← Book details Kishiyar Uwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 26

Sashe 14

Kishiyar Uwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shekararta d'aya Allah ya azurta ta da samun haihuwa ta haifi jaririn d'anta namiji Wanda yaci sunan Ahmad, sosai ake nunawa jariri gata da soyayya , musamman Maimunatu k'anwar hajiyan, Ahmad ya tashi cikin gata , shekarar goma a lokacin ya gama primary zai tafi secondary akayi auren k'anwar hajiya wato Maimunatu , aka kaita garin kano, sosai basu ji dad'in rabuwa da juna ba amma ba yadda suka iya, haka suka hak'ura.
Ajin Ahmad biyu a secondary , Allah ya azurta Maimunatu k'anwar mahaifiyarsa da samun k'aruwar yarinya mace hakan yayi masa dad'i sosai ganin cewar dama bai tab'a zuwa gidan gwaggon ta sa ba, amma kash lokacin yazo musu ana dab da fara jarabawa , haka ya hak'ura , ya gama makarantar secondary da kwali mai kyau , a lokacin business din mahaifinsa ya bunk'asa dan har k'asar waje yake fita , a haka Ahmad ya fara makaranta , toh a wannan lokacin Allah ya had'a shi da LAILA, y'ar gidan Alhaji Abbas mai dollar , tunda LAILA ta d'ora idanunta akan na Ahmad , taji ta kamu da sonsa, tun baya lura da ita har sai da tasan yadda akayi ta cusa masa soyayyarta a zuciyarsa , sunyi soyayya sosai , a lokacin da iyayensu suka sani abin ya musu dad'i sosai ganin ko wanne a cikin yaran nasu daga babban gida ya fito , a wannan lokacin kuma Ahmad ya tafi bautar k'asa a wani k'auye a kano cikin k'aramar hukumar takai , bayan ya gama bautar k'asarsa ne aka d'aura musu aure kuma ya tafi da LAILA k'asar wajen domin k'aro karatun na sa, a farkon aurensu sosai LAILA takeyi mishi biyayya , sun zuba soyayya amma daga baya kuma sai abin ya chanza salo rashin mutunci sosai ta farayi masa , ya rasa gane kanta , a iya saninsa LAILANSA bata da mugun hali amma ya akayi ta fara nuna masa wani hali na daban, babbar matsalarsa guda d'aya itace ta rashin haihuwa , da farko ya zaci yana da matsala amma da akayi masa bincike aka gano ai lafiyarsa k'alau , yayi nacin duniya LAILA taje a duba ta amma tace ita ba inda zataje ai haihuwa ta Allah ce, baisan da gangan LAILA take shan magungunan hana d'aukar ciki ba , bayan tabi shawarar k'awayenta , su Aliya fire, lokacin da ta sanar dasu tana da ciki suka ingizata ta zubar da shi a cewar su wai zata tsofe da wuri , tun daga nan take amfani da maganin hana d'aukar ciki , Allah sarki ko shi Ahmad d'in baima San tayi cikin ba kuma an b'arar masa da abinda yake nema ido rufe, a haka suka yi shekarun da zasu yi su ka dawo Nigeria , ko da suka dawo yaso su zauna a gidansu amma tace ita za'a takura mata , haka bada yaso ba ya gina musu gida , a wannan shekarar da su ka dawo , Allah ya yiwa mahaifin Ahmad rasuwa sunji rasuwar ba kad'an ba amma daga baya su ka hak'ura suka dangana , su ka ci gaba da rayuwa ,Ahmad kuma ya ci gaba da kula da kamfanin nikan da mahaifinsa ya rasu ya bar masa.

CIGABAN LABARI.

Ranar litinin da wurwuri Fatima ta shirya , domin tun dare hajiya ta sanar da ita cewar da safe , yayanta zaizo ya kaita makaranta , dan haka kafin k'arfe bakwai ta gama shirinta tsaf , tana jiransa , a bakin k'ofar falo su ka yi kicib'us lokacin ya shigo ita kuma zata fita , da sauri ta dafe k'irjinta tsabar tsoro dan bata zata shi bane ba, " yallab'ai ina kwana , ta fad'a tana dubansa ", shi kuwa lulawa yayi chan duniyar tunani , ya'akayi yarinyar nan ta girma , to kwata2 kwana nawa rabona da ita , ko da yake dama wahala ce kuma tana sanya haka, " yallab'ai fa ina gaisheka ," sai a sannan ya farga sannan ya amsa , tambayarta yayi ina hajiya ta fad'a masa tana cikin d'aki , juyawa yayi yana tunanin girman da Fatima tayi a k'ank'anin lokaci, gashi kayan makarantar sun amsheta gaba ki d'aya kayan maroon colour ne amma rigar tasu mai gida gidan bak'i a jikinta , kuma hijjabin d'an karamine dan da kad'a ya haura k'asa k'irjinta,da sallama a bakinsa , sun gaisa da hajiya , ya fad'a mata zasu wuce makaranta zai kai Fatima, sosai ta musu addu'ah sannan su ka fita daga cikin gidan bayan sunyi sallama da Fatima, toh a hanya sosai su ka yi hira , har ya dinga mata tambayoyi tana bashi amsa daidai ," am ni kuwa Fatima har yau bansan labarinki cikakke ba , ko za'a taimaka a bani nasha", ya tambaya yana murmushi , sosai ta shagala da kallonsa, har sai da ya juyo ya kalleta sannan ta sunkuyar da kai tana murmushi, shima murmushin yayi , dab da sun k'ara bakin gate d'in makarantar , anyi mata cike cike da komai na sabon d'alibi , sannan aka bata aji , shi kuma Ahmad ya tafi wajen aiki.
Koda aka kai ta a desk din da aka ajiye ta su biyu ne," sannu ta cikin bencin ta fad'a", " yauwa sannu" ," suna na Halima Nasir, nice too meet you", ni kuma suna na Fatima Iliyas ", murmushi ta mata sosai suka yi hira , a rana ta farko su ka shak'u ko da aka tashi , Halima taso su kai Fatima gida kasancewar yallab'ai Ahmad bai zo ba amma Fatima ta sanar mata yayanta zaizo d'aukarta, ilai kuwa suna tsaye ya k'araso sallama sukayi kowa ya nufi wajen Wanda yazo d'aukarsa , a hanya sosai Fatima ta saki jikinta da Ahmad ta dinga bashi labarin makarantar da sabuwar k'awarta da tayi, shi kuwa ba abinda yakeyi sai murmushi, " to kince zaki bani labarinki ko ba yanzu ba", " zan baka amma abinda zan iya cewa , akwai sark'ak'iya cikin labarina, ka bari in mun samu lokaci ba school, kazo ni kuma zan baka labarina ", murmushi ya sake yi , a daidai nan su ka k'arasa bakin gate d'in gidan , sun shiga cikin ko gama parkinga bai yi ba ta fita da gudu ta nufi falo da sallama ta k'arasa a lokacin shi kuma ya kunno kai , a cinyar hajiya ta zauna , "wash sai kin karyani , cewar hajiya da take k'ok'arin d'aga ta daga kan cinyarta ", shagwab'e fuska tayi ta turo d'an k'aramin bakinta waje , Ahmad dake tsaye zuba mata idanu yayi abin kawai ya burgeshi , lallai wannan yarinyar shagwab'ab'b'iya ce , hajiya ta mishi magana , firgigit ya dawo daga tunanin da ya tafi , gaisawa su ka k'arayi , a yayin da Fatima tace" mummy wallahi makarantar akwai dad'i sosai bari nayi wanka nazo na baki labari "," to kiyi Sauri ina jiranki, shi kuwa Ahmad rakata yayi da idanu har ta shige d'akinta.
Bayan tayi wanka tayi sallah ta fito ciki Riga doguwa sai siririn hannu , kalar ruwan hoda , rigar ba ta da nauyi , tayi parkinga gashinta da ribom shi ma pink , a kusa da mummy ta zauna ta shagwab'e fuska , ni kuwa nace su Fatima an samu abinda akeso ko da da kike hannu Inna Asabe anayi oho, " mummy yunwa nake ji wallahi", tashi maza kije kici abinci kinsan bana San kina zama da yunwa ", tashi tayi ta nufi dinning area , yayin da Ahmad ya rakata da idanu , ya rasa abinda ke faruwa dashi komai yarinyar tayi abun birgewa ne, " tana da kyau abinda yace kenan ya kautar da kansa gefe guda", da sauri ta nufi wajen zama ta zauna abinci taci sosai sannan ta koma su ka ci gaba da hira , Ahmad bashi ya bar gidan ba sai bayan sallar isha'i.

A b'angaren LAILA kuwa, sosai duniya ta dawo mata sabuwa, saboda sun shirya da Ahmad yadda ya kamata, kuma a nata tunanin ai Ahmad ya mayar da Fatima garinsu , batasan su na tare da mahaifiyarsa ba kasancewar ita d'in ba mai son zuwa gidan sirikarta ta bace ba, sosai hankalinta ya kwanta , takecin Karen ta babu babbaka , hmmmmm hajiya LAILA muje zuwa , mata a gidan Alhaji Ahmad.
Chapter 14 · 0% Book details