← Book details Kishiyar Uwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 26

Sashe 11

Kishiyar Uwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Lokacin da Ahmad ya isa k'ofar falon , thumb print ya danna , aikuwa a take k'ofar ta bud'e , shiga yayi da sallama , masha Allahu wani tangamemen falo ya bayyana , ga sanyi Ac da ya gauraye wajen , a d'aya daga cikin kujerun d'akin , wayar shi ya d'aga ya k'ira daga chan aka d'aga "haba habibty gani fa na dawo ina falon k'asa , kuma wallahi na gaji ," daga chan b'angaren aka yi magana , ban san me a kace ba na ga ya b'ata fuska , ya kashe wayar , kai shi ya zai yi wajen ba dad'i cikin gida ma haka , "Allah ka duba lamari na, ya fad'a yana duba k'afar bene , wata mata ce take saukowa daga ganinta kasan hutu ya ratsa ta akalla ba za ta wuce Ashirin da bakwai ba a duniya , sosai tayi kyau ba k'arya , ba ta da tsayi sosai amma fara ce , anyi mata kitson attach ya zubo har kafad'a , daga ganinta kasan idanunta sun bud'e da duniya, ' LAILA ' kenan uwargida wajen Ahmad , " haba Laila kina sa ne da cewar jiya mu ka yi zan dawo ai kya kirani ki ji me ya tsayar da ni amma kika yi ignoring nawa, kamar ba mijinki ba haba Laila, ya fad'a yana dubanta ", tab'e bakinta tayi " haba my luv ka san dai nima banda time ko saboda ka ga nima na fita aiki , " kallonta kawai yayi ya girgiza kai ya rasa meyasa kwata kwata LAILA bata damu dashi ba yana matsayin mijinta , ganin ba za ta tambayeshi meya faru ba ya sanya ya fara fad'a mata abin da ya faru da shi , "uhmmm Allah ya kiyaye" kawai ta ce sannan ta juya ta fita a d'akin , girgiza kanshi yayi sannan ya tashi ya shiga band'aki , wanka yayi sannan ya shirya yana fitowa falo wayar shi tayi k'ara dubawa yayi ya ga Dr Sadeeq ne ya kira dan haka ya d'aga cikin hanzari , sallama yayi , aka amsa tachan d'aya b'angaren ," ok to gani nan zuwa , kawai ya fad'a ya nufi saman d'akin LAILA , ya na bud'a d'akin ya hango ta akan bed tana charting, sallama yayi mata bata amsa ba , kawai ta d'aga mishi kai , juya wa yayi ya fita had'e da girgiza kansa , harabar gidan ya nufa sanye da yadi d'an Abba kalar sky blue da hula zanna bak'a , da sauri direba ya taso, girgiza masa kansa yayi alamar ba tare zaku fita ba hakan ya sanya ya koma kan bencin baba mai gadi , shi kuma ya nufi motarsa , shiga yayi , ya kunna , baba me gadi ya wangale masa bakin gate ya cinna hancinta wajen gidan ya nufi titi .

ASIBITI

Da sauri ya k'arasa asibitin , a bakin office ya had'u da Dr Sadeeq yana k'ok'arin fita domin komawa d'akin da Fatima ta ke , " ah mutumin ya haka tun d'azu na kiraka amma sai yanzu , ko dai madam ta rik'e ka ne , ya fad'a had'e mik'a masa hannu domin suyi musabaha" , shi dai Ahmad bai ce k'ala ba , suka juya suka nufi d'akin Fatima, a lokacin ta farka har nurses sun taimaka mata tayi wanka tayi sallah , da sallama suka shiga amsawa tayi had'e da kallon k'ofa , Dr Sadeeq ne ya fara k'arasawa cikin d'akin had'e da zolayar ta ah lallai kin warke irin wannan kwalliya haka , ya fad'a ya nunawa Ahmad wajen zama Wanda ya kafe a tsaye yana kallon yarinyar da ya kad'e , kyakykyawa ce ya fad'a a ransa , zama yayi , doctor ya gabatar da shi a wajen Fatima , gaisar dashi tayi cikin murya mai sanyi amsawa yayi, kuma bai d'auke idonsa daga kanta ba , shi dai yana yiwa yarinyar nan kallon sani , " ya sunanki ya fad'a yana dubanta ", Fatima " abin da tace kenan ta juya suka cigaba da hirarsu da doctor jefi jefi yake sanya musu baki , ya dad'e sosai daga bisani ya nufi gida bayan yayi mata sallama ya tafi ita kuma ta kwanta saboda har lokacin bata dawo daidai ba.

Sai da Fatima ta kwana kusan bakwai ta warke garau , amma ba ta tab'a fad'awa kowa maganar y'an uwanta ba , a nashi b'angaren Ahmad yayi tunanin ya tambaye ta ko dan ya mai da ta danginta amma ganin cewar ba ta da lafiya ya sanya sai a yau ya tare ta da zancen dangin na ta , bata b'oye masa komai ba dan tana ganin kamar wannan wata mafaka ta samu ko Allah zai sanya ya taimaka mata ta wani fannin ganin cewar yana da tausayi , jin labarinta ya sanya yayi alk'awarin cewar zai tafi da ita cikin danginshi kafin ya san me zai yi akai .

Satin Fatima biyu Dr Sadeeq ya ba ta sallama , har bakin mota Dr ya raka su , sannan ya koma su kuma suka fita daga cikin asibitin zuwa gida Alhaji Ahmad.........

Please
Share
&
Comments

To be continue...........

DAN ALLAH AYI HAK'URI DA WANNAN SABODA NA GAJI .

SAI ALLAH YA KAIMU WANI SATIN ZAN K'ARAYIN TYPING , LUV U FAN'S🥰🥰

🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿

🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸
(True life story)

🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸

NA SADAUKAR DA LITTAFINA NA KISHIYAR UWA GA, PHAREEDA , INAJIN DAD'IN COMMENTS D'INKI SOSAI DA SOSAI, ALLAH YA BIYAKI.🥰

SHAFI NA 19_20

Ko da suka k'arasa cikin unguwar , tun daga bakin layin Fatima ke rarraba idanu , " oh ni Fatima na kawo kaina ga mahallaka , yanzu ace ni zanyi rayuwa anan , anya ma kuwa ba d'an mafiya na biyo ba , innalillahi wa'inna ilaihir raji'un , shikenan tawa ta k'are , duk abinda take fad'a tana fad'ar shi ne a cikin zuciyarta" , a take tayi dana sanin gudowarta daga k'auye , dama ta tsaya an d'aura mata auren da bilya da wannan yawon gashi bata ga tsuntsu bata ga tarko, shikenan a banza a wofi wasu mutanen zasu cinye ta , garin lalubar dangin mahaifiyarta ta b'ige da zuwa mahallakarta madadin ta ganta a zariya sai gata a Kaduna , ta shiga zurfin tunani da tashin hankali ta yadda har su ka iso k'ofar gidan mai gadin gidan ya bud'e suka shiga bata sani ba .
Chapter 11 · 0% Book details