaro kar a kuma kawo musu hari. Sabon president yana zuwa ba tare da bata lokaci ba yasa akayi dismissing case din saboda ya gano rashin gaskiya kawai akeyi. Anan ne yazeed yayi resigning.

Mr. President yayi bakin ciki na rashin jami'i mai gaskiya da amana Dan haka ya hada masa taron bankwana a wajen taron ne aka Kira yazeed domin yayi jawabi cikin jawabin Nasa ne yake cewa zai koma ya kula da hard work din mahaifin sa kuma insha Allah? daga ranan har tashin kiyama baya fatan shi ko wani a zuri'arsa su kara involving kansu da government business kawai zasuyi kuma individually zasu dinga taimakon kasarsu ba sai sun tsunduma kansu a cikin ba idan an nemi gudun muwarsu toh zasu bayar. Idan sunga ana Abu da ya Saba doka toh zasu yi magana.

Kuka jama'a keyi wiwi! Anan taron ne akayi presenting award of excellence ma yazeed as the BEST MILITARY PERSONNEL of the year. It was a heart touching moment,box daya na tissue paper na karad saboda kuka anan ne nima aka bani award Dina as THE BEST FICTION WRITER of the year. Muka ci abinci muka sha sannan muka watse ana ma juna fatan ALKHAIRI.

Washe gari da safe suka lulu suka dawo Kaduna domin yazeed yayi shirin fara aiki as JEEMAR GROUP PRESIDENT yayinda minal taga cewa ya kamata su ciyar da almajirai domin godiya ga Allah Dan haka asabar din data kewayo ta Nemo tsofi 20 aka fara girki. Manya manyan tukunya fiye da lamba hamsin guda 20 aka daura kenan ko wacce tsohuwa 1 tukunya 1, yayinda aka biya ko wacce dubu hamsin kuma anyi haka ne Dan a taimaka ma tsofin ma.
inspection minal tazo yi yayinda take testing ana bude tukunya farfesun kaji ta hau kakarin amai. Dannewa tayi ta dandana ai take ta fara amai ba sassauci nan hankalin tsohuwa ya tashi itakam kashinta ya bushe.

Kowa ya rude ya rikice aka samo likita ta dubata tace yuzu dai she can't say amma tana suspecting ciki ne da ita dan haka aka bata pregnancy test tube aikuwa positive. Nan shagali ya karu murnane ba'a cewa komai, run saga ranan minal batada aiki sai cin gurasa da zogale.

BAYAN WATA 7

Minal zaune akan gado ta mimmike kafa bakin nan cike da gurasa da zogale yazeed shigo ya zauna a gefenta,daura kafafun nata yayi a cinyan sa yana Mata tausa saboda sun Dan kumbura yace mummy gurasa na shirya sai tafiya turo baki tayi tace daddy zogale ka tafi dani Dan Allah yace a hakan? AI idan na kaiki can zaki wahala ne gara nan akwai mom kuma ai bakuyi hutu ba karki damu yanzu zakiga weekend din ya kewayo na sake dawowa kinji? Tace Tom shikenan Allah ya tsare ya kuma kare yace ameen.

Saukowa tayi dakyar tare da kanka kwanta me kwabon zogale yazeed ya ja kumatun ta yace nikam Allah ya tunamin ranan haihuwar ki, irin wannan ci da kike yi zaki rakanin ma kina cin zogale cikin mamul mamul da baki tace babu ruwanka.?

Fitowa sukayi tibi tibi suna dariya har ya shige mota bayan sunyi sallama ya sauko ya rungume? ta tare da kissing gurasa da zogale (cikinta) yace bye bye my little babies da big baby dariya suka fashe dashi kamin ya shige motan suka wuce yayinda minal ta koma cikin gida.

.........................

Zaune take a kan gadon dakinta yayinda take hango duk abinda ke faruwa a farfajiyan gidan, aani Luna da tafarfasa zuciyar ta keyi kamar tayi hauka haka takeji. Fincike drip din dake hannunta tayi yayinda ta yage riganta jiyoyin kanta sun tashi cikin huci tace nayi regretting aurennan da nayi auren banzan nan da nayi shi ke hannu kusantar ka masoyi na yazeed. Ke kuma sh*giya sai na hallakar dake da wannan tsiyar dake jikin ki sannan ta naushi gini Wanda har jini sanda ya fito daga hannun ta inda ta lashe tare da cewa na rantse da jinin nan sai na kasheki.

WA IYAZU BILLAH!

Toh masoyana Rabin raina, a halin yanzu dai ba baku satan amsan wacece ita. Shin a ganinku wacece ita? Duk Wanda ta canka zanyi dedicating Mata next chapter.

Me Kuke ganin zai faru a gaba?idan kika canka zan miki kyautar chapters guda 3 a jere.

Shin labarin nan yazo karshe ko da saura?

Ina tsimayi amsoshin ku. Domin inyi muku wani update yau ina bukatar comments masu tsari

Kuyi sharing lungu da sako domin wani ma ya samu.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU wato

Miss_untichlobanty ?

11th march,2020

*??KURUCIYAR MINAL??*

?by miss Untichlobanty ?

*?CHAPTER 77?*

RECAP

Zaune take a kan gadon dakinta yayinda take hango duk abinda ke faruwa a farfajiyan gidan, aani Luna da tafarfasa zuciyar ta keyi kamar tayi hauka haka takeji. Fincike drip din dake hannunta tayi yayinda ta yage riganta jiyoyin kanta sun tashi cikin huci tace nayi regretting aurennan da nayi auren banzan nan da nayi shi ke hannu kusantar ka masoyi na yazeed. Ke kuma sh*giya sai na hallakar dake da wannan tsiyar dake jikin ki sannan ta naushi gini Wanda har jini sanda ya fito daga hannun ta inda ta lashe tare da cewa na rantse da jinin nan nawa sai na kasheki.

*CONTINUATION*

Jiki na rawa nurse din dake kula da ita tazo ta riko hannun ta dake zubda jini cikin harshen turanci tace ina rokon ki ki barni in koma kasar mu kar wata rana su gane ba a coma kike ba su kasheni dama ance yan ta'adda ne bakaken fata. Mari ta falla Mata tace ki iya bakin ki. Hawaye nurse din ta fara tace maza goge hawayen nan sannan kika sake wani ya gano me ake ciki ni da ke ne. Kamata ma yayi ki ji dadi ana biyan ki ba tare da kinyi aiki ba.

Cikin kuka nurse din tace idan yanzu suka shigo suka ga hannun ki da ciwa ta yaya zan fara bayani? Hankade ta tayi Tate da zama bakin gado tace gyara min hannu na.
Jiki na rawa kamar mazari haka nurse din ta fara dressing hannun nata. Itako tunani take a ranta kamin tace ni ayush nayi alkawari indai bazan samu yazeed ba toh babu mai samun sa kuma wad......

Ringing wayanta ya fara hakan yasa bata karasa maganan ta ba ganin goje love na yawo akan screen din yasa ta jan tsaki tare da dauka cikin murya my zaki tace my love! Ta dayan bangaren goje yace wifey wai yaushe zaki tashi daga jinyan karyan nan ne ? Nayi missing dinki fa.

Murmushi mai sauti tayi tace soon karka damu sai anjima banason su jiyo ni bye zan kashe wayan ne.
Wani tsaki taja tare da fadin kaina aikinka ya kusa karewa. A bangarenshi kuwa tunanin yadda zai kashe ayush ne da tayi taking control ta masa handing over.
Bokanta ta Kira sukayi kus kus Wanda nima banji ba. Tace shikenan ko da akwai wani Abu. Ta dayan bangaren boka mugu yace wannan aikin babba ne dan haka ina bukatar ki samo fatan farjin mace sabon gawa zan miki wani hadi sai kisa a cikin jikinta,ki tabbata kin tura sosai tace zan iya bayarwa ayi? Boka yace ko da wasa, da kanki zakiyi!
Tace naji matsalata dakai ka fiya tsauri, dariya ya sheke dashi tace dadi na fa? Tace aikin ka ba wasa.
Dariya suka sheke dashi mai ban tsoro Wanda yasa cikin nurse kadawa da daukan ruwa dukda cewa batamin yaren tasa ba abin arziki ake kullawa ba.

?wan?wasa kofan dakin da akayi yasata kwantawa yayinda nurse din ta lillika mata fake drip da sauran su.
Bude kofan tayi zakiyya ce ta shigo ta zauna a bakin gadon tare da shafo kumatun kanwarta tana Mata kallon so, kamar kullum yauma sanda ta tamabayeta yaushe zaki tashi? Hawaye ne suka dinga zirya a idanunta.

Bayan aani lokaci tace ma nurse din zata tafi nurse dai nata gyada kai ne Dan banda film bata taba ganin irin wannan mugunta ba.
Ayush kam tunani ta lula bayan zakiyya ta fita. Juyi tayi tare da tuno sanda ta fara haduwa da goje.

FLASH BACK
Chapter 64 · 0% Book details