← Book details Kishiyar Uwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 26

Sashe 6

Kishiyar Uwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan wasu 'yan watanni da rasuwar malam lokacin cikin maimunatu ya tsufa sosai gashi ba kwanciyar hankali , wannan ya sanya ta rame ta lalace , tayi bak'i , abin tausayi ga ba kulawa daga wajen miji sun rigada sun maidashi rak'umi da akala bayajin maganar kowa sai ta Asabe, Allah ya taimaki maimunatu kannensa na zuwa ta tayasu hira dan haka sai damuwarta ta ragu sosai, ana wannan yanayin ciwon nakuda na kamata ga malam baya nan , ciwo takeyi sosai tun dare har safiya amma Asabe na jinta bata koda lek'a ba , ita a burinta ma kawai maimunatun ta mutu kowa ma ya ana cikin haka Allah ya jefo da hadiza k'anwar malam din aikuwa tana ganinta cikin wannan halin ta juya ta sanarda mahaifanta aikuwa basu dade da zuwa ba Allah ya sauketa lafiya ta samu d'iyarta mace masha Allahu yarinya son kowa kyakykyawar sosai, kowa in ya ganta sai ya kara kallonta saboda tsabar kyau, a lokacin da Asabe taji anyi haihuwar an samu mace murna tayi sosai da sosai a ganinta ita zata haifo namijin , haka akayi suna malam bai dawo ba k'anin malam din shi ya sanyawa jaririya sunan mahaifiyar maimunatu yarinya taci suna Fatima, komai y'an uwan malam sukayi saboda yana chan harkar fataucinsa, ko da ya dawo bai wani nuna murna sosai ba duk kuwa da abinda yake nema shiya samu , haka dai rayuwa tayi ta yin juyi da rayuwar Maimunatu da yarinyarta Fatima cikin rashin kulawa da k'unci , bayan watanni hud'u Asabe ma ta haifi d'iyarta mace bataso hakn ba amma kuma ba yadda ta iya lokacin malam yana nan dan haka zo kaga murna da farin ciki ba kama hannun yaro , ranar suka aka sanyawa yarinya zainabu , anyi shagali sosai , a haka rayuwa tayi ta tafiya har Fatima tayi shekara d'aya ko tsakar gida basa iya fitowa, a sannan ne Asabe it a da k'awarta sukayi mata asiri akan in ta tafi karta dawo gidan a lokacin ne aka aika mata da zancen mahaifinta bashida lafiya , da kyar aka barta ta tafi da sharad'in bazata tafi da Fatima ba haka ta barwa mahaifiya malam iliya ta tafi, cike da kewar yarinyarta, Allahu Akbar a hanyarsu ta tafiya Allah ya aiko da wani gagarumin hatsarin motar da maimunatu take ciki tayi hatsari mutane da yawa sun rasu Allahu Akbar Allah ka jik'an musulmi amin, a lokacin da labarin hatsarinsu ya Shiva cikin k'auyen ba k'aramin tadawa mutane hankali yayi ba da kuma aka sanar musu da cewa ba Wanda yayi rai a cikin matafiyan lallai mutanen k'auyen sunji rasuwar tata musamman ma y'an uwan malam dashi malam din , amma Asabe a lokacin ne ma duniyarta ta koma sabuwa ba ta da wata damuwa a haka har aka karaci alhinin rasuwar akabar masu rashi da rashinsu.

Bayan kamar data biyar a lokacin Fatima tayi wayo sosai dan haka Asabe ta takura da sai an kawo mata ita ai itama mahaifiyarta ce da kyar iyayen malam suka bada ita, to fa tun lokaci ta fara zan wahala har kawo yanzu ba wanka ga aikin da yafi karfinta shi ake bata tunda ta tashi bata san mecece kulawa ba duk kuwa da 'yan uwan malam na k'ok'ari amma wani lokacin basu ma San anayi ba , babu irin rayuwar da Fatima bata gani ba a gurin KISHIYAR MAHAIFIYARTA data baya da abin ya fara sakinsa sai ya bar harkar fatauci ya koma gona don ya dinga kulawa da yarinyarsa haka kuma suka rufe masa baki ta yadda bazai tab'a fad'awa Fatima labarin mahaifiyarta ba. Wannan kenan

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
(ASALIN LABARI)
Kwata kwata malam bayajin dadin rayuwar da d'iyarsa ke ciki , gashi yanzu yana halin rashin lafiya mai tsanani ga tsufa ya kamashi, gashi a yanzu ne yarinyarsa take buk'atar kulawa a gareshi .

Ranar wata Asabar da safe baraka ta je wajen Asabe , da zancen auren Fatima da Ado tunda ya matsa mata , da sauri Asabe ta amince ga bisa la'akari da tayi na ganin y'an birni in dai sun shigo garin suka d'ora idanunsu akanta su ce suna San ta , iya kuma ba kowa tayiwa burin auren irin wadannan ba sai Abu , ta sanar da ita babu damuwa , amma sai da su ka sanya aka kulle musu bakin malam din , aikuwa tana fada masa ya amince duk da zuciyarsa bataso amma haka ya yadda, lokacin da ya sanarda Fatima bata mu da masa ba duk kuwa da babu Wanda ta tsana a duniyar nan sama dashi,sosai ake tayin shirye shiryen biki , a wannan lokacin ciwon malam yayi tsanani.

Ranar wata Asabar bayan Fatima ta dawo daga tallah, sallama tayi a d'akin mahaifinta ya amsa mata muryarsa na karkarwa saboda ita kadai ke kulawa dashi , "Fatima ki yafemin na miki laifi na hadaki da wanda bakya so nasan ban kyauta ba amma ina ganin gwara haka fiyeda ki zauna cikin bak'in ciki , sai maganarsa ta katse numfashinsa yana kai kawo chan kuma sai taji shiru , aikuwa da gudu ta fita tana k'walawa inna Asabe kira ," Inna! Inna! Inna kizo wallahi baba ya rasu mun Shiva uku" da gudu Asabe ta fito ta nufi d'akin malam din abirkice dan ganewa idonta meya faru........

Godiya ta musamman gareku masoyana ina fatan kuna cikin k'oshin lafiya kuma zakuji dad'in karatu , ayi karatu lafiya.

Luv u all my dear fan's😍😍

Please🙏🏻
Share
&Comments

To be continue...........

🌿🌿🌿Nussad🌿🌿🌿

🌸🌹Kishiyar Uwa🌹🌸(True Life Story)
🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸

GODIYA GA ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA DAYA BANI DAMAR CI GABA DA RUBUTUN LITTAFINA , MAI SUNA KISHIYAR UWA .

GODIYA TA MUSAMMAN GA Y'AN MOONLIGHT WRITERS ASSOCIATION, ALLAH YA K'ARA HAD'A KAWUNANMU AMIN

GODIYA TA MUSAMMAN GA Y'AN UWA NA DA ABOKAN ARZIKI.

GODIYA TA MUSAMMAN GA FANS DINA , DAMA FANS DIN LITTAFIN KISHIYAR UWA, INA GODIYA SOSAI, INA FATAN ALLAH YA BANI DAMAR KARASA ISAR DA SAK'ON DA NAKESO NA ISAR , KUMA BANA FATAN NA BAKU KUNYA .

MASU TURO DA COMMENTS INAJIN DADIN HAKA.

INSHA ALLAHU YANZU MUKA NUFA CIKIN LITTAFIN GADAN GADAN , INA FATAN ZAKU BIYONI DOMIN JIN MAI YAKE SHIRIN FARUWA.

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
SHAFI NA7️⃣-8️⃣

Koda inna Asabe ta k'arasa cikin d'akin , ganin halin da malam yake ciki ya sanya ta zunduma ihu tana kururuwa , Abu ce ta fito daga d'akinta cikin yatsina fuska tana duban Asabe cikin gadara " wai ke inna ki damu mutane da sanyin safiyar nan baki ganin mutane suna yin bacci", galala Asabe ta tsaya tana kallon Abu cikin ido kana ta dubeta " yo ke dan k'aniyarki kina ganin mahaifinki cikin wani hali amma kuma kika tsaya kina yiwa mutane zancen banza" "ni dai gaskiya ana takuramin wallahi " ta fad'a ta komawa cikin d'aki ta banko k'ofar d'akin, maganar Fatima ce ta dawo da ita cikin hayyacinta " inna bari na duba in baba muhammadu yana nan "( kanin malam iliya ) , bata jira me zatace ba ta fallah da gudu ta bar Asabe na sallallami had'e da tafa hannaye.

Ba'afi mintuna biyar ba sai gasu sun shigo cikin azama , kanin nasa ya shiga cikin d'akin da sauri dan ganin me yake faruwa, da Sauri ya dawo ya dubi Asabe "maza shiryashi asibiti zamu kaishi har yanzu da sauran ransa " wata ajiyar zuciya Fatima ta saki kana ita kuma Asabe ta shiga domin shirya shi .

Baba muhammadu ne ya shigo shi da samari biyu suka taimaka masa suka Sanya malam a cikin mota , domin tafiya da shi asibitin , Fatima ta k'ekasa k'asa akan tanason zuwa amma Asabe ta hana ta haka tanaji tana gani aka tafi da malam asibitin.

Ko da suka k'arasa basu samu wata matsala ba aka shigar da shi d'akin da za'a dubashi , an dubashi anan aka gane yawan tunanin da yakeyi da kuma wani abu da ya ajieshi a ransa ya haifar masa da ciwon zuciya mai tsanani, sosai wannan maganar ta razana k'anin nasa, haka ma Asabe ta girgiza da wannan maganar , ita bama wannan ba me malam din ya ajiye a cikin zuciyar tasa shi take tunani fiye da rashin lafiyar tashi , haka suka gama komai da ake buk'ata kana suka zauna tare da shi.

Achan gida kuwa Fatima kasa tsinana komai tayi sai tunanin mahaifinta takeyi, bataso ta rasa shi a halin yanzu da take matuk'ar buk'atarsa a rayuwarta , ya Allah ka dubeta ka Sanya mata tawakkali a halin rashin lafiyar mahaifinta amin.

Har k' arfe uku na rana basu dawo ba, lokacin har ta gama abinci da komai da komai na gidan sai dai tallah ne yau kam bazata iya zuwa ba , gashi ta Sanya abinci a cikin kwano tana jiran ko za'a daukawa mahaifinta akai masa , haka tayita zaman jiran amma shiru.

Abu ce ta fito daga d'akinta da kaya a hannunta , watso mata tayi a fuska , " gashi nan ki wankemin saboda kayana sun taru babu masu wanki a cikin" dubanta Fatima tayi tare da cewa " amma ai kinga Baba bashi da lafiya ko ta yaya zan iyayin wanki a halin da nake ciki , " au bazakiyi ba kenan, to wai ma da kike cewa Baban bashida lafiya ina ruwana da rashin lafiyar tasa , kinga in zakiyi min wanki kiyi in kuma kika k'iyi kema kinsan sauran banza kawai, ta juya ta shige cikin d'akin na ta , tabar Fatima baki bud'e , babu yanda ya iya haka ta d'ebi kayan ta wuce ta wankesu, ba ita ta gama ba sai da akayi sallar magariba , kana ta gama wankin tsaf saboda akwai su da yawa.
Chapter 6 · 0% Book details