← Book details Kishiyar Uwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 26

Sashe 15

Kishiyar Uwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A b'angaren Fatima kuwa, sosai ta ke karatun ta cikin hazak'a , kuma halinsu yazo d'aya da Halima, dan a waje d'aya suka bambanta da juna shine , ita Fatima miskilace , while Halima kuma na da surutu da yawa, jarabawar farko , Fatima ta d'auki first class , Halima kuma second class, sosai yallab'ai Ahmad ya ji dad'in haka , yasan kuma ba asarar kud'insa yakeyi a banza ba, kyauta ta musammam yayi mata , kuma had'a mata da waya k'irar IPhone 11 pro, murna sosai tayi , da wannan kyauta bayan sun samu hutu Fatima ta tambayi hajiya kan tanasan taje gidansu Halima , hajiya a barta , ta kuma fad'awa driver ya kaita , sosai su ka yi murna da ganin juna, har k'arfe bakwai , sannan ta koma gida bayan mahaifiyar Halima ta bata kyauta da kyar su ka rasu, ko da ta isa gidan , a falo ta tarar da hajiya da yallab'ai , sannu da gida ta musu sannan ta nunawa hajiya kyautar da mamansu Halima ta mata, ran Ahmad ne ya b'aci au dama fita take yi any how any time , sai da ya bari bari hajiya ta tafi d'akinta sallah , sannan ya kutsa kansa d'akin Fatima a lokacin ta idar da sallar isha'i kenan , fuskarsa babu walwala, " ke dama yawo like zuwa, ya tsare ta da idanu yana jiran amsarta ", sosai ta tsorata , dan haka cikin rawar murya tace" am...am..ba.. ba haka bane ba , wallahi..... ba ta k'arasa ba ya katse ta " kar na k'ara ganin k'afarki a waje kin tafi yawo kinji na fad'a miki ", sannan ya juya ya fita, saboda ranshi ya b'aci ko sallama bai yiwa hajiya ba fice daga gidan ya nufi gidansa, ita kuwa Fatima zama tayi ta fashe da kuka sai da ta yi mai isarta sannan ta yi shirin kwanciya bacci , shi kuwa ko da ya k'arasa gidan ko takan LAILA bai bi ba ya kwanta . amma ne fafur bacci yak'i zuwa, ransa ya kai mak'urar b'aci , minti bayan minti sai ya juya yayi tsaki , to shi menene ma zai dameshi dan ta fita, ni kuwa nace muje zuwa malam yallab'ai Alhaji Ahmad, hhhhhhh. sai da tsakar dare sannan ya samu bacci ya d'aukeshi, bayan ya gama tunane2sa ko na menene oho🥴

A b'angaren LAILA ma gajiya tayi da jiranshi , ganin bai dawo ba sai kawai ta kwanta ita ma , kasancewar ita ba ta damu da damuwar wani ba ta ta kawai ta sa ni.........

DANALLAH A DINGA YIMIN SHARING NA BOOK DIN NAN PLZ👏🏻

Please
Share
&
Comments

To be continue........

🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿

🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸

(True life story)

🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸

CHAB ANA WATA GA WATA GASKIYA BAZAMU LAMINTA BA ACE KHAF BABU MASOYAN LAILA INA, AI MU GASKIYA MUNA BAYAN LAILA 100%.

HMMM SISTER BABU RUWA NA IN KIKA HAD'U DA FANS D'IN FATIMA , ZAKIYI BAYANI🥴😝

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

SHAFI NA 25_26

Washe gari da safe ko fitowa baiyi ba, saboda rashin baccin da ya samu jiya, LAILA kam koda ta fito ta tarar bayanan a zatonta ya fita hakan ya bata damar ficewa daga gidan bayan ta barwa Aisha mai girka musu abinci sallahu, akan abinda zata girka musu.

A chan b'angaren Fatima ma bata fito ba sai wajen k'arfe goma na safe , Mummy bata taso ta ba kasancewar tayi tunanin ko unguwar da taje ne ya sanya bata tashi da wuri ba, batasan al ' amarin da ya faru ba , tsakanin yaran nata guda biyu, bayan Fatima ta tashi sai da tayi wanka duk da fuskarta a d'an kunbure take hakan bazai hana mutum ya gane taci kuka ta k'oshi ba, da sallama ta shiga d'akin mummy , " yauwa haba daughter, ina ta tunanin ko lafiya yanzu nake shirin in tashi inje in duba ki , mummy ta fad'a tana k'ok'arin juyawa saboda dama ta bata baya tana kallo cikin d'akin ", juyawa tayi jin Fatiman tayi shiru , " innalillahi lafiya ke kuwa naga fuskarki duk ta tashi , meye ya sameki , cikin kad'uwa Mummy ke fad'ar haka",sai a sannan Fatima tayi k'ok'arin bud'e bakinta sannan ta ce " Mummy kaina yakeyi min ciwo tun jiya da daddare, ta fad'a tana k'ok'arin kawar da k'wallar da ta taru a idanunta", janyota jikinta tayi sannan ta tambaye ta taci abinci girgiza mata kai tayi alamar a'a , umartarta tayi da taci abinci sannan ta sha magani da to ta amsa , sannan ta juya ta fita, ta nufi dinning area.

A chan b'angaren kuwa sai sha d'aya na safe ya farka , a lokacin baccin da yayi ya saukar masa da ciwon kan da ya dawo gida yanayi, toilet ya shiga yayi brush , yayi wanka , kasancewar yayi sallar asubah, ya sanya yana gama feshe jikinshi da turare ya nufi d'akin LAILA kasancewar duk a up stairs d'in yake, da sallama a bakinsa ya tura , amma ne yana shiga yaji shiru tsammaninsa tana toilet dan yaji zubar ruwa, amma kusan 20 minutes, babu wanda ya fita a toilet, dan haka ya k'arasa bakin toilet d'in ya k'wank'wasa , shirun da yaji ne ya tabbatar masa da bata ciki , aikuwa rufe band'akin yayi , baya ya kashe ruwan , sannan ya nufi down stairs, a k'asan ma dai bata nan , Aisha mai girka musu abinci ce , ta fito daga kitchen, da alamar ta gama aikinta zata koma masaukinsu na masu aiki, " am ina matar gidan , ya fad'a kamar ba shi yayi maganar ba", da sauri ta rusuna har k'asa ta gaidashi sannan ta shaida masa ta fita, gyad'a kai kawai yayi kasancewar ransa yakai k'ololuwar b'aci, ya rasa mai ya sanya LAILA har yau bazata chanza ba , nuni yayi mata da hannu alamar taje, dan haka ta tashi ta fita abinda , shi ma hanyar falon ya nufa, yana fita ko abinci bai nema ba, ya shiga motarsa , gateman ya bud'e masa , ya cilla hancin motarsa ya nufi gidan Mummynshi.

Fatima tana zaune tana cin abinci , duk da ranta bayaso kasancewar har yanzu bakinta ba appetite, da sallama ya shigo cikin falon , ba kowa a cikinshi , Fatima dake zaune tana ganinshi gabanta ya fad'i dan yanzu wani mugun tsoronsa takeji, shi kuwa bai ma kula da ita ba , gadan gadan ya nufi dinning area'n kasancewar yunwar da yakeji ga b'acin rai na fita LAILA bata tambaye shi ba, zama yayi k'ansa a k'asa, kamar daga sama ya tsinkayo muryarta na gaida shi, amsawa yayi sannan ya yi mata nuni da alamar ta zuba mishi abincin , aikuwa cikin rawar jiki shiga zuba mishi abincin , kunun tsamiya ne da kosai sai k'amshi tarugu yake yi , sannan farfesun hanta, sai kuma shayi Wanda tasan dole zai buk'ata, shi kuwa duk wani motsinta idonshi na kai , amma sai ya nuna kamar ma ba kallonta takeyi ba , hakan ne ya bata damar fecewa bayan ta gama zuba mishi abincin, da ido ya bita, kasancewar yanason yaga mai ya sanyata rawar jiki haka, da ya tuna kuma da abinda ya faru jiya murmushi kawai yayi, sannan ya fara cin abinci.
Bayan ya kammala a lokacin Mummy ta fito da shirin fita unguwa gaisawa suka yi sannan ya mata a dawo lafiya , har ta kai k'ofar falon ta juyo had'i da cewar " yauwa ka sanya k'anwar taka ta sha magani , batajin dad'i ", da kanshi kawai ya amsa sannan ta juya ta fita shi kuma ya kishin gid'a, ya fuskantar TV saboda anayin labarai.

Lokacin da aka kirawo sallah , hakan ya sanya ya nufi toilet d'in Mummy alwala yayi , sannan ya nufi masallaci, ko da ya dawo tana falo a zaune, sannu da zuwa ta mishi , ya amsa yana satar kallonta, " ki kawomin abinci nan, abinda ya fad'a kenan yana gyara zaman shi a jikin kujerar", cikin sauri ta nufi kicin d'in , da kallo ya bita kawai , ko da ta gama zuba mishi abincin, kallonta yayi had'i da cewar " ke kinci ne" kai ta girgiza alamar a'a , " kurma kika koma, ya k'ara jefa mata wata tambayar, " a'a kawai tace je ki d'auko chokali", bakinta ta motsa alamar tana son yin magana ganin ya had'e fuskarsa ya sanya ba musu ta d'auko, nuni yayi da ta sanya ciki , ta sanya sannan suka fara cin abinci, cikin nutsuwa take ci , shi kuwa gogan duk lomar da zata kai bakinta sai ya kalla, kwata kwata bata wani ci da yawa ba ta tashi alamar ta k'oshi , wani mugun kallo da ya zuba mata shi ya sanya dole ta koma ta zauna suka ci gaba da ci, bayan sun gama ya sanya ta d'auka magani , cikin ya mutsa fuska , ta zuba a baki ta kora da ruwa, sannan ta nufi d'akin ta .

A b'angaren LAILA kuwa, sai k'arfe biyar ta koma gida , ko da ta shiga , ganin Aisha a kicin tana girkin dare , hakan ya sanya ta tambaye ta ko ya dawo, anan ta shaida mata ai dama bai fita ba, sai bayan ta fita sannan ya fita, kasancewar LAILA y'ar duniya ce hakan bai sanya ta damu ba tayi shigewar ta d'akinta.

Sai bayan sallar isha'i sannan ya koma gida , bayan ya yi musu sallama , ya nufi hanyar gidanshi, ko da ya koma bai nunawa LAILA yasan ta fita ba, har tayi zaton ko Aisha k'arya ta mata , shi kuwa yana sane , amma ya share ta , saboda ya gane bazata shiryu ba, sai wani ikon ubangijin.

Ana cikin haka , aka koma makarantar su Fatima , sosai tayi murna da komawar ta su kasancewar ba wani Hutu ne sosai ba, ko da ta koma yallabai shi ya ci gaba da kai ta makaranta kafin a samu mai kaita , na musamman a cewarsa😝🥴😳.
Chapter 15 · 0% Book details