← Book details Kuruciyar Minal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 80

Sashe 10

Kuruciyar Minal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yazeed yace afuwan nawan wallahi wani abune ya taso

Jamal yace sunfini kenan

Yazeed yace bazaka gane bane

Jamal:

mom masa'ul khair
(good afternoon)
ina wuni?

Mom:
masa'ul noor khaifa anta ya ibny Jamal
(good afternoon how are you my Darling son jamal)
Lpy klau Ykk Dana Jamal?

Jamal:
ana bi khair wallah
(am absolutely fine)
Lpy na klau
Ain zakiyya ?
(where is zakiyya?)
Ina zakiyya?

Mom:
zahabat ilaaa boutikiha
(she went to her boutique)
Ta tafi boutique dinta

Jamal:
mata sa tarji'i?
(when is she coming back?)
Yaushe zata dawo?

Yazeed:
anta uskut tatakallam kaseer wallah walakin arafta annany annany karihtul dajij
(hey pls keep quiet,you talk too much while you know I hate noice)
Kai Dan Allah kayi shiru ka fiya magana bayan kasan na tsani hakan

Jamal:isbir ya sadiky la atakarir Insha Allah
(sorry dude I will never repeat it okay?)
Yi hakuri mutumina bazan sake ba

Yazeed :
khairullak
(better)
yafi maka

Point out shine abinda yazeed ya fada sai ga atine da salma sunzo suka tsuguna a gabanshi

yace do the right thing sumul sumul suka tashi suka koma kitchen gasu sundawo su biyar tare da kayan abinci iri iri Suna bin hanyar dinning room

sanda suka gama jerawa tukunna yazeed yace

Dan uwa muje kaci abinci ko?

Mom tace Toni bara in Shiga ciki Dan na gaji

Sukace to mom a huta gajiya

tace shukran
(thanks)
na gode

Dinning room din suka Shiga Jamal ya kalli abincin
yace Dude ya haka ina kasar waje inci wannan yanxu nazo Nigeria ina expecting tuwo sai naga abinda na baro.
Ya fadi hakan ne a accent dinshi na balabe sai hausar tayi wani zakwai da ita amma fah bai kai na yazeed ba.

Yazeed shima cikin accent nashi na larabawa-larabawa turawa-turawa kuma cikin sanyin murya

yace yanzu muka gama maganan da mom soon har sai wannan kazantar taku ta isheka.

Kallonshi Jamal yayi irin kaji dashi kamin yace

Ka kiyaye watarana abinda kake Cewa kazanta zakazo kanaci harda santi

Yazeed ya tabe fiska Kamar yaga danmalelen da yara suka jagwalgwal yace Allah ya kiyaye

Jamal yace munanan dakai zama sukayi suka ci abincin Suna hiran yaushe rabo

Bayan sun gama ci suka tafi side din yazeed domin yin alwala su tafi masallati

Amina da taci kuka har tayi baccin wahala ta tashi sanadiyyar fitsarin daya matseta

da gudu tayi hanyar wata kofa data gani wadda take sa ran toilet ce

aiko tana afkawa taja waya super sanadin kamin ta bude kofar ya Dan bata wahala Duba da batasan irin kofar Ba

hakan ya taimaka wajen fara saukar fitsari wadda ya hadu da tiles yayi sanadin zamewar tata

Ihun data rafka kamin ta suma shi yasa yazeed da Jamal yin hanyar dakin aguje domin shi yazeed shaf ya manta da ita a side dinshi Suna Shiga dakin sukaga jini jini akasa

Sai a lokacin yazeed ya tuna da Amina na dakin

Tsayawa yayi abakin kofa yayinda Jamal ya jiga bandakin Dan ganin meke wakana

Ganin Jamal ya fito jikinshi a sanyaye yana kallon yazeed hakan yasa yazeed ya dauka ko minal ta kashe kanta
a hankali minal ta fito jikinta duk jini tana dingishi sanadiyyar zamewan da tayi wani ajiyar zuciya yazeed ya sauke ganin tanada rai

Ko kallon Inda yake Jamal baiyi ba ya fita fiskannan a daure Kamar hadari

Sai kuma ya jiyo yace me nake gani?
Cukumosa yayi tare da masa tsawa yace yazeed kayimin bayani Idan Ba haka Ba mum ta sami labari

Yazeed ya kalleshi yace mai karka fasa fada yana Dan murmushin gefen baki don't atunaninsa wasa Jamal yakeyi

Juyawa Jamal yayi ya fita

Direct side din mom ya wuce a lokacin har ta fara bacci Kamar a mafarki takejin yadda ake buga mata kofa hakan yasa ta bude ido

Adan tsorace ta bude kofar ganin jamal fiskannan tayi jaa tace son lapiya?

Kamo hannunta yayi sai part din yazeed hankalinta a tashe Dan tadau wani abunne ya samu danta daya daya

A Abangaren su yazeed kuwa harara ya banka mata kamin yaje ya kwanta akan gadon yace tayi knee down
Tayi tsamo tsamo da ita a cikin fitsari duk ta zama abin tausayi kwalliyan duk ta cabe

Kinyin tayi illa ma turo baki da tayi alamun gardama saukowa yayi daga gadon ya daga hannunsa zai dalle bakin

Puuuuuumm aka bugo kofar dakin duk suka kalli wajen

Abangaren su inna kuwa hankalin kowa ya tashi aunty fauziyya sai kuka take acewarta laifin tane tunda a hanyarta na dawowa daga gidan tane ta bata

Baba kam ya ma kasa yin Komai Dan jinya ce ta kamasa rif daya Ba abinda yake furtawa sai Innalillahi wa inna ilaihi raji'un

Kowa hankalinsa ya tashi abin dai Ba dadi gashi ya Abubakar saura 3days ya dawo

*Anan ne ink din bairo na ya kare bara insiyo wani domin rahoto muku labarin kuruciyar minal*

*Ku Muna Mani soyayya ta hanyar commenting*

*Sannan Ku nunawa kuruciyar minal soyaiya ta hanyar sharing.*

*Love u wujiga wujiga*

10th July 2019

Karamarsu babbarsu ce fa

Mzz untichlobanty💕
[1/11, 1:52 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹🍀by @mzz_untichlobanty🌹

*CHAPTER 16*

Kallon wajen dukkansu biyu sukayi

Minal hawaye da majina duk sun chabe mata fiska

Jan majinan tayi kamin ta mitsitsika hanci sannan ta goge a hijabin daya hada launi daban daban kama daya kalarsa da kalar jini,da jurwayen fitsari tare da kanzon majina😂
Takowa tayi cikin dingisawa ta tsuguna tace ina kwana au ina yini hajiya

Dan Allah kicewa oga sir ya mayar dani gida wallahi yunwa nakeji gashi Nasan hankalin iyayena ya tashi.

Dagota mom tayi ta Shiga dakin tana takawa idon ta cikin na yazeed Wanda ya kasa fassara yanayin mahaifiyar tas

Bai ankare Ba yaji saukan mari
Wani tashin hankali ne ya saukar masa tunda ya mallaki hankalin kansa bai taba ganin bacin ran mahaifiyarsa akansa Ba balle ta dakesa.

Hakan yasa lokaci daya zazzabi ya rufe oga sir Dan baima lura da Cewa yana ha'bo ba

Zama yayi kan gadon jagab Ba tare da yace Komai Ba kuma bai motsa Ba kwakwalwarsa ce ta daina aiki

Baki mom ta bude ta fara magana dukda ko zuciyarta ta girgiza ganin ta fidda jini Daga jikin Dan nata amma abinda yayi ya wuce wannan.

Haba yazeed ban taba tunanin irin haka daga gareka Ba dukda Nasan irin zaman da kakeyi da matarka ban taba tunanin ko da wasa zaka Ra'bi zina Ba
Bama a zina ka tsaya Ba zinar ma fyade kayi?

Amina jin bata gano Inda mom ta dosa Ba kuma da alama mom ta saba layi Dan da alamu bata fahimceta Ba sai tayi saurin Cewa Hajiya dama oga sir da ya fita fyade yayiwa wata?

Juyowa mom tayi fiskanta da alamar tambaya domin kanta itama ya daure shima dai Jamal hakan ta kasance masa.

Domin duk Wanda yaga minal a yanayin da take kuma acikin side din yazeed to lalle Abu na farko da zaiyi tunani shine fyade yazeed yayi mata
Duba da yadda shi Jamal din ya samota a bandaki a sume sannan tana tashi abinda ta fara yi shine kuka to lallai abinda zaizo kanka kenan.

Mom tace yata dama Ba fyade yayi miki bah ?
Minal ta gyada kai kamar kadangaruwa atake nadama ya saukarwa mom kawai sai ta kama hannun minal tayi side din ta da ita domin jin Karin bayani.

Abangaren Jamal kuwa dakin yazeed yaje ya dauko cotton sannan ya dawo zauna a gefen yazeed,cotton din yasa ya goge masa jinin sannan ya tura wani a hancin ya ruko hannun yazeed din.

Rumgumesa yazeed yayi ya fashe da kuka mai sauti Kamar maraya gaba da baya me karancin shekaru.

Jamal bai hanasa kukan Ba illa ma bubbuga bayansa da yake yi alamun lallashi

Saida yayi mai isarsa sannan ya tashi zai fita Jamal yayi saurin rikosa tare da mikewa tsaye Suna fiskantan juna yace lallai mudin abokai ne amma abokantakan ya ya karfafa Yan uwantakan mu lallai nidin na kasance mai kuskure d............

Hannu yazeed yasa ya rufe masa baki tare da girgiza kai yace lallai nine me laifi da ban sanar dakai Ba kuma ai sanda kace zaka kawo mom saina mata bayani,na dauka wasa ne Kamar yanda ka saba Dan nima baizo kauna Cewa zakuyi min mummunar fahimta Ba saboda yanayin yarinyar. Lallai kaidin amini ne na Gaskiya saboda alkhairi kake sona dashi Dan haka karka bani hakuri.

Rungume juna suka kara yi kowannensu na hawayen farin ciki kamin kuma suka fashe da dariya suka tafi domin yin sallh Dan lokaci ya tafi.

Abangaren su mom kuwa wani daki ta kawo minal sannan taje dakin zakiyya wardrobe din ta ta bude Dan tasan pin din taga duk babu laces da atamfofin

Wani kofa acikin dakin  ta bude dakine girman sa Kamar store babu Komai aciki sai akwatina 5 wasu takalma masu kyau amma zakiyya tasa a store Wai sun tsufa alhalin Kamar saga kwalinsu aka cirosu ko kurar arziki basuyi ba

Akwatinan mom ta bude ta dauko wani lace mai kyau da takalmi da kuma hijabi sannan ta rurrufe wurin ta kawo dakin da tabar minal

Ajiye kayan tayi sannan ta kalli minal wacce ta zauna a kasa tace Yan mata tashi ki zauna akan kujera mana ayayin da take nuna mata sofan dake dakin

Girgiza kai tayi tace Ba Komai nan ma yayi
Mom ta kamo hannunta ta zaunar da ita sannan tace
ya sunanki?
Tace Amina
Mom tace ya akayi kikazo gidannan kuma me hadinki da Dana

Kallon mom minal tayi kamin ta fara kwararo mata bayani cikin nutsuwa,kamunkai da tarbiyya Kamar da gaske tun daga fitowarta daga gidan aunty fauziyya har izuwa yanxu

Not telling her that this is not the first time she met yazeed

Shiru mom tayi tana nazarta maganan

Da ta tambayi yazeed kamin ta mareshi amma ai kowaye yaga yanayin aminan abinda zai ce kenan kuma ko Ba Komai soyayya ta jawo hakan ai Dan masoyinka ke hukuntaka akan laifinka

Makiyinka ne zai ganka kana Abu Ba daidai Ba ya barka ko ya kara ma kwarin gwuiwa
Chapter 10 · 0% Book details