← Book details Kishiyar Uwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 26

Sashe 20

Kishiyar Uwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahmad zaune a falon mummy , wanda farin cikin ya rufe wai yau shine ya auri d'alibarsa kuma masoyiyarsa tun lokaci k'uruciyarta, yana zaune Mummy ta fito daga cikin d'akin na ta , "yauwa son ina son magana da kai ", gyara zamansa yayi yana sauraronta" a gaskiya Fatima bazata tare a gidanka ba yanzu , saboda haka na maka yadda kakeso to nima kamin yadda nakeso ", wata kuwa yaji ta d'ebeshi jingina yayi da jikin kujerar da yake kai , ya lumshe idanunsa, me yasa mummy tace haka , me yasa zata masa haka..........

HMMMMMMM TO FA , KO MEYASA MUMMY TACE HAKA, FAN'S ANYA KUWA MUMMY? YA ZA'AYI KIYI MANA HAKA KUMA?😭😭😩

Please
Share
&
Comments

To be continue........

🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿

🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸
(True life story)

🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸

SHAFI NA 35__36

" Mummy me yasa , ya tambaya kamar zaiyi kuka, idanunsa sunyi jazur da su alamar b'acin rai", duk da Mummy ta tsorata da yanayin da ta ganshi amma sai ta yi kamar bata ganshi ba " Ahmad ina da dalilai masu k'arfi wanda ya sanya bazan baka Fatima ba yanzu, dalilina na farko shine Fatima k'aramar yarinya ce bata san komai game da rayuwar aure ba sannan kanaso ka had'ata da LAILA a matsayin matanka, wanda hakan babbar illah ne ga rayuwarta , sauran dalilin sai lokaci yayi zan sanar da kai ko menene, yanzu lokacin da za'a bata dama ne tayi karatunta , mu barta , hakan yafi al'ala ", shi dai tunda ta fara magana ya kasa gane inda maganarta ta dosa , ita kuwa Mummy da gayya ta fad'a masa haka amma ita kad'ai tasan dalilin da ya sanya ta hana Fatima tarewa a gidan mijinta, ganin abun bana k'are bane ya sanya ya mik'e jiki a sanyaye ya nufi hanyar falo, hajiya na ganin shi , taji tausayin shi amma ta k'yale saboda tana da wani buri na daban akan Fatiman.

Toh ko da mummy ta sanarwa da Fatima shawarar da ta yanke taji dad'i duk da cewar itama bata fad'a mata asalin b'oyayyen sirrin na ta ba , wanda daga ita sai mahaliccinta suka sani.

A haka satittika suka dinga wuce wa, tun Ahmad baya nuna damuwarsa akan hanashi matarsa da hajiya tayi har ya fara nunawa , akwai wata rana da yazo takanas ya cire kunya , ya fad'awa hajiya amma fir ta kafe ta nuna batasan zancen ba, gashi LAILA ma har a lokacin iyayenta sun hana ta dawo wa, wai sai ta k'ara hutawa sosai ita kuwa duniya tayi mata kyau yawo kam ba inda bata zuwa duk kuwa da aure akanta , dan bayan barinta gidan Ahmad , ta je kasashe kusan guda uku, ba tare da ya sani ba a cewar iyayenta wai yawon bud'e idanu, kuma wanne mutum ya tsayar da ita zata tsaya ta yi magana da shi har ma ta bada phone number d'inta ga mutum, dan tana bin maganar k'awayenta na cewar itama ta shiga duniya a dama da ita ta mori abun arzik'i, lokacin da ta fara wannan rayuwar ji tayi ai a da duk kuwa da mai kud'i ta aura amma a cikin kurkuku take, saboda had'uwar ta da wani guy d'an gidan wani tsohon minister, Alhaji Badamasi Ali , suna soyayya a yanzu sosai ,duk da cewar ta fad'a masa tana da aure ,amma ta yi masa k'aryar cewar mijin na ta ya saketa, rayuwa kam sosai ta sauyawa LAILA tana cin karenta babu babbaka , k'awayenta kuwa su Aliya fire abun nema ya samu suka dinga ingi zata , a cewar su ita ma kamata yayi tunda basu yi aure ba itama bazata zauna ba.

A b'angaren Fatima kuwa, sosai ta maida hankalinta akan karatun ta, kasancewar sun shiga ajin Senior ne , sannan a b'angaren science take , Halima ma sosai take karatu kasancewar ta samu k'awa mai kaifin basira, zuwan Halima kusan biyar gidansu Fatima bayan da aka d'aura aurenta da Ahmad, amma tun zuwan Fatima na farko , tayi tambayar duniya mummy tace ta tambayi mijinta, kuma ta tambaye shi ya hana ta, shi ma tunda suka masa haka , sai ya ja zarensa, ita dai mummy wani sa'lin abun har dariya yake bata, shi kuwa Ahmad a nashi ganin da had'in bakin Fatima aka hana shi ita, in ba haka ba ai sai ta fad'awa Mummy cewar ita gidan mijinta take so, chab kaji fa wata rashin kunya wajen Ahmad🤪.

Mummy ce ta masa magana akan dawo war LAILA , ya fad'a mata yayi magana da mahaifinta amma yace har yau bata gama hutawa ba, Allah ya kyauta abinda tace kenan ta juya ta shige d'aki ta bar shi a tsaye, shi yayi tsammanin ma zata dawo ma sa da matarsa ne kawai tunda ita LAILA iyayenta sun hana ta dawo wa, a gaskiya fa yana buk'atar matarsa , toh ko kuma kawai zuwa zai yi Mummy bata nan ya d'auke ta ai bazata dubi tsabar idonsa tace ya dawo da ita ba, kai akwai rashin kunya kuma, haka dai ya gama tsayuwarsa ya juya ya fita, ya nufi gidansa.

8 MONTHS LATER.

Fatima ce ta shigo cikin falo sai nishi take yi alamar hajiya da yunwa da take addabarta, kasancewr sun fara exam , hakan ya sanya bata samu wani bacci na kirki ba, tana shiga bata ma lura da mutum ba , kawai ta shige d'akinta, tana shirin kulle k'ofa dan tana so ta shiga wanka, tasan Mummy ba ta nan amma tasan ta kusa dawo wa, dan haka take ta sauri tayi wanka, ji tayi an tura k'ofar d'akin baya tayi tai taga taga zata fad'i yayi sauri rik'eta team a jikinshi , k'ok'arin kurma ishu take yi , ganin zata tara musu jama'a ya sanya ya rufe mata bakinta da tafin hannunsa , cikin kunnenta ya fad'a ma " its me", gauron numfashi ta sauke , sanin ko waye,rungume ta tsam yayi a jikin shi , ita kuwa ba abinda takeyi sai k'walalo idanu waje, bayanta ya shiga shafa mata a hankali, yana magana" daughter d'in mummy har da ke aka had'a baki aka hanani ke ko, me yasa kika biyewa mummy, da takeson raba mu , ya fad'a yana k'ok'arin kai bakinsa ya zuwa na ta, k'ok'arin kaucewa ta shiga yi ya sanya ya rik'e ta tsam yadda baza ta iya k'wacewa ba , jin lallausan bakinsa cikin na ta ,karamar sumewa tayi , sai da ya gama jagulata iya son ransa, ganin da yayi tsayuwa na k'ok'arin gagararsu ya sanya ya jata har kan gadonta, still bakinshi na cikin na ta, ita kuwa, ido yayi wuri wuri anji sabon hannu , wata masifaffiyar kunyarsa take ji , shi kuwa sai da ya gama bidirinsa sannan ya d'aga ta ya rungume ta ajikinsa , sosai Fatima yayi enjoying na wannan al'amari da ya kasance tsakaninsu amma kuma tana bala'in jin kunyar yallab'an, k'ok'arin tashi ta shiga yi , hakan ya sanya ya k'ara matse ta , sannan ya fara magana cikin muryarsa kamar ta masu jin bacci , yana sanya mata albarka, ta dole ya sanya ta tayi alk'awarin in dai ya zo gidan Mummy zata dinga barin shi yana yin abinda ya mata yanzu, sai da ya gama , sannan ya fito har lokacin Mummy ba ta dawo ba , ya nufi motarsa ya shiga ya kunna ya bar gidan cike da nishad'i.

ONE YEAR LATER.

Alhamdulillah , Ahmad na zaune a falon gidansa , wayarsa tayi k'ara , a wannan lokacin iyayen LAILA sun dawo da ita , amma sun gindaya zarud'a da dama, ya kuma aminta da su kasancewar yasan shi ma abinda ya k'ulla , dan rashin mutuncin da su ka masa bazai k'yale ya tafi a banza ba, ita kuwa LAILA duk wasu al'amura da take yi a baya bata sauya ba sai ma k'aruwa da tayi , kuma tayi sababbun samari duk da tana tare da d'an gidan minister, shi kuwa Ahmad kusan kullum in dai yaje gidan Mummy ya tarar bata nan, kuma Fatima tana nan sai ya kwashi romonsa , duk da ba wani abu da yake shiga tsakaninsu amma romancing kuwa tana shansa, tun bata saba ba har ta zama gwana.

D'aukar wayar yayi , sabuwar lamba ya gani, da kamar bazai d'aga ba kuma sai ya d'aga, cikin mutunci su ka gaisa da mutumin , a nan yake sanar ma sa da cewar shine wanda yasan inda kakan nin Fatima suke, ya dawo daga fataucin da ya tafi , cikin farin ciki , ya amsa masa suka gama maganar akan sati mai kamawa zasu zo ya kaisu sosai ya masa godiya , ya ajiye wayar , cikin hanzari ya d'auki mukullin mota ya nufi gidan Mummy.

Ko da ya k'arasa a lokacin suna falo a zaune, yayin da Fatima take tsefewa mummy kitson da ta mata, cikin fara'a ya gaida mummy ita ma Fatima ta gaida shi ya amsa, al bishiri ya musu na cewar sati mai kamawa zasu tafi zariya domin an samu labarin dangin Fatima na wajen mahaifiyarta, Fatima da ke zaune ji tayi kamar ta tashi ta taka rawa dan murna, godiya kam ya shata ba adadi, murna ta shiga yi ji take yi kamar ta janyo satin ya zama gobe,jin kiran sallah ya sanya Mummy mik'ewa ta nufi bed room d'in ta domin yin sallah, matsawa yayi kusa da ita " me zan samu ya fad'a yana kallonta, dan kinsan sai kin bani tukwici na , rufe fuska tayi , ganin haka ya sanya ya d'auke ta chak zuwa d'akinta , sosai ya murzata son ranshi , sannan yayi wanka a ciki yayi alwala ya nufi masallaci , ita ma hakan ta kasance sai da ta yi wanka sannan tayi sallah.

ONE WEEK LATER.

Fatima tun da asubah ta shirya , domin a yau ne zata ga iyayen mahaifiyarta , a yau ne zata ga ko hoton mahaifiyarta ne , hajiya tayi da zama dan haka ta fito falo ta zauna, Ahmad kuwa bashi ya zo gidan ba sai karfe goma da rabi na safiya a lokacin Fatima ta k'agu , yana zuwa ba dad'ewa mummy ma ta fito suka yi Karin kumallo sannan suka dauki hanyar zariya.
Chapter 20 · 0% Book details