← Book details Kuruciyar Minal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 80

Sashe 53

Kuruciyar Minal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanda suka jira ummi kusan 15 mins kamin ta fito kawaye sun Mata ca ta ko ina.
Gida suka nufa suna isa ta fice yayinda zakiyya ta fito a hankali abbansu ya lura da tafiyarta yace zakiyya lafiya dai ko ?me ya Sami kafanki Sosa kai tayi alamun karya zatayi tace faduwa nayi murmushi yayi Dan yasan ba haka bane kuma ummi nada alaka da wannan amma sai ya basar. Bayan sun shige ciki yace ta Kira masa ummin.

Kiranta tayi nan ma sanda tasha dunguri kamin ta fito. Kememe ta tsaya Akan mahaifin nasu. Tafi uku ya lafta Mata a jere sanda tayi adungure sallar mage kamin ya hau jibgarta.

Ihu ta fara tana neman dauki. Hakuri zakiyya ta fara bawa baban nasu tana kuka domin duk wulakancin da ummi ke Mata tana sonta.
Mommy dake sama tana baccin asara ne ta sauko tana fadin me zan gani haka Alhaji banson wulakanci. Dan bakasan zafin haihuwa ba yasa kake jibgar min yarinya ko? bakasan wahalar da nasha ba saide kaga na dirosu shine zaka........ itama mari ya yage Mata yace ke badawiyya ni ba mijin tace bane inada iko da gidana karkiga na daga miki kafa ko Nemi ki kawomin rainin hankali. Duk ke kika janyo yarinyar nan bata ganin kan uban kowa da gashi. Wallahi ko kiyayeni. Yana kaiwa nan ya fice domin an fara kiran salla.

Daki uwarsu tasa zakiyya dake ta kuka saboda batason taga iyayenta na fada ta jibgeta. Tun tana kuka har ta dena.

Washe gari ta tashi jikinta duk yayi tsami haka ta shirya suka tafi boko. Umar na tsaye a bakin gate domin both boko da islamiya makaranta daya suke zuwa. Ganin yanda jikinta yayi birtsi birtsi yasa ya jata lungu hankalinshi a tashe yace my zakiyya ya haka? Me ya sameki? Kuka ta fashe dashi kamin tace yayarta ne ta Mata hakan lallashinta yayi ta yi har sukayi missing first period.? Dukda cewa ya fita da aji daya a boko hakan bai hanasu zama tare ba. Haka yaci gaba da kula da ita a kwana a tashi har akayi hutu. Allah ya taimaka dukkansu iyayensu nada Karfi Dan haka suke waya ta land line ko kokuma su rubuta letter soyayya suke me tsafta kowa yana fatan idan sun girma suyi aure. Cikin Hutun kullum sai ummi tayi kokarin fita amma uban ya hana haka ta hakura saide Rama da Tasoma yi da alamu akwai abinda ke damunta.

Bayan sun koma islamiya da sati 2 aka Koma boko.
Suna shiga makaranta zakiyya ta tafi wajen farouq yayinda ummi ta nufi bayan ajinsu.
Wani matashi kamar Dan shekaru 17 ne yazo ya sameta ya tara afro a kannan harda sarka tana ganinshi ta rungumesa. Yace my baby! Wannan sati 3 da akayi a hutu bakiji yanda na keji ba kamar nayi hauka. Nan fa suka yi ashararancin su sai lokacin break suka koma cikin yan aji. Nan fa take cewa ina hilwa akace Mata ai hilwa tunda tayi ciki ubanta ya cireta makaranta cika baki ta dinga yi tana cewa Ai itakam ubanta bai isa ba. Nan ma yan clique din tasu staff room suka nufa ko wacce ta nufi wajen nata akayi zina aka kwashe kaya daga gaban annabi. Kuma a cikin staff room din kowa na kallon kowa bayan an gama wannan kuma Mata suka koma wajen Mata maza ma haka. Abin kazanta da kayan Allah wadarai. Matsalar da suka samu shine sun rufe kofofi da ko ina amma sunbar guda biyu.

1. Kofar Allah sun manta da cewa yana ganinsu a duk inda suke.
2. Akwai wata yar karamar window wacce basu rufe ba kuma duk abinda sukayi akan idon zakiyya da mardiyya.? Shiyasa tun daga Ranan Ranan zakiyya ta tsani duka biyu kuma yana daya daga cikin dalilin da yasa bata bawa yazeed hakkinshi.

Bayan Sati biyu lokacin birthday din zakiyya saura 1 week. Umar da mardiyya kullum sai sun hadu suna shirye? shiryen yadda zasu Mata surprise saide kash. Ummi ta kewaya ta nuna Mata amanarta Suke ci. Tun bata yarda ba har ta fara yarda domin duk sanda suka labe suna magana da tazo sai su canja abin na damunta. Ana saura kwana gobe birthday dinta tana zaune tana addua Allah ya taimaka Mata ya kawo Mata dauki ummi ta shigo. Dariya ta fashe dashi tace ke banziya ce wayace miki Allah zai jiki ko ya ansa addu'ar taki? Babu ko daya farouq dinki da mardiyya sunacin amanarki kuma ba dainawa zasuyi ba gobe ki ritsasu kawai duk sanda kika shiga matsala ba zuwa zakiyi ki shinfida sallaya kina addua ba aikin banza kike ai action kawai zaki dauka.

Da haka da haka ummi ta cirewa zakiyya son Allah a zuciya Ta gurbata Mata tarbiyya. Washe gari kuwa zakiyya tana zuwa ajin da ummi ta fada Mata ta Sami farouq yana taba kirjin mardiyya dukda ko kayansu yananan komai normal.

Nan take ta fara cewa ba ita basu sunci amanarta wa ya mutu wa ya tashi sannan ta fice tana kuka wiwi. Abinda bata sani ba kuwa shine wannan ajin da suke ciki nanne meeting point din duka yan ajinsu before aje school hall inda suka ara daga wajen makaranta domin yin Partyn.

Kan farouq ne yadau zafi ya fice bai ma san inda yake tafiya ba mota yayi ciki dashi kuma akan idon zakiyya domin taga sanda ya fita ta biyo bayansa. Da gudu ta antayo tana zuwa ta janyosa jikinta tana kiran sunansa dakyar ya bude bude idonsa. Kuka take sosai can ya fara magana kamar haka: "zakiyya kisani cewa tun kina nursery 3 nake sonki kuma har yau ban daina ba. Benci amanarki ba ki tambayi kawarki me mukeyi yan ajinku da ajinmu ma shaidu ne. Inaso ace mun girma......"? tari mai jini ya sarkesa dadai lokacin mardiyya ta karaso domin taga fitowar zakiyya sunansa ta fara Kira tare da cewa mai ta samesa kuka kawai zakiyya keyi tare da nadamar yarda da abinda ummi ta fada Mata tayi. Magana yaci gaba dayi "naso ace na aureki amma bai yuwuba inasonki wallahi ina... " kasa karashewa yayi tare da Kamewa can ta saki jikinsa da alamu ya sheka. Ihu ta fara kwallawa hakan shi ya janyo hankalin students aka fara fitowa me gadi na kokarin hanasu akayi sama dashi. Kuka zakiyya keyi harda shidewa mardiyya na tayata.

Aranta Addua take tana cewa Allah indai Kaine Allah ka dawomin da farouq Dina jin shiru yasa ta yarda da maganar ummi. Allah sarki anan ummi ta daura ta akan keken bera.

Tun daga lokacin idon zakiyya ya bude ta bankare itama abin kuwa ya kara karfi ne bayan ance an nemi mardiyya an rasa. Tundaga lokacin ta sauya saide dukda haka bata taba yin zina ba.

Bayan watanni aka gano ummi nada ciki. Hakan yayi sanadin zuciya mahaifinsu ta buga. Hajiya badawiyya kuwa tasa aka barar da cikin. Wasa? wasa islamiyar ma suka watsarta bokon ma zakiyya ce ta karashe ummi daga ss2 ta tsaya._

Koda zakiyya? ta gama bada labarinnan ta jikawa minal Riga da hawaye.? Lallashinta minal tayi kamin suka cigaba da sabgoginsu.

Koda zakiyya ta tambayi yazeed bai hanata zuwa gidansu summy ba domin dadi yaji atleast ta shiryu.

Jibi nayi saiga summy ta tazo daukan zakiyya aiko suka wuce gidansu su summy tunda suka shiga zakiyya yaji hankalinta bai kwanta ba. Drinks aka kawo Mata tasha kadan daganan summy tace "Muje ko? Tana dakinta ne" binta zakiyya tayi a baya haka dai har suka isa zuwa dakin suna shiga summy ta rufe kofa tare da wulli da key din. Kallonta zakiyya tayi tace ban gane ba Menene? kuma haka? A zafafe sumaiya ta hada bakinta Dana zakiyya atake zakiyya ta shiga wani yanayi saboda drink din data sha.........

TOH FA! SAI KU BIYONI A CHAPTER NA GABA DOMIN JIN YADDA ZATA KAYA A TSAKANIN SUMAIYA DA ZAKIYYA.

NA GODE SOSAI DA HAKURINKU NA RASHIN JINA 2 DAYS. INA MATUKAR YINKU IRIN TOTALLY DINNAN.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU

miss Untichlobanty ?

26th January, 2020.

??KURUCIYAR MINAL ??

?by miss Untichlobanty ?

?CHAPTER 70?

Rufe ido zakiyya tayi sakon da sumaiya ke aika Mata na ratsa and then it click to her Cewa wannan abin zunubi babba.
Babu shiri ta hankadeta tare da cewa me haka sumaiya ina maman taki?. Dariya summy ta sheke dashi tace shegiya ni. Ji muryarki yadda kike magana kamar yar kwaya tsabar jarabar Dana tado miki, wa yace miki inada uwa? Matsowa tayi kusa da ita tana yauki tare da shafo Fuskar zakiyya tace haba my zaky basai mun tsaya muna ja inja ba. Mari zakiyya ta yarfa Mata tace kin bani kunya wallahi am ashamed ashe ke fasika ce ban sani ba?kazama,dakikiya kuma jahila? Ke nayi miki kama da yar iska ne? Dariya summy itama tayi tace hmmm lallai ma zakiyya bakisanni ba.

Marinta ta Rama tare da cewa ince ke wayaiya gaki matar manya ko? Kiyita dressing kina bude tsiraici, toh kin budo ni kuma na gani kuma ya min,kuma sai na samu. Tsaki zakiyya taja ta dauko key din da summy ta ajiye ta bude kofar tana kokarin fita summy tace me zakice idan nace kina sa kafarki wajen dakinnan zaki rasa uwarki.
A zafafe zakiyya ta juyo tace ke banson hauka kina jina ko? Karki kuskura kisa uwata a shirmennan naki. Dariya summy ta fashe dashi da kaji amon sautinta babu imani a cikinsa. Tace uhmm su hajiya zakiyya manya!dariya ta kuma fashewa dashi sai lokacin zakiyya ta lura cewa summy ta girmeta sosai,sannan ko dacewa basuyi a matsayin kawaye ba. Zuwa yanzu daga skin tight sai bra ne a jikin summy Wanda zakiyya bata ma San yaushe ta cire kayan ba. Kallon jikinta yayi taga hijab dinta ne ya yamutse.
Chapter 53 · 0% Book details