← Book details Kishiyar Uwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 26

Sashe 4

Kishiyar Uwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asabe na zaune a tsakar gida aminiyarta ta shigo da gudu cike da alamar firgici a fuskarta , dubanta Asabe tayi cike da haushi ta ce " wai baraka yaushe zakiyi hankali ne wai ke ba kiga cikin da ke jikinki ba kika shigomin irin haka salon ki zo haihuwa ki mutu " dakatar da ita Baraka tayi ta hanyar cewa " yo ba gwarama mutuwa ba an san lokacin ka ne yayi akan wannan bala'in da ya ke shirin tunkararmu" " wanne bala'i kuma Allah ya tsaremu da shi "ta fada tana tura d'an kwalinta gaba har zuwa girarta , " ke Asabe da labari na zo miki naga alamar ke baki sa ni ba ko " ? Ta tambayeta ta jiran amsarta "dan Allah ki fadamin mana kina wani jan zancen" ta sake tura dan kwalinta gaba, "to wallahi mijinki yqna nan yana shirin k'ara aure" , "kan uban chan ba Ankara da garin da ta b'arar ba , ta zunduma wani uban ashariya ," haba biri yayi kama da mutum , shiyasa ya kasa sukuni a cikin gidan nan har ya tafi fataucin nan ashe ya san abin da su ke shiryawa shi da matsiyatan iyayan na shi ", lallai ya taro wa kansa bala'i wallahi ," a'a tsaya mana ai ba hargagi zakiyi ba " cewar baraka da ta ke sake neman wajen zama, " tsayawa zamuyi mu fitar da maganin matsalar da ta ke tunkaro mu", zaman 'yan bori tayi ta zuba uban tagumi hannuwa biyu biyu , " inajinki baraka" ta fada dana kallonta " me ki ke so ayi yanxu "? Ta tambayeta tana kallonta , " kinsqn babu yadda za'ayi nabar wata mata ta auri malam wallahi kina ganin bana haihuwa ta yaya zaayi na bar wata ta shigo ta haifawa malam iliya d'a musamman ma na miji ta yadda zata cinye dukiyarsa " " kinyi gaskiya kuwa aminiyata" yanzu kinaso a tsayar da maganar aurenko"? Ta tambayeta ," eh " ta bata amsa " to yanzu tashi zakiyi mu tafi chan kauyen lajawa akwai wani hatsabibin boka , sunanshi boka sha yanzu magani yanzu , amma ina fatan kinada kudi a hannunki "? Ta tambayeta tana kallonta ," eh da akwai wanda malam ya barmin da zai tafi ban tab'a komai ba ", " to tashi zakiyi mu tafi dan kinsan da zafi zafi akan daki karfe", " eh to bara na Shiga na dauko mayafina" ta shige daki a birkice domin dauko mayafi ,sannan su ka yi waje cikin hanzari.

Mata mu kula! Mu kula ,a kula! , kawaye sukan kawo cikas sosai a zaman aure , kar ki bari kawarki ta rudeki takaiki ta baroki akan tudun dana sani , sirrinki ki boyeshi karki sake ki bayyanawa kawarki halin da kike ciki da mijinki , zata sanyaki kiyi danasani a rayuwarki da rayuwar aurenki baki d'aya, daga k'arshe mijinki ya sakeki , in batada aure ta aure miki shi , Allah ka shiga tsakanin na gari da mugu amin .

Basu k'arasa cikin dajin ba sai da sukayi tafiya sosai har rana ta fad'i kana suka karasa , dan har Asabe ta sare amma Baraka ta k'arfafa mata guiwa da kyar su ka karasa bayan bakar wahalar da su ka sha k'afafunsu sun kumbura sosai sun jigata , kana su ka karasa wajen , tunda su ka nufi wajen Asabe takejin iface iface namun daji kukan tsuntsaye da sauransu , a haka su ka karasa ," Ku shigo da baya" cewar boka sha yanzu , cikin wata gabjejiyar murya, da sauri suka juya har suna kokarin bige junansu , Baraka ta zunduma ashar ta yiwa Asabe da nunin itama tayi wannan itace sallamar Shiva wajen bokan , aikuwa itama tayi , sannan ya basu izinin zama , su ka zauna ,Asabe ta bud'e baki zatayi magana yayi mata nuni da tayi shiru , zuwa kamar Minti biyar sannan ya bushe da wata mahaukaciyar dariya sai da yayi mai isarsa sannan ya dakata, yayi nuni da wata kwarya sai ta taho da kanta ta zauna a mazauninta kan wata tararriyar kasa , yayi nuni da ruwan cikin kwaryar aikuwa yayi bakikkirin daga baya kuma ya koma fari, aikuwa ya shek'e da dariya" angama bukatarki ta biya za'a fasa auren nagama komai , yanzu maganar aure babu ita na Sanya kiyayya mai karfi tsakaninsu " Myrna sosai Asabe tayi najin an fasa auren malam iliya ,su ka yiwa boka sallama da zasu tafi ya bata maganin da zata zuba masa a abinci da Wanda zata zuba tayi wanka sai turaren da zata sanya Wanda idan har ya shak'a to zai manta da kowacce mace a duniya sai ita, sannan suka nufi hanyar gida a lokacin anyi sallar magariba sannan su ka karasa gida , sai da suka huts sannan Baraka ta nufi gidanta itama, da kudirin aikata abinda boka ya sanyata ta kwana , dan tana tsammanin dawowar malam a tsakankanin wannan lokacin , a haka tayi bacci tattare da mummunan k'udiri a ranta.

A chan gidan su malam iliya kuwa anata shirye shiryen biki saboda wannan bikin na so ne , ana wannan yanayin malam iliya ya dawo saga fatauci , lokacin da ya je gidansa da yaga Asabe bata nuna masa wata alama ta nuni da cewa tasan zancen hakan ya saka ya ji dadi kuma yayi mamaki bisa ga yadda yasan qauye da gutsuru tsoma , amma yaga sab'anin haka, hakan ya sanyashi ya tafi gidansu domin gaida mahaifins. Tana fita Asabe ta yi shirinta tsaf da magungunan da bokq sha yanzu ya bata ta zauna zaman jiran malam ya dawo daga gidansu ..............

Please🙏🏻
Share
&comments.

To be continue........

Luv u all my fan's🥰🥰😍

🌿🌿🌿Nussad🌿🌿🌿
🌸🌹Kishiyar Uwa🌹🌸
(True life story).

🍁Daga alk'alamin Nussad🌸
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
Ina matuk'ar godiya gare ku masoyana , saboda nuna kulawarku ga littafina mai suna Kishiyar uwa , a gaskiya na rubuta shi ne badan komai ba sai don tunanin da nayi wannan shi ne abin da yake damun al'umma , idan mata taga an bar mata 'ya'yan abokiyar zamanta idan har basa shiri da ita to fa su ma yaran nata sun Shiga uku , dan Allah mata mu kiyaye wannan hakkin lallai sai Allah ya tambayemu a kanshi , ki sanya a cikin ranki idan da yaranki ake yiwa haka ya ya zakiji a cikin ranki , Allah yasa mu gyara amin.

Ina ganin comments naku gaskiya ina jin dadi , kuma ku ma burgeni , insha Allahu bazan baku kunya ba

Comments🥰
Maman Ammar
Kishiyar uwa🌹💞nicely sis Allah ykara basira ina matukar jin dadinsa wlh 🥰🥰

~phareeeda
Allah sarki Fatima zakisani kuka 😭😭😭😭😭😭😭😭

Duk naga comments ina godiya.

Shafi na5️⃣

Ko da malam Iliya ya k'arasa gidansu ya tarar ana ta shirye-shiryen biki , wajen mahaifinsa ya fara zuwa ya gaida shi amsawa yayi kana ya mishi maganar "angama komai da ake buƙata yanzu abinda ake jira shi ne saboda su na so su kai kayan aure da sadaki, saboda auren ya kusa, amsawa yayi da to , kana yayi godiya, ya yi masa sallama ya shiga cikin gidan wajen iyayen sa mata , nan ma ya tarar suna ta shiri sosai , ya gaida su ya mu su alkhairi, ya tsaya sai da su ka ga ma komai na harkar kai kayan auren, da sadaki sannan ya nufi hanyar gidansa.

A can gida kuwa Asabe ta gama har had'a komai da tasan boka sha yanzu ya ba ta, dan haka a halin da ake ciki malam Iliya kawai ta ke jira ya dawo gida, tayi wanka da magani ta shafa turaren da sauran kayan amfanin da ya bata za ta sanya masa a abinci.

Da sallama ya shiga a bakin sa , amsawa tayi cike da kwarkwasa , ƙamshin turaren da boka ya bata shi ya shak'a ai kuwa ta ke yaji kanshi yana juyawa , wanka ta jashi yayi, a hakan dai ta bashi wannan abinci ya ci , kana ya fada mata kanshi na yin ciwo zai kwanta rakashi tayi har sai da ta tabbatar da ya kwanta sannan ta fito daga ɗakin ta, fita tayi daga gidan domin sanar da k'awarta halin da ake ciki.

Har bayan magariba bai tashi ba har Asabe ta dawo daga gidan Baraka , sannan ya tashi daga baccin , zuciyarsa yaji ta b'aci gaba ɗaya yaji auren da ake shirin yi masa ya fita a ransa , yaji ya tsani yarinyar gabaki ɗayanta, haka ya kwanta ransa na b'aci, ko da gari ya waye mahaifinsa ya kirashi bai je ba , har aka kwana uku bai je ba , kai auren ya taho dangin sa nata harkokin biki amma shi banda shi, dan haka mahaifinsa ranshi ya b'aci yayi niyyar zuwa har gida ya same shi.

Da wata ranar talata lokacin saura kwana biyu a ɗaura auren mahaifin nasa yayi dirar mikiya a gidan, faɗa ya rufe shi dashi, sosai shi kuwa ko a jikin shi ,sai ma duban mahaifin na sa da yayi yace masa shi ya fasa auren daskarewa mahaifin nasa yayi abinda bai taba ji ba , juyawa yayi ba tare da yace komai ba ya tafi gida cike da damuwa, ko da ya sanar da matan nashi sosai su ka ɗauki zafi akan haka, amma da yayi musu bayanin yadda zasu fi ganewa su san ba laifin sa ba ne ba, sai su ka daina hargagin da su ke yi , a haka aka bawa iyayen yarinya hakuri abin ka ga k'auye gari fa ya ɗauka aka yi ta ƙananan maganganu, daga baya komai ya lafa, ita kuwa data ga haka sai ta saki jikinta tayi ta iya shegen ta abin ta , ta kuma mai da zuwa wajen boka sha yanzu kamar masallaci, mahaifinsa ya nema masa ak'alla yara sunyi biyar tana wargaza auren daga baya mahaifinsa ya hakura ya zubawa sarautar Allah idanu, yayin da tsanar Asabe ta dawo sabuwa a zuk'atan matan gida da yaransu .
Chapter 4 · 0% Book details