← Book details Kuruciyar Minal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 80

Sashe 74

Kuruciyar Minal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace dalla dubata ni zakiyi wa barazana? Yanzu abar wannan magana zuwa anjima. Ya zakiyi da motata?
Fuskar kulya tasa adan shagwabe tace da alamu kai Dan masu kudi ne, abar maganan kaji? Yace kai ni warin talauci ma nakeji. Kasa kasa tace koma dai menene banza me mako kawai. Yace me kika ce? Tace karka damu zan biya kudin gyaran nawa ne? Yar bazawar dariya yayi yace kinsan nawa ne kudin motan nan kuwa?

Tace nawa ne? Murmushi yayi yace bar wannan zancen, tunda ke daliba ce zan miki ragi muyi 50 50 ki bada rabi in bada rabi. Tace nawa kenan yace ki kawo dala dubu Goma $10,000. Ido ta zaro tare da Jan numfashin da bata shirya ba tace mene? Yace bakiji ba? Cewa nayi $10,000. Tace la ga yan sanda nan sunzo ma. Juyawa yayi yana juyowa yaga wayam ta arce iska ya nausa tare da fesar da iskar. Yana shirin juyawa yaga wallet dinta. Dauka yayi yaga student ID card dinta a ciki yace hmm zamu hadu sannan ya shige mota.

???Zayya tana kwance a hostel tana bacci taji Karan motan yan sanda ta cikin speaker sukace zayyana mainasara you are under arrest kiyi saranda ko mu miki karfa karfa, kin dauka zaki rusa masa mota ki tsira ne?? Da sauri ta leka window aiko motocin yan sanda ne guda 10 gaba daya sun saita window dinta da bindiga. Shugaban yaci gaba da cewa bazaki iya arcewa ba kiyi saranda kawai ko muyi harbi sauri tayi ta rufe window ta hanyo hularta da akwatinta sai ruwan bullet kakeji aiko ba shiri ta kwanta luf.???

Vibration din da wayanta yayi yasa tayi firgigit ta tashi daga mafarkin da take tare da sauke ajiyan zuciya ta goge gumin da ya tsattsafo Mata tare da kara wayar a kunnanta tace hello ? Ta dayan bangaren yace NINE! Tsaki taja tace me kuma kakeso yace AI bamu gama da case dinmu ba. Cikin tsiwa tace wani case kuma Bayan an wuce wajen? Tsk ince nabar muku makarantar Dan haka ka dena takura mini kaji ko? Ta karashe tana mai daga murya. Kallon wayan yayi kamin yace lafiyarki kuwa? Ko kan da matsala ne? Tace kai Aminu Yusuf kanason ka mutu ne? Yace Aminu Yusuf? Waye shi? Nifa SAHIR YAZEED ABDULMAJEED? UMAR ne.

Tace mene? SAHIR YAZEED ABDULMAJEED UMAR? hmm waye kai? Yar murmushi yayi yace nine mamallakin Lexus dinnan da kika bata ko ince kika rusa.? Zaro ido tayi tare da zare sim din wayar ta fara kukan shagwaba.

Bayan Sati daya minal da feena sun fito shopping kawai sukaji ana sanarwa wai customers suyi hakuri su fita baban mutum zai shigo. Minal tace wallahi babu inda zani ko shugaban kasa ne zai shigo, yo menene za'a wani shiga hakkinka. Ince duk Abu zamu siya? Feena ne tace nide yaya minal kinga tafiya ta minal tace jeki.

Yazeed yana cikin shopping din inner wears dinsa Dan baiyarda a siyo masa saboda kar a cutar dashi. Yaji kamar karan takalmi coge ta dayan bangaren kewaya wa yayi yaga wata macece amma bayanta yake gani tana siye siyenta. Body guard dinsa ne yace malama ke kurmace da za'ayi sanarwa a fita ke ki zauna a ciki kin wani dibo hijab kamar..... yazeed ne ya daga masa hannu yace karka zagi hijabi domin yanada muhimman ci a addini amma mafiya yawa Mata basusan da hakan ba Dan haka ka daraja mai hijabi balle ma irin su Abuja ai sai an daure za'a saka shi.

Murmushi tayi jin zantukan yazeed hakan yasa ta juyo domin taga waye sannan raji dalilin da yasa sai mutane sun fita zaiyi siyaiya amma me tana ganin yazeed ne tace wow! Daidai kenan dama kere na yawo zabo na yawo wata rana zasu hadu. Wato shine Dan wulakanci ranan nan ka dauki hoto na mai makon kace min man baki na ya baci wato ga shashasha ko?

Jin hayaniya yasa manager yazo dubawa ganin minal ke fere yazeed yasa yace security ku fita da ita hannu yazeed ya daga musu. Itako sands tamai tastas ta hankade keken siyaiyar nata wa manager sannan ta kalli yazeed tace kaikuma karka bari mu hadu a karo na uku mtsww, Sannan ta fice tana cika tana batsewa.

Feena ne tace yaya me ya faru, kauda kai minal tayi tace ashe wannan Dan renin hankalin daya Dakar mini mota na ne. Feena tace kina nufin yazeed abdulmajeed ne ya daki motar ki? Waiyo dama nice. Tsaki minal tayi tace ya akayi kikasan cewa banzan yazeed dinku ne? Feena tace da farko dai wasu yan nata ne naji suna cewa shine. Ba biyu kuma ba banza bane me kudi ne kuma.... minal ne ta datseta ta hanyar cewa karma ki fara banasonji kar kunnena suyi ciwo.

Yazeed kuwa a hanyarsa na zuwa gida ya Kira secretary dinshi yace ya batun personal assistant dinnan kowani department sun bada sunan masu hazaka? Secretary din yace eh yazeed yace this time around ni zanyi musu jarabawan da kaina Dan na gaji da canje canjen P.A dukansu kasalallu ne basa son aiki ko kadan.

Washe gari minal tana zuwa office aka miko Mata letter dinta akan cewa vacancy ne na PA din president kuma tana cikin masu hazaka idan tanaso toh karfe 10 am taje floor na Goma sha biyar wato na karshe anan zataga sauran abokan aikinta masu neman mukamin.

Karfe 9:45 ta shiga lifter domin zuwa floor din, ba kowa yake zuwa haka kawai ba sai da dalili Dan haka bata taba hawa nan ba. Lambobin ta duba taga daga floor na 14 ya tsaya. Fitowa tayi ta tambayi yadda ake zuwa sama aka nuna Mata wasu lifts guda biyu bata lura da rubutun dake sama ba kawai ta shige daya gani tayi tsarinshi daban ne harda kujera tace ikon Allah mutane da securities ne suka fadin wait! Dakata amma ina ta Riga ta danna top floor Dan haka ya rufe. Hankalin kowa ya tashi yau karamar ma'aikaciya ta shiga lift din president! Securities har wani zawo zawo sukeji.

Tana Isowa floor din ta fito abinda ta fara haduwa dashi shine secretaryn yazeed da wata assistant dinshi sun minke hannu kowa yana jira yaga wacce ta kawo hayaniya cikin building din. Harara assistant sin ta aika Mata yayinda secretary yace malama juya ki karanta saman kofan da kika fito. Karantawa tayi taga an rubuta PRIVATE ELEVATOR wato na musamman ne. Murmushin jin kunya tayi kamin tace yi hakuri ina sauri ne ban tsaya na karanta ba. Dan murmushi yayi yace ba komai amma ki kiyaye tace insha Allah.

Layi tazo tahau ta tsaya taga kowa sai gyara kwalliya ake tace wadannan ko lafiya sukewa tsoho kwalliya? Sunayensu aka fara Kira ko wacce ta shiga sai ta fito tana kuka, Kazan kuwa jiki a sanyaye suke fita sunan minal aka Kira ta shiga tana fargaban wani tambaya akeyi da yakesa mutane kuka da mutuwar jiki.

Kamar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta shiga saide kujeransa ba ita yake fuskanta ba baya ya bata wato yana kallon gari ne tunda ofishin nasa bangare daya glass ne. Cikin kakkaurar murya kuma kamar ya gaji da yin maganan yace idan akwai jagwalgwalon da kuke Kira kwalliya a fuskarki toh ki fita ko jarabawar baza'a miki ba idan ko babu to kalli gefenki na dama. Babu musu ta aikata hakan kujerace akai akwai laptop da kuma files guda 10. Yace kalli agogo karfe nawa ne? Tace 11:50 yace mun rasa soft copy na wadannan files da kike gani Dan haka so nake kamin karfe 12:30 ki sake typing duka idan kuma bazaki iya ba toh KEMA GA HANYA!

HHHH TYPING IS NOT EASY! KARKU MANTA KUYI COMMENTING DA KUMA SHARING.

NAJI WASU SUNA CEWA SUN ZAMA CONFUSE PLS KU FADAMIN ABINDA YA RUDAR DAKU DOMIN AYI MUKU BAYANI.

ONE LOVE?

miss Untichlobanty ?

16th April, 2020.

+2347069510076

*??KURUCIYAR MINAL??*

?by miss untichlobanty?

*?CHAPTER 92*

RECAP

Yana fita yayi dariya yace yan Matana aci chewing gum lafiya yana Mata dariyar mugunta. Itama a bangaren ta yana ficewa tace sai kace ban sanka ba kawai zan yarda cewa ka hakura. Hmm nasan so kake kabi dare ka cinye dan haka gadi zanyi sannan tayi ma kofar gwaliyo.

CONTINUATION

A asibiti kuwa ayush tasha plasta a mazaunai sannan kar ta dinga zama saide kwanciya ko tsayuwa. Tafiyar ma gwale gwale takeyi Kamar yar kaciya. Wayarta ta dauko taga missed call aciki harda na Dan iskan mijinta wai ya dawo daga Mali. Tun shekaru biyar da suka wuce ya tattari tarukucensa ya tafi neman Mata ta da harkar gabansa da sunan kasuwan ci saida ya kwaso kanjamau tukunna ya lallabo ya dawo.

Bayan sun kammala wayar ne taga cewa wata number ta Mata missed call Kira tayi bugu biyu aka dauka tare da fadin barka da war haka hajiya ayush ashe de baki canja lamba ba.

Ayush ne tace wai wa ke magana? Dariya akayi ta dayan bangaren tace hehehe su ayush manya shekaru nawa ne har kin manta da SUMAYYA? Ayush tace wace sumaiya kuma? Tace summy de guda da kika sani yar lesbian yanzu kuwa magajiya ce.

Dafe goshi ayush tayi a ranta tace mutum na fama da wata matsalar sai wata ta kunno kai. Daidai lokacin mamata ta turo kofa ta shigo dakin da take hakan yasa ta dawo daga tunanin da ta shiga tace toh summy kike ko wa ya akayi? Summy tace ya akayi? Lokacin da na yi miki aiki ba cewa kikayi idan kin samu dani za'a raba ba? Jini shiru yasa na share na bar kasona tare da ke a matsayin ajiya yanzu ko fatara nake babu kasuwa sosai Dan haka so Nike ki bani. Ayush tace turo account number ki. Summy tace ance miki cikin sauki zan karba na wuce AI wallahi gidan da kike nan zan zauna kima San yadda zakiyi ki shigar dani ayush ta kunduma ashar tace bara in kashe wayar muga tsiya. Summy tace wallahi ko bakar magana kika kara yi min wallahi sai na zo na miki tone tone.
Chapter 74 · 0% Book details