← Book details Kishiyar Uwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 26

Sashe 26

Kishiyar Uwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bayan sun koma ne, baba Asabe ke zaiya ne musu duk abin da ya faru, har da abin da ya faru da zainabu , tace" yaron nan ashe ba d'an arziki bane ba , ashe da ake cewa ya samu aiki a kudu , ba aikin Allah da Annabi ne ya kai shi ba, bayan aikin da yake yi , harda neman mata, watan su d'aya ta fara fuskantar k'alubale a rayuwar aurenta, da abun yayi tsamari , haka zai shawo kayan mayensa, ya shigo ya mata dukan tsiya , ya kawo mata yan mata karuwai , da k'yar tayi haihuwa d'aya a haka sai da ta Haifa masa wad'annan yaran , ba abinci , kullum sai duka , da k'yar bayan haihuwar jaririn nan ta samu Allah ya sanya ya sake ta , gashi ba kud'in mota , haka nan mak'wafciyarta ta bata kud'i da wadanda tayi aikatau ta had'a ta nufo gida, shi yana chan yana shek'e rayuwarsa a chan, ta fad'a tana matsar hawayen namada ", da k'yar su ka lallab'ata tayi shiru, sosai su ka jajanta mata, a ranar suka koma Kaduna da zama, amma kafin su tafi sai da su ka ajiye musu alkhairai da dama , sannan Fatima ta bada kwangilar a gyara gidan na su , ta bawa baba muhammadu jari , sosai tayi rabon bajinta wa dangin na ta , ana murna da komai su ka tafi duk da sun so su kwana amma mummy tace zata zo na musamman ta kwana, sannan su ka koma Kaduna.

A chan b'angare d'aya , bayan an saki LAILA da Aliya , sosai ta shiga harka da samari , ta had'u da wani saurayi , sosai rayuwarsu su ke yi, bai fada mata yana da cuta mai karya garkuwar jiki ba , sosai su ke mu'amalarsu , bata tashi farga da cewar ta kamu ba sai da ciwo matsananci ya taje wajen likita gwajin farko aka tabbatar mata da cewar ta kamu da HIV , kamar zata yi hauka su ka dawo da mummynta gida , rayuwa duk ta sauya mata , gashi mahaifinta yanzu karayar arziki ta same shi , haka dai ta k'arasa jinyar cutar ta tana karb'ar maganin gwamnati a asibiti.

Fatima ta koma gidan ta , soyayya mai tsabta su ke zuba wa, kullum tana godewa Allah da ya sauya mata rayuwarta zuwa mai kyau, a yanzu ta gama karatunta tayi jarabawar k'arshe su na jiran sakamako , saboda kamfanin Ahmad da yake k'asar waje yana buk'atar cigaba ya sanya yayi tunanin cewar gwara su tafi da iyalinshi chan , domin ita ma ta cigaba da karatunta a fannin Medicine.

A b'angare d'aya soyayya mai k'arfi ta ginu tsakanin doctor Sadeeq da Halima k'awar Fatima tun lokacin da ya ganta a sunan y'an biyu ya rikice mata, a yanzu dai an Sanya ranar aure sai dai fatan Allah ya sanya ayi da mu Amin.

Bayan komai ya kammala , su ka fara shirin tafiya kasancewar komai , ya yi kyau game da result na Fatima , hakan ya Sanya ana i gobe zasu tafi su ka shawarci junansu akan su kai ziyara asibiti, su bada taimako aikuwa , sunyi abinda ya dace , suna k'ok'arin fita daga asibitin Fatima taji ana kiran sunanta, da sauri ta juya , wata ta gani mai kama da LAILA sai dai wannan bata kai LAILA komai ba saboda a iya sanin Fatima LAILA ta kere mata da yawa, " baki ganeni ba ko Fatima , LAILA ta fad'a tana k'arewa Fatima kallo dama shi uban gayyar wato Ahmad , Wanda ya rumgume Al hassan a kafad'arshi , yayin Al hussain yana kafad'ar Fatima , bayani sosai tayi musu sannan su ka gane , aikuwa Ahmad yayi saurin jan Fatima domin ya tsani ganin LAILA a rayuwarsa , Fatima ce ta bashi hak'uri su tsaya su fuskance ta, LAILA hak'uri ta shiga bawa Ahmad dama Fatima , ta fad'a masa duk abinda ta masa, kama daga samun cikinta har zubar da shi da ta dinga yi, sosai yaji bakin cikin abun amma daya tuna da yadda LAILA take sai ya godewa Allah da ya sanya jininsa bai fito ta tsatsonta ba , sannan ta nemi yafiyarsa, yace shi ba komai, haka ma Fatima , ta zayyane musu abinda ke damunta sosai su ka jajanta mata, su ka mata al' kairi sannan suka barta tana zubar da k'walla na abinda ta yiwa rayuwarta , da tuni yanzu ita ke da wad'annan zuk'a zuk'an yaran, haka tana ji tana gani su ka tafi su ka barta .

Ana i gobe zasu tafi suka je suka yiwa Mummy sallama, dama sun je zaria sun yiwa maman Fatima sallama , da dare suka gama shirya kayansu tsab , tare da na yaransu.

Washe gari da misalin k'arfe takwas na safe jirginsu ya d'aga sai England, a babban birnin London suka sauka , sosai rayuwarsu ta sauya , Fatima ta fara karatunta a babbar jami'ar k'asar, sosai shi ma Ahmad ya mai da hankalinsa kan aikinsa da kuma iyalansa , rayuwarsu gwanin ban sha'awa.

Bayan wani dogon lokaci, wata mata na hanga tana ta fama da yara , " Mummy wallahi bani ne ba Al Hussain ne , wallahi ba ni na dake ta ba ,duk su ka fad'a a k'ok'arin su na kare kansu ", " to naji Fatima ta fad'a," zo nan habibty ki fad'amin waye ya dake ki, Ahmad da ke tsaye ya tambayi y'ar yarinyar wadda take ta zumb'ura baki gaba, haba Nusy ta fad'amin kinji " ," Daddy ba yaya Al Hussain ne ya dake ni ba ", " ah lallai zan gamu da shi , bari kiga , ya fara k'ok'arin tashi ya kamo su , k'ara su ka saka , suka rungume Fatima , ita ma ta rungume su , yana zuwa da Nusaiba a hannunsa aikuwa ya had'e su gabaki d'ayansu yana dariya , tare da basu sumbata kowannensu a kumatu , yana mai jin dad'i da Allah ya azurta shi da iyali masu aminci.

TAMMAT BI HAMDULLAH

ANAN NA KAWO K'ARSHEN LITTAFIN " KISHIYAR UWA ", KUMA INA FATAN KUNJI DAD'INSA KUMA ZAKU YI AMFANI DA ABINDA KUKA JI MAI KYAU SANNAN KU WATSAR DA WAD'ANDA BA SU DA KYAU .

INA GODIYA GA Y'AN MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION, DA WAD'ANDA SUKE YIMIN EDITING NA BOOK D'IN NAN.

INA GODIYA GA Y'AN KISHIYAR UWA FAN'S, ALLAH YA K'ARA MANA ZUMUNCI AMIN.

JINJINAR BAN GIRMA GA SIS HUMAIRA DA SIS FAREEDA , KUNYI RAWAR GANI SOSAI ALLAH YA SAKA DA ALKHAIRI AMIN.

NA SADAUKAR DA LITTAFINA GABAKI D'AYANSA GA , MAHAIFINA DA MAHAIFIYATA , ALLAH YA K'ARA MUKU NISAN KWANA MAI ALBARKA AMIN

INA GODIYA SAI MUN SAKE HAD'UWA CIKIN WANI SABON LITTAFIN NAWA MAI SUNA " BAK'AR GABA" INA FATAN KAMAR YADDA KUKA BI WANNAN SHI MA WANCHAN A SANNU ZAKU BISHI DOMIN JIN SAK'ON DA YA ZO MUKU DA SHI .

TA KU HAR KULLUM

NUSAIBA MUSA SALEH SABON RUWA
(NUSSAD)

PLEASE
SHARE
AND
COMMENTS

🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿
Chapter 26 · 0% Book details