← Book details Kishiyar Uwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 26

Sashe 25

Kishiyar Uwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A chan b'angare guda kusa , sosai Ahmad ya sanya anayi masa bincike, akan Wanda ya shigar masa gida a ranar da Fatima zata haihu, shaidar farko da aka samu a wajen mai gadin da ke kallon gidan Fatima ne, cewar LAILA ce da k'awarta ko da wannan magana ta isa ga kunnen Ahmad , ya razana sosai kuma yak'i gasgata hakan , amma yanzu ya gasgata, kuma abu kad'an yake jira ya sanya a kamo masa su , ko ya koma gida baya nuna mata damuwarsa , kuma har lokacin kowa al amarin gabansa yake yi , bai sanar da ita har a lokacin Fatima ta haihu ba, ita ma bata nuna masa ta sani ba , ganin anyi shiru da zancen ya sanya daga ita har k'awarta Aliya suka saki jiki, aka cigaba da harka da samarin bariki.

A b'angaren Ahmad, tun Fatima na kwana ashirin ya matsu ta koma , tun baya fad'awa Mummy yana jin kunyarta har ya same ta ya sanar da ita , amma fir tak'i, ko da ya tuntub'i Fatima da maganar ta shaidawa Mummy tana son komawa, k'in fad'a tayi , hakan ya hassala shi , domin yana buk'atar matarsa a kusa da shi da yaransa, sai ya d'auke musu wuta ya daina zuwa, ya maida kansa gun tabbatar da zarginsa akan LAILA, ya k'yale su , domin yanaso yaga iya gudun ruwan Mummy da Fatima.

AFTER 2 WEEKS.

A lokacin komai ya kammala na bincike , LAILA na zaune a falo tana shan ice cream aka k'wankwasa k'ofa , cikin gadara ta tashi ta isa wajen k'ofar tana tambayar ways , shiru aka mata , cikin fusata ta bud'e me zata gani y'an sanda , sun kusa bakwai maza sai mata mutum biyu , basu yi wata wata ba suka damk'i hannunta bayan sun bata shedar kamawa, sannan aka cilla ta bayan mota sai police station , ko da su ka k'arasa, tana ta so ta musu taurin kai aikuwa , ta sha jibga koni na tausaya mata 😩, DPO ne ya kira wayar Ahmad , ya shaida masa da cewar an kama LAILA tana hannunsu a halin yanzu aikuwa , yana wajen aiki amma haka ya tattara kayan aiki ya nufi office d'in y'an sanda.

Ko da ya k'arasa sosai LAILA tayi mamaki, da jin cewar wai Ahmda ya sanya a kamata , to me tayi abinda ta fara tambayar kanta kenan , amma sai ta dake, ko da aka fara fad'a mata abinda ya fara ai daskarewa tayi , bata gama dawo wa daga cikin duniyar da ta shiga ba, taji saukar takarda fara a hannunta , bud'ewa ya bata umarnin tayi , aikuwa tana bud'ewa ta zunduma ihu , " Ahmad ni zaka yiwa haka , ni zaka saka sakin ma na wulak'anci har uku ", " shi ne abinda ya kamata da a yi miki, domin dama na gaji bazan iya zama da wadda zata ga bayan iyalina ba , dama na gaji da halinki, dan haka kije na sauwak'e miki , kuka sosai ta shiga rairawa , anan Ahmad ya tafi ya barta bayan ya shaidawa DPO akan itama k'awar LAILAN a kamo ta , sannan ya juya ya tafi yabar LAILA a hannun y'an sanda, ya kuma shaida musu cewar da an gama zasu wuce kotu..............

INA GODIYA SOSAI DA NUNA K'AUNARKU GARE NI , KWANA BIYU KUNJINI SHIRU, BUSY NAKE SOSAI , FATAN ZAKU YI ENJOINING NA WANNAN PAGE D'IN , LUV U FAN'S😍😍😍😍

Please
Share
&
Comments

To be continue.............

🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿

🌸🌹 KISHIYAR UWA🌹🌸

(True life story)

🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸

SHAFI NA 47__48

Bayan ya tafi, y'an sanda biyu maza d'aya mace, suka jefa LAILA a cikin mota domin nuna musu gidan Aliya su cika umarnin DPO.

Ko da suka k'arasa a lokacin Aliya na tsakar gida tana rufe d'aki kasancewar ta samu labarin an kama LAILA ya sanya ta yi sauri had'a kayanta tana k'ok'arin barin garin, ko da ta ga LAILA tare da y'an sanda , tuni hantar cikinta ta kad'a , zawo mai k'arfi ya kamata , amma basu barta tayi ba su ka jefa su a mota aka nufi office, a wannan lokacin sai da suka ci dukan tsiya , sun ma fita a hayyacinsu , sannan aka rabu da su, duk wannan al'amarin da yake faruwa , mahaifan LAILA basu sani ba haka ma Mummy bata sani ba , ya kyale su sai sun gama girbar abinda su ka shuka sannan zai saka a mik'a su kotu, saboda mutuk'ar Mummy ta sa ni shirinsa ya wargatse kwata kwata , haka ma iyayensu , hakan ya sanya yayi shiru da bakinsa.

A chan b'angaren Fatima kuwa, daga ita har yaranta suna samun kulawa sosai a gurin Mummy, kuma suna kwana na talatin da biyar , hakan ya sanya ta shawarci Ahmad akan cewar Fatima tana yin arba'in za su tafi k'auye domin ganin gida tare da shaida musu al'amuran da su ka faru , sosai ya yarda da hakan shi ma addu'arsa bai wuce ya kalla wadda ta wahalar da matarsa ba , Allah kad'ai yasan hukuncin da zai d'auka akanta , ko da aka sanarwa da Fatima sosai tayi farin ciki dad'in dad'awa ta taji da mamanta za'aje , wannan kenan.

A chan chaji office kuwa, su LAILA sun sauya kamanni sosai baka gane su Ba, musamman ita LAILAN wadda hutu ya ratsa fatarta , abin gwanin ban tausayi , Ahmad da kansa ya ga ya dace akan cewar ya sanar da mahaifinsu, ko ba komai ai yanzu sun gasu, wayar mahaifin LAILA ya kira ya sanar da shi , aikuwa cikin tashin hankali ya nufi office d'in , haka ma mahaifin Aliya , sosai ransu ya b'aci musamman baban LAILA a ganinsa wai an tozarta y'arsa , ganin hargagin da su ke yi masa a kai yana k'ok'arin haddasa masa ciwon kai ya sanya ya bar office d'in, ko da ya sanar da Mummy bata ji dad'i ba amma , kuma hakan da yayi shi ne daidai , ta yi addu'ar Allah ya k'ara kiyayewa.

To da k'yar da sud'in goshi aka samu Ahmad ya hak'ura , akan kai su LAILA kotu , sai da aka kai ruwa rana , tin Fatima batasan me ya faru ba har ta sani , ta shaida masa ita kam ta yafe , ya k'yale su , wannan dalilin ya sanya ya k'yalesu .

Ranar da suka cika kwana arba'in aka d'auki hanyar kano , da Mummy ,Ahmad, da maman Fatima , da ita kanta Fatima sai y'an biyu , ko da suka k'arasa garin da k'yar Fatima ta gane gidan na su , saboda ya tsufa ya lalace , babu duk wani kayan more rayuwa kamar da, tun daga tsayawar su mutane suka fara lek'owa , mata ta Katanga , su na ganin ikon Allah , d'aya bayan d'aya su ka dinga fitowa daga cikin motar , abin mamaki ya bani wa jama'ah ganin bak'in turawa suna shiga gidan Asabe , to ko laifi tayi , a nan tsaye mutane suna kallo su ka shigewarsu.

Tsakar gida su ka tarar da wata tsohuwa ga tulin yara a gabanta , kuma da alama ba tsufan shekaru ba ne ba , kawai halin rayuwa ne , kallonsu ta shiga yi , domin ba wanda ta gane a cikinsu , daga cikin d'akin su ka jiyo maganar wata tsohuwa , " yanzu ke zainabu a haka zamu dinga zama da yunwa, ko fita bazaki yi ki barato mana abinci ba, ta fad'a tana shirin fitowa "," wallahi inna kinsan Ba bayarwa mutane zasu yi ba ,kawai mu zuba idanu mu gani, lah inna na manta kinga bak'i muka yi ", da sauri ta fito daga d'akin tana lalubar bango , Fatima da ke tsaye daskarewa tayi ganin wadda aka kira zainabu , kenan Abu ce ta koma haka, toh ina mijin na ta , duban ta ta kai ga inna Asabe innalillahi ta furta ganin yadda kamannin ta su ka sauya, ga makanta, oh rayuwa kenan duk gudunka iya ka abinda Allah ya sanya zaka tsaya toh fa anan zaka tsaya .

Sosai Asabe ta shiga rud'ani jin Fatima ce ta zo har da miji da kuma yara, ai abun bai bata tsoro ba sai da taji mahaifiyar Fatima tayi mata bayanin ko ita wacece , sosai kuka ya kufce mata , " nayi nadama marar amfani , Fatima ki yafemin nasan na k'untatawa rayuwarki da yawa , amma ki yafe ni , komai da kika ga ya faru da ke nice sila, ta juya ga mahaifiyar Fatima, wadda imani ya k'ara cika zuciyarta ganin wai Asabe ce a wannan bigiren , nan ta shaida mata cewar ba komai ta yafe mata, shi kansa Ahmad Wanda ya k'udurci yi mata wulak'anci ai sai ya nemi bakin yi ya rasa.

Kafin kace me gida ya cika da y'an uwa, Allah sarki har da baba Muhammadu, har kuka yayi, kuma yaji dad'in ganin Fatima da mahaifiyar Fatima, kowa mamaki ya kama shi ganin ashe dama Maimunatu bata rasu ba, sai da su ka sarara sannan , Fatima ta sulale ta nufi gidan rahina, sosai suka yi murnar ganin juna , sosai su ka yi hira sannan ta mata alkhairi , ta raka ta har bakin zaure , su ka gaisa da Ahmad sannan suka wuce...........

Please
Share
&
Comments

To be continue........

🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿

🌸🌹 KISHIYAR UWA🌹🌸

(True life story)

🍁 Daga Alk'alamin Nussad🌸

SHAFI NA 49__50

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

'KARSHE💃🏻💃🏻
Chapter 25 · 0% Book details