← Book details Kishiyar Uwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 26

Sashe 21

Kishiyar Uwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sun sauka lafiya , suna isa Ahmad ya kirayi wayar mutumin, ba'afi minti goma ba sai gashi ya k'araso, suka yi musabaha da Ahmad , ya gaisa da su mummy , sannan ya shiga mota domin yi musu jagora.

Sosai mummy ke kallon yadda garin ya sauya duk da ba wani dad'e wa tayi bata je ba, a k'ofar wani gida suka tsaya , mai kyau da tsari, ya sanar da su sun k'araso su fito , tabbas unguwar su Mummy ce Ahmad yq fad'a a ransa , ita ma Mummy abinda take fad'a kenan kuma ma ai k'ofar gidansu aka tsaya , jin k'ofar gidan ya tsaya yana nuna musu da su fito su shiga ga gidan nan da sauri Fatima ta k'arasa ta shiga ta bar su mummy a waje, mummy ce cike da al'ajabi ta kalli mutumin wanda sunanshi malam iro " kana nufin wannan gidan shine gidan kakanin Fatima, ta tambaya tana kallonsa", " k'warai kuwa hajiya", " toh ai nima gidan mu ne, kenan Fatima ta kasance y'ar Maimunatu kenan k'anwa a gurina", da sauri suka dubi hajiya , cikin zare idanu , sannan Ahmad yace.................

HMMMMMM YA KENAN FAN'S, IDAN HAR FATIMA TA KASANCE Y'A A GURIN HAJIYA YA MAKOMAR LAILA KENAN,?

SHIN KENAN DAMA MAHAIFIYAR FATIMA NA DA RAI?

Please
Share
&
Comments

To be continue................

🌿🌿🌿 NUSSAD🌿🌿🌿
🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸
(True life story)

🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸

SHAFI NA 37_38

Ahmad ne ya dubi mummy cike da mamaki , sannan yace"Mummy kina tunanin Fatima itace kenan y'ar gidan goggo na maimunatu, ya tambaya ya karewa Mummy kallo da sonjin abinda zai fito daga bakinta"," Ahmad ba zamu tabbatar ba , sai mun k'arasa daga ciki , ni kawai ina yawan ganin kamaninsu amma har yau ban tabbatar ba , yanzu dai kawai mu k'arasa zai fi mana da tsayuwar da muke yi " sannan suka juya domin k'ok'arin shiga gida.

A b'angaren Fatima kuwa , ko da ta shiga cikin gidan , ba kowa a tsakar gidan dan haka ta shiga k'wala sallama, wata y'ar dattijuwa ce ta fito ta amsa mata sallamar, a zuciyar Fatima kuwa jin ta take yi kamar a mafarki , lallai ta k'ara tabbatarwa da zuciyarta wad'annan ahlinta ne , saboda yadda take fusgar kama da ita, a wani b'angaren kuma tana mamakin yadda kamanin wannan dattijuwar ya kasance d'aya da Mummy , to ko dama anayin haka , tana cikin wannan zancen zucin su Mummy da Ahmad kai har ma da wanda ya musu rakiya, "ah maraba lale lale, mutanen kaduna kune da safe , sannunku da zuwa", dattijuwar ta f'ada , da sauri Ahmad ya k'arasa ya rungume kakarta sa, " kai ni sake ni karka karyani, na fasa yin auren da kai, tunda baka iya yin cefane ba " dariya suka sanya gabaki d'ayansu , cikin falon su ka shiga , sannan aka k'ara gaggaisawa, Mummy ce ke tambayar k'anwarta ta, Hajiyarsu tace mata ta shiga kasuwa, amma ba dadewa zata yi ba , taje yin cefane, da toh ta amsa tana addu'ar Allah ya sanya hasashen da ta dad'e tanayi ya kasance gaskiya amin, sosai suka yi hira , sai wajen karfe biyu sannan ta dawo daga kasuwar a gajiye, da sallama a bakinta , k'arasawa tayi k'ofar falon da sallama a bakinta, gabanta ne ya fad'i ganin yarinyar da tayi mai tsananin kama da ita, haka su ma mamaki ya kama su da ita kanta Fatima , to wacece wannan , mai kama da ita, zama tayi ta gaida su Mummy , Ahmad ya gaida ta, sannan Fatima wadda gabanta ke tsananta dukan uku uku, ita ma a b'angaren maimunatun haka ce ta kasance har yanayin muryarsu iri d'aya , sai dai ta Fatima akwai yarinta a cikinta, " yaya dama zaki zo, amma ko jiya munyi waya baki fad'a min ba , ta fad'a tana kallon yayarta ta", " wallahi k'anwa kinga wadda ta taso mu nan , ta nuna Fatima , dama ke muke jira , wani abin al'ajabi ne yake faruwa, kinsan wannan yarinyar, ta fad'a tana nuna Fatima " , girgiza kai tayi alamar a'a" zaki iya tuna d'iyar da kika haifa, wadda saboda bakin cikin abinda aka miki, baki k'ara ko da marmarin komawa garin da kika yi aure ba ballantana ki duba ta , kuma.......ai tun kafin Mummy ta k'arasa maganarta da take son yi , Maimunatu mahaifiyar Fatima ta taka har gaban Fatima ta daga ta , ta rungume tsam a jikinta, dama ba shakka wannan yarinyar tunda ta kalleta take jin wani abu a tattare da ita , dama ita ce d'iyarta mafi soyuwa a gare ta, dama tana raye to ta yaya su hajiya suka gano inda take , har su ka d'auko ta, hajiya ce ta katse mata tunani ta hanyar fad'in nasan kina da tarin tambayoyi a kanki toh yanzu kuwa zan warware miki komai", a b'angaren Fatima kuwa, wadda ke jikin mahaifiyarta ta lafe tana zubar da hawayen farin ciki da na tausayin rayuwarta a baya , dama mahaifiyarta tana raye, toh me yasa mahaifinta kafin ya rasu ya bayyana mata mahaifiyarta ta rasu, wani kuka ne ya kufce mata, bubbuga bayanta mahaifiyarta ta , ta shiga yi na tausayin tilon y'ar ta ta , sai da su ka tsagaita da kukan , sannan Mummy ta shiga bawa mahaifiyar Fatima labarin duk yadda akayi har Ahmad ya tsinci Fatima , da zamanta a wajenta , harda batun auren Fatima da Ahmad, sosai mahaifiyar Fatima tayi murna da jin haka, tayi farin ciki sosai da sosai ga yarinyar ta ta dawo bayan haka da auren wanda ya fi soyuwa a gare ta, sai da su ka gama koke kokensu sannan , su ka fara kiciniyar cin abinci, yayin da Fatima ta d'ora kanta a cinyar kakarta , kowa zuciyarsa wasai, a b'angaren Ahmad , shi yasan iya abinda yake kissimawa a ransa , sai dai kawai ya yi murmushi, a haka su ka fara cin abincin cike da walwala.

A b'angaren LAILA kuwa, tana zaune saurayin da tayi kwana biyu da su ka wuce ya kirata , d'an gidan wani shahararren mai kud'i ne ,kuma k'usa a gwamnati , mai suna Aareef ya kira ta, cikin yauk'i da nuna isa ta d'aga wayar , bayan sun gama hira ya fad'a mata yana so su had'u, dama ta gaji da zaman gidan , dan haka ta amsa masa da toh , ya fad'a mata inda zasu had'u , ta shirya , ta fita bayan ta sanarwa da kukunsu abinda zata dafa,shikenan abinda yake gaban LAILA a yanzu Allah ya kyauta amin.

ZARIA

Bayan sun gama cin abinci aka zauna hirar bayan saduwa, mahaifiyar Fatima ce ta shiga bawa Fatima labarin yadda al'amarin ya kasance, bayan ta baro gidansu Fatima da nufin zuwa gaida mahaifinta wanda bashi da lafiya.

ASALAIN YADDA ABUN YA FARU*

Bayan na baro gidanku, duk da a lokacin na so tafiya da ke amma a lokacin mahaifinki yana cikin halin asiri wanda innarki Asabe ke yi masa, sai ya hana ni tafiya da ke, saboda haka bada son raina ba na hak'ura, duk da nasan halin k'uncin da zaki shiga a hannun matar mahaifinki a lokacin kina da shekara d'aya a duniya, mun fara tafiya a hanya ,mun kusa isa zariya , bamu San yadda akayi ba , mu dai sai ganin wani bak'in hayak'i ya lullub'e motar daga baya kuma bansan me ya faru ba , sai a gadon asibiti , nayi jinya sosai kasancewar , ta samu karaya ba d'aya ba a jikina , hakan ya sanya na jima ina jinya, bayan na warke akayi niyyar mai dani, amma ni ko sunan garin aka ambata sai hankalina ya tashi , nayi kamar zanyi hauka , toh kinji dalilin da ya sanya ban k'ara ko da zuwa inda kike ba.

A nan ita ma Fatima ta shiga bawa labarin irin rayuwar da ta tsinci kanta a ciki ba mahaifiyarta ta ta ba , hatta Mummy da kakarta sai da su ka zubarda hawaye, na tausayin halin da Fatima ta tsinci kanta a ciki , babu abinda ya gigita mahaifiyar Fatima sai labarin rasuwar malam Iliya mahaifin Fatima, tayi kuma sosai , sai da aka bata baki da nasiha sannan ta hak'ura ta dangana, a nan suka tsayar da zasu yi sati a nan , zasu kuma su bar Fatima wayen mahaifiyarta ta yi wata , duk da Ahmad bai so watan ba amma yana ganin in yayi adalci gwara ya hak'ura , haka kuwa akayi sun gama kwanakinsu, suka bar Fatima kasancewar anyi hutu dama, sosai suka dinga zaga dangi da ita aka nuna mata duk wad'anda bata sani ba , anan take tabbatar da cewa ita d'in y'ar dangi ce.

A b'angaren LAILA kuwa rayuwa ta bud'e musu ita da Aareef su ke cin karensu babu babbaka, yanzu kam LAILA ta zama y'ar hannu ba inda bata zuwa, maza kowanne iri bi take yi , sai dai kawai mu mata addu'ar shiriya.

ZARIA

Sai da Fatima ta cika wata d'aya , sannan aka fara shirin komawarta bayan mahaifiyarta ta gyara ta sosai, domin Ahmad ya sanar mata bata tare a gidansa ba , ya fad'a mata duk yadda suka yi da Mummy, ta kira yayarta ta , ta rok'eta akan ta barwa d'anta matarsa, sosai ta mata magana ta yadda zata fuskanta, kuma ta amince da hakan , dama ita tunaninta a bari a samu dangin Fatima kuma an samu sannan dad'in dad'awa tayi hasashen akwai dangantaka da Fatima shiyasa, ko da aka sanarwa da Ahmad sosai yayi far in ciki, ya kuma shiga hidimar gyaran gidan da Fatima zata zauna kasancewar ba gida d'aya zasu zauna ba, hakan ne ya sanya Ahmad bai lura da halin da matarsa LAILA ke ciki ba , baya ma da lokacinta , harkar aikin gidan Fatima kawai yake yi.
Chapter 21 · 0% Book details