Sashe 19
Kishiyar Uwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mummy ce ta kalle shi had'i da fad'ar" lafiyarka kuwa Ahmad , wannan wacce iriyar magana kazomin da ita ne wai , ta fad'a tana kallonsa da son jin dalili", sunkuyar da kansa yayi k'asa ya kasa cewa komai , ganin haka ya sanya mummy sassauta murya saboda ta gane fushi yayi," haba son ta yaya za'ayi wannan d'anyen aiki baka ga abinda ya faru ba da matarka da daughter, son Fatima yarinya ce, bazata iya kishi da LAILA, kuma ko ba haka ba Fatima makaranta take zuwa , yanzu ta soma karatunta kana ganin in aka katse ta anyi mata adalci, tambaya tana jiran ya bata amsa"," Mummy ni dai kawai hakan nake so kuma bana San a d'auki lokaci mai tsawo nan da wani satin in Allah ya kaimu ya kama ranar juma'ah kenan", mummy ce ta dube shi , har cikin ransa da gaske yake ya sanya ta saukar da murya naji NA amince , amma da sharad'i za'ayi bikin amma nan da wata d'aya tunda ka matsu ayi a hakan", Fatima dake zaune jin abinda mummy ta fad'a sai da cikinta ya bada wata k'ara k'uuuuuuu , shikenan za'a kasheta da ranta ya zatayi kenan , kamata yayi ace tun kafin ayi auren nan ta samu ta fece, duk da son da mummy take mata ya kamata ace ta barta ko ba dan komai ba sai son tasan halin LAILA, a yanzu ma da ta gansu a tare ta fara sabauta mata rayuwa ballantana kuma ace ta auri mijinta ai shikenan kuma sai dai ta kai ta lafiya, tana cikin tunanin nan taji Mummy na kiran sunanta , cikin sanyin murya ta amsa. " ina fatan hukuncin da muka yanke yayi miki,mummy ta fad'a tana kallon Fatima da son jin me zata fad'a", Fatima tsintar kanta tayi da amincewa Mummy ba tare da ta San ta amince ba , murmushi mummy tayi , a gaskiya har cikin ranta ta aminta da Fatima , kuma tasan zata yiwa yaran d'anta tarbiyya, shi kuwa Ahmad da ke zaune sosai ya shagalta da kallon Fatima, sosai yarinyar take burgeshi, shi kad'ai sai kaga yana murmushi , mummy ce ta taimaka mata ta yi wanka ta gyara jikinta sosai a gurin cin abinci ne ta so tayi gardama , amma da Ahmad ya had'e fuska ya koma yallab'ai na asali, sai ta amsa ta fara ci sai da taji kamar zatayi amai sannan ta jijjiga kanta hakan ya sanya mummy ta k'yaleta, ganin da mummy tayi kamar Fatima na jin bacci ya sanya ta taimaka mata ta gyara kwanciyarta ba dad'ewa kuwa baccin ya kwasheta , su kuma suka ci gaba da tattaunawar bikin, nan Ahmad ya shaidawa hajiya ai LAILA tana gidansu , sosai ta nuna b'acin ranta akan haka , tace ya je ya taho da matarsa, ya fad'a mata bai ma San ta tafi ba jiya ne bai ganta a gida ba da ya koma , amma zai je ya dawo da ita, ya kuma sanarwa da hajiya Dan Allah ayi komai cikin sirri, wannan kenan.
A chan b'angaren LAILA kuwa , sun barbaje a falo ita da k'awayenta duniya ta koma mata sabuwa, ba abinda yake damunta, duk inda taga damar zuwa babu mai hana ta , hakan ya sanya take cin karenta babu babbaka, wata wadda suke kira da woman leader ce ta dubi LAILA a yatsine" wallah babbar hajiya kina bani mamaki , kamar ba LAILA ba, y'ar k'walisa, ki tsaya namiji yana b'ata miki rai, in nice ai wallahi sai na barshi , ko da shine autan maza"," ki kyaleta abinda nakeso ta gane kenan amma tak'i ta fuskanta , Aliya fire ta fad'a tana kallon LAILA", "yanzu toh me kuke son nayi , LAILA ta tambayi su Aliya fire, " ki rabu dashi kawai kizo a kwashi rabo da ke, Aliya ta kuma fad'a "," a'a inason mijina bazan rabu da shi ba gaskiya , amma nasan me zanyi ", Aliya naga ta tashi ta zagaya wajen LAILA ,suka gama maganganunsu ban dai san me ta fad'a mata ba , suka kwashe da dariya , su ka tafa harda woman leader, sannan su ka cigaba da hirarsu a haka mummyn LAILA ta sauko , aka cigaba da hirar da ita .
BAYAN SATI 1
Alhmadulillah, bikin Fatima yayi sauk'i sosai sai abinda baza'a rasa ba, zaune su ke, likita ya shigo ya duba ta , sannan ya sanarwa da mummy dama yana son sallamarsu ne tunda mai jiki Alhamdulillah ta warke, nan ya basu sallama , mummy ta kira Ahmad yazo ya d'auke su ya mayar da su gida , ko da suka koma sosai Fatima ta gasa jikinta da ruwan d'umi , tayi wanka , abinci taci kad'an sannan ta kwanta bacci kasancewar tana fashin sallah .
A chan falo kuwa Ahmad yana zaune da hajiya so yalr ya ga Fatima ta fito , shi ya sanya ya zauna suka ci gaba da hira da mummy, ganin babu niyyar fito wa kuma yana da aiki a office ya sanya ya hak'ura ya koma office ya ban mummy ita kad'ai a falon.
BAYAN SATI 2
Ahmad zaune yake a cikin office, wayarsa tayi k'ara , d'agawa yayi , ganin mai kiran ya sanya da kamar bazai d'aga ba amma sai ya danne ya d'aga, sallama yayi sannan ya gaishe da mai kiran , magana suka yi wadda bansan me suka ce ba , naji ya amsa da toh, sannan ya d'auki mukullin motarsa ya fita, sai da yayi tafiyar minti arba'in sannan ya k'arasa a bakin gate d'in ya faka motarsa , ya k'arasa ya k'wank'wasa, Baba mai gadi da yake zaune yana jin radio ya k'araso yana tambayar waye, jin muryar Ahmad ya sanya ya bud'e, gaisawa suka yi sannan ya masa alkhairin da ya saba yi masa sannan ya nufi cikin gidan .
Ko da ya k'arasa a bakin k'ofar falon ya tsaya , sallama yayi sannan aka bashi izinin shiga , a zaune ya samesu , su ukun , daga mummyn har daddyn sai kuma LAILA , gaishesu ya fara yi , cikin yatsina su ka amsa,cikin b'acin rai daddyn LAILA ya fara magana" ashe kai Ahmad mutumin banza ne , ka dakar min yarinya kuma ka korota gida, sannan kak'i zuwa ka bada hak'uri, toh ko mu zamu zo mu baka hak'urin, mummyn LAILA ce ta chafke maganar" Alhaji ai rik'a yayi shiyasa ya yi mana haka , wallahi kawai mun kai zuciya nesa ne bamu kai kararku kotu ba ", nan dai suka gama yi masa rashin mutunci, ko da ya sanar musu zai tafi da matarsa hanawa suka yi wai sai ta gama hutawa, haka ya tashi ranshi a b'ace ya nufi bakin gate domin tafiya , kome ya tuna kuma sai ya saki murmushi mai k'ayatarwa , sallama yayi wa Baba mai gadi sannan ya tafi office.
Bayan kamar kwana biyar da faruwar haka, Ahmad ya nufi gidansu , domin sanar da Mummy abinda ya faru kasancewar yana busy, ko da ya sanar mata addu'ah ta masa akan Allah ya sanya hakan mafi alkhairi ne , yaso yayi magana da Fatima amma kuma tun ranar da ya bayyana abinda ke ransa , suke wasan b'uya da ita , wani sa'ilin tana jin yazo zata gudu d'aki, ita dai Mummy abin har dariya yake bata.
Fatima ce zaune a d'akinta a lokacin saura kwana , goma d'aurin aure , sosai ta fad'a cikin kogon tunani , anya zata iya zaman gidan nan kuwa, me ya sanya ma ta amincewa Mummy akan maganar auren d'anta, saboda sunyi miki halacci a rayuwa, zuciyarta ta furta hakan, so da dama tana yin yunk'urin guduwa amma sai zuciyarta ta hana ta, ta so ta sanar da k'awarta amma tunawa da ta yi mummy ta gargad'eta da gayawa kowa ya sanya ta k'yale Halima, wayarta ce ta hau kuma sakamakon rurin da take yi , d'auka tayi ganin mai kiran sai da gabanta ya fad'i , cikin sanyin murya ta yi sallama, sai da ya ja ajiyar zuciya , har sai da taji , " Fatima me na miki ne irin haka, bakya so na ne kome, kinsan yadda kike a zuciya ta da har zakiyi min wannan horon, ya fad'a cike da sanyin murya ", ita ma kanta tasan zata kyautawa , amma ya zatayi ita gaskiya tana jin tsoro sosai, haka ya dinga janta da hira har ta saki jiki dashi , sukayi hira , sai da ya tabbatar da bata da damuwa sannan ya sanar mata da cewar za'a had'a mata kayan lefe zasu je ita da hajiya ta zab'i abinda takeso amsa masa tayi , sannan suka yi sallama.
Masha Allahu , a I gobe d'aurin aure mummy ta d'ibi akwatunan Fatima ta kai mata har cikin d'akinta , ta nuna mata ita dai Fatima duk kunya ta rife ta da k'yar ta gani sannan ta yi godiya , ko da dare yayi kasa bacci tayi har ladan yayi kiran sallah a kunnenta yayi , bata samu ko bacci d'aya ba saboda fargaba, a haka tayi wanka ta shirya cikin kayan da mummy ta d'inka ma ta , ta bi lafiyar gado ta kwanta saboda rashin baccin da ta samu ya sanya mata ciwon kai, aikuwa bacci ya kwasheta ba jimawa.
10:30am
Alhmadulillah, karfe goma da rabi amintattun hajiya mutum takwas wad'anda suka yi mata waliccin yaran na ta , su ka sheda d'aurin auren yaran na ta, Wanda wani amintaccen limami ya d'aura .
An daura auren Fatima Iliyasu da kuma Ahmad Muhammad Ahmad, akan sadaki naira dubu d'ari lakadan , sosai hajiya tayi musu alkhairi , bayan ta fad'a musu yadda angon ya tsara auren nashi , suka aminta da hakan sannan suka yi wa mummy sallama, su ka tafi.