← Book details Kuruciyar Minal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 80

Sashe 78

Kuruciyar Minal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka suka dinga kwasar mutane, me shayi ne, masu kasa irin kayan marmari a titi ne.... sanda akayi gudu iya gudu aka gaji aka tsaya hutawa dogo yace wai ni wa ya gansu ne samrin nan sukace wannan hajiyar ce.? Yace wai to ma a ina kika gansu ne? Dariya tayi tace zakusha mamakin inda na gansu. Cikin mafarki nagansu in fada muku. Ashar irin ta yan daba ya danna yace wannan matar ta ma raina mana hankali wallahi kai kuyi Mata na jaki.

Rufeta akayi da mugun duka matan inyamuran nan suka zage dantse suka kiranta kamar sun Sami sakwara. Akayi Mata ruf dubu aka jijjibge ta. A TAKUCE de daga nan itama tasan inda dare yayi Mata domin haukace wa tayi dalilin da yasa haukace kuwa shine saboda lokacin da za'a tsafin anyishi ne cewa in dai ayush tana raye mom din yazeed bazata taba yin hankali ba toh yau da safe ayush tayi gaba sanadiyyar cinye gaban ta da aljanin yayi domin satin ta daya a gidan wasu halittu masu Lama da kuda suka fara fitowa daga kasar ta suna cinye Mata fata. Atakaice de tayi mutuwar wulakanci iya wulakanci ga bata sallah ga shirka ga zalinci ai kowa ma yasan makomar ta.

A gida kuwa safina fadi take nikam yanzu komai nawa ne nayi baje baje kawai abinda yamin saura shine na fitar da wannan kucakar matar tasa.? Waka take tana rangaji daure da towel zata shiga wanka saboda ance za'ayi baki kar su kawo Mata raini.

Bude bandaki tayi tana rangaji da juyi. Jijjiga tayi zatayi juyi, juyin ta ke da wuya santsi ya kwasheta ya hada da gini sannan ta fadi ta baya ta doke da toilet sit a take a wajen jini ya cika kwakwalwar ta sai barzahu.? Allah yaji kan mu'umini ameen!

Motar su zaliha ne ta faka a cikin gidan su minal.? Da sauri yaransu me suna kabir ya fito yana fadin wow daddy! Gidan uncle dinnan ya hadu. Kace ya ma sunanshi? Luku yace sunan shi uncle yazeed. Ciki ya shiga da gudu yana fadin kowa ya fito , king kabir yazo. Nine sarki kabir Dan lukman dariya minal tayi tana saukowa tace maraba sannu da zuwa Dana sarki kabir.

Alamun tunani yayi kamin yayi sauri ya riko hannun minal yace kece wannan kyakkyawa matar uncle handsome ko? Murmushi tayi masa sannan tace kaima AI kyakkyawan saurayi ne kabir Dina. Yace toh ya akayi kika sanni? Tace mommyn ka ne ta tura min hotonka.

Dadai lokacin su zaliha suka shigo rurrungume juna akayi aka Dan zubda kwalla abin ka da Mata. A one sitter? zata zauna shima luku na yayi kokarin zama. Tureshi tayi shima ya ture ta. Ture ture suka soma kabir ya girgiza . Dan in da sabo ya Saba ya samu guri tare da fara latsa tablet dinsa yana shan alewa. Sahla ne ta sauko da tayi bulbul da ita tana dauke da juna biyu karami shekaran jiya suka San hakan fadi Dan samri Kaine kanin namu? Dago kanshi kabir yayi yace wow! Kaga mata kyakkyawa fara sol idan na girma yar ki zan aura.

Zaliha ne ta zauna a kujerar luku ya ciccibeta ya dagata shi ya zauna. Dariya tayi tace daidai kenan ta dake cinyarsa. Wani tunani ne yazo masa Dan haka ta kasa kasa ya fara tattaba Mata jiki ganin zai nemi ya tsinkata gaban yara yasa ta tashi kuma duka abinda sukeyi akan idon minal.

Sahla kam tuni game ya 'bage tsakanin ta da mutumin ta kuma sirikin ta acewar sa fa kenan. Hira su minal suka kafa yayinda luku yace ina mutumina ne? Minal tace na barshi a daki yana shiryawa yaci ace ya sauko ma yanzu.

Daidai lokacin yazeed ya fara saukowa yana fadin my man ! Tare da fadada murmushin sa. Rungume juna sukayi kabir kam ajiye game yayi yazo ya kewaye yazeed sau uku sannan ya kalli baban sa yace daddy zan iya zama gidan uncle dinnan Dan inyi kyau? Luku yace kai de da masifar kyau dinka. Indai Abu na da kyau toh kai shikenan kabi ka damu mutane kenan akai.

A mota kuwa tunda zayya ta shiga take ma wa sahir magana amma ko inda take bai kalla ba Dan yasha alwashin koya Mata hankali.
Tace wai me nayi maka ne kawai murmushi yayi Mata yace .......

......

A gidan sabir da bushra ba laifi ana Dan zaman lafiya,yana Dan aikinsa saide me ya lura tunda sukayi auren bushra tayi sanyi dayawa bawai tuban bane kadai akwai matsala hakan yasa yauwa kamar kullum ya tisata a gaba yake tambayar ta matsalar ta. Da Kumar ya samu ta budi Baki zatayi magana ta "ance ana bukatar bone marrow transplant cikin gaggawa da a lissafi na yanzu kwana 20 yayi min saura."

TO WAI SHIN ME SAHIR ZAICE MA ZAYYA ?

KUNASON KABIR KUWA?

YAYA ZA'A KAYA DA JINYAR BUSHRA ? ZATA MUTU KO ZATA RAYU ?

Takuce KARAMARSU BABBARSU,? Jared Ku manta da VOTE, follow And? comment .

Miss untichlobanty ?

https://my.w.tt/WGgiLRPs36

?? *KURUCIYAR MINAL*??

? _By miss Untichlobanty_ ?

? *CHAPTER 96*?

RECAP

A gidan sabir da bushra ba laifi ana Dan zaman lafiya,yana Dan aikinsa saide me ya lura tunda sukayi auren bushra tayi sanyi dayawa bawai tuban bane kadai akwai matsala hakan yasa yauwa kamar kullum ya tisata a gaba yake tambayar ta matsalar ta. Da Kumar ya samu ta budi Baki zatayi magana ta "ance ana bukatar bone marrow transplant cikin gaggawa da a lissafi na yanzu kwana 20 yayi min saura."

CONTINUATION

Salati sabir yayi yace bushra shine kika boye mini baki sanar dani ba ko wani daga gida tace nima a kurarren lokaci na sani shiyasa ma na nemi tuban kowa Dan na fahimci rayuwa ba'a Mata garage sai ta aiko ma Abu alokacin da baka tsammace sa ba.

Riko hannunta yayi tare da zura Mata hijabi sai family house Dina Alhaji mansur domin a fara gwadasu ko za'a samu Wanda yahau daidai a dangi kamin a fita waje wato MRD (matched related donor)

Babu bata lokaci suka nufi asibiti yayinda mom tayi kokarin kiran yazeed amma is not rechargeable Dan haka tabar masa message.

A gidan kuwa su zaiya ne suka iso nan akayi introducing Mata su waye su zaliha. Kabir yaron su luku ne yace la kamar su daya kuma sai ya saka kuka tare da rungume sahla. Cikin damuwa tace menene? Yayinda hankalin kowa yayo kanshi.

Jan hanci yayi yana goge kwalla cikin kuka da shessheka yace meyasa ba'a cemin na shirya ba? Luku yace big boy ka shirya me? Yace ganin kyau mana ashe hassanan rafi kyau kuka barni nayi garajen zabar Mata. Kama haba yazeed yayi Dan ya rasa abin cewa yadda yake zato zance yayinda minal tace iko sai rabbu zayya kuwa waks ta yanko inda ake cewa "ni bazance komai ba Dan zafi ban shafa ko mai ba"

Shiko kabir cewa yayi AI da nasan akwai Wanda yafi aunty sahla kyau da nace yarta nakeso. Riko hannun zayya yayi Mata fuskar abin tausayi yana Mata wani munafukin Dariya yace aunty zayya ta zaki bani yarki? Sai inyi Mata biyu da yarki Dana aunty sahla Dan bakyau daukar alkwari sannan ba'a cika ba da sai ince na fasa nata. Minal ne ta daki zaliha na wasa tunda a gaban yara suke tace zally ke yanzu duk iyayin naki sanda kika juyewa danki kai kuma kana gani ka barta uncle luku? Kabir ne ya kyalkyale da dariya yace daddy dama sunanka luku? Yace daga yau daddy luku zauna ce maka. Zuwa yayi ya shafa cikin sahla dukda ba'a ganin komai yace uwar gida ta ina miko gaisuwa.

Zayya ne ta kama kwankwaso tace "ummi..." wato minal "ni fa ban gane ba wai wannan yaron me yake nufi ne yake ta zancen wani uwar gidansa?" Tsayawa yayi a gabanta ya gyara Riga tare da ninke hannu yace ni nan da kike ganina babban saurayi, ko cikin turawan nan mr. handsome ake cemin Dan haka.......

Wucewa zayya tayi Dan bata da lokacin sa ta zauna a gefen minal tare da cewa ummi ke nake saurare... zana zahir ma yayi yayinda sahla tayi sauri sauri ta zauna a gefen zayya tace sister albishirinki ai kin kusa zama aunty..... zayya tace tun Bance goro ba? Sannan ta washe baki tace kice Allah? Minal tace wai ku bakuda kunya ne? Zayya bata ma bi ta Jan zancen minal ba ta rage murya kasa kasa tace sis bani sirrin... sahla tace yafi karfinki saide kije kice wa mijinki ya fada miki. Zayya tace an gama Dan itafa tunaninta wani abin za'a sha shiyasa ko ajikinta a inda take zaune ta kalli sahir tace bro wai kasan sirrin ? Toshe Mata baki sahla tayi tare da wucewa daki da ita Dan taga alamun kan da matsala.

Hira sukasha sosai kamin yazeed yace ina wayata mu dauki hoton tarihi. Kabir dake game ya kalla yace big boy je ka Kira mana aunties dinka. Sannan yace wa minal ta dauko wayarsa a daki tace aiko kaga mun manta bamu Kira safina ba. Bata rai yazeed yayi Dan shi already ya sake ta tun sanda ya dawo hankalinsa Dan haka yave kirata dama akwai abinda zan fada Mata sai muyi hotan karshe.

Dauko wayan minal tayi ta kawo masa sannan ta tafi kiran safina aiko tana bude bandaki ta kwalawa yazeed Kira haurowa sama sukayi suna tambayan lafiya hannunta na rawa ta nuna musu bandaki salati suka saka. A bayansu sukaji ance kin kasheta KIN KASHE KIN YAR UWA TA.

A asibiti kuwa an gwada su duka family din wato donors su maman ta da nafisa da auntyn su ana tsammanin result sukaga su yazeed sun shigo da gawar safina wajen su sukaje suna tambayar lafiya wata fiririyar fitsararriya ne tace me kuwa ya faru an kashe mini yar uwa toh wallahi za'ayita. Ran yazeed ne ya baci yadda ta hakikance cewa minal ne ta kashe safina. Mari ya falla Mata yace ke bakida hankali ne kinsan cewa wannan magana ba karama bace? Zance ne ya miki dadi har kike Barbada cewa ita tayi kisa bayan kinsan hukuncin kisa ne ga Wanda ya kashe?
Chapter 78 · 0% Book details