← Book details Kishiyar Uwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 26

Sashe 10

Kishiyar Uwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A haka sukayi tafiyar kusan awa d'aya da rabi kafin nan su isa cikin garin zaria, bayan an karb'i kud'in motarsu , kafin nan suka k'arasa garin zaria, bayan an Shiga cikin tasha a lokacin kusan k'arfe ukun dare , mutane suna ta sauka daga motar yayin da Fatima tana chan ta shiga duniyar tunani bata ma san an k'arasa cikin tashar ba , direban ne yana k'ok'arin juya motar domin komawa ya k'ara d'ebo wasu fasinjojin , juyawar da zaiyi ya hangota a zaune tana tunani , "baiwar Allah direban ya fad'a ya d'an dukan saman kujerar" firgigit ta farko daga duniyar tunanin , sai a lokacin ta farga da cewar lallai fa sun isa garin zariya , " ki sauka anzo fa , ya fad'a had'e da nuna mata wajen da sauran mutanen suka fita, tsimmokaran kayanta ta d'iba sannan ta sauka daga motar , tana k'ara rik'e kayan nata, shi kuma direban ya juya da motar ta sa bayan ya sauke dukkan fasinjojin, domin komawa , sai a lokacin Fatima ta fara tunanin ina zata shiga , waye ta sani a garin zaria ita yanzu ya ya zatayi , sai a sannan ta ji tsoro ya kama ta , ga dare ya yi gashi cikin tasha ne ga mutanen da suka zo da su duk kowa ya kama gabansa , gefe ta koma ta zauna ta zubawa sarautar Allah idanu kafin gari ya waye tasan nayi , mutane taga suna gilmawa kamar walk'iya , tsoro ne ya kama ta , d'ago kanta tayi aikuwa taga sun yi mata rumfa , irin yan iskan cikin tasha ne , wani gabjeje ne ya yi magana cikin kakkausar murya , yana mai nuni da ita ," ke me kikeyi a nan ya fad'a yana k'walalo idanu " kakkarwa jikinta ya fara yi , tsoro sosai ya shige ta , " magana ake yi miki ba , wani ya fad'a daga cikin wad'annan y'an mutane , " kaga rik'emin ita kawai kagani babban nasu ya fad'a , chafka d'aya daga cikinsu ya kaimata da sauri ta zille ta fara ihu ga babu mai taimako, gudu take yi suna bin ta a baya har suka fita daga cikin tashar suna bin ta a baya, sosai takeyi gudu har ta hau kan babban titin garin basu daina bin ta ba, ga babu mutane sosai kowacce mota kawai wuce was takeyi , a lokacin Fatima ta gaji lik'is tana neman fad'uwa , tsautsayi ya sanya tana k'ok'arin tsallaka titi mota ta d'ebo da gudu aikuwa ta kwasheta , k'arar da ta saka ne ya sanya wad'annan mutanen suka juya da gudu suka koma idan suka fito , da sauri mai motar ya fito daga cikin motar ya k'arasa inda ya ga yarinyar a kwance hasbunallahu ya furta ganinta da yayi cikin jini ko motsi bata yi , a cikin zuciyarsa ya fara tunanin to me ya fito da wannan yarinyar cikin wannan daren ganin tunanin bazai kai masa ba ya sanya ya d'auke ta da Sauri ya nufi cikin mota da sauri gashi dare yayi a haka ya tada motarsa ya figa da gudu kasancewar yana Sauri ne dan haka madadin ya kaita asibiti kawai sai ya wuce da ita cikin garin Kaduna ya bar zariya da ita kasancewar gaba ki d'aya ya gama rud'ewa .
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Sai ana kiran sallar asubah sannan su ka k'arasa , asibitin cikin garin ya wuce da ita saboda yana da amini Dr Sadeeq, tun kafin su k'arasa ya sanar da shi halin da ake ciki, dan haka suna isa ya tarar da nurses suna jiran isowarsa ciki kuwa harda Dr Sadeeq din , da sauri aka d'orata akan gado aka shiga da ita cikin asibitin , shi kuwa mutumin da ya kad'eta kwata kwata ya rasa nutsuwarsa , ya kai ya kawo haka ya dinga yi " haba Ahmad kayi a hankali mana ko sai ka jawowa kanka wata matsalar , Dr sadeeq yayi furucin yana duban abokin nasa , " girgiza kai kawai Ahmad yayi saboda bayaso ya zama sanadiyar salwantar rayuwar wannan baiwar Allah , " bakasan me nake tsoro ba sadeeq , wlh ina cikin tashin hankali bansan me zanyi akai ba idan yarinyar nan ta rasa rayuwarta ta sanadiyya ta , Ahmad ya fad'a kamar zaiyi kuma , " d'aya daga cikin likitocin asibitin ne ya fito kasancewar Dr Sadeeq ya tsaya wajen abokin na sa domin kwantar masa da hankali ," a gaskiya yarinyar nan ta auna arzik'i amma mun samu ta farfad'o daga doguwar suman da tayi ,Dr Khalil ya fad'a yana duban Dr Sadeeq"," yawa Dr sannu da k'ok'ari min gode fa " , " ah ai babu komai ai maigida Ahmad ai namu ne Allah ya kiyaye gaba ", suka amsa da amin a tare , sai a lokacin ne Ahmad ya sauke nannauyar ajiyar zuciya , Dr Sadeeq ne ya dubi Ahmad , " am abokina ya akayi ne al'amari irin wannan ya faru" a take Ahmad ya bawa Dr Sadeeq labarin yadda abin ya faru tun daga farko , sannan ya k'ara da cewar hasalima ina sauri ne saboda laila na sanarda ita cewar zan dawo a yau daga kano shiyasa ", " amma baka tsammanin iyayen ta zasu nemeta , Dr Sadeeq ya fad'a yana duban Ahmad ," nima haka make ta tunani amma komai ma in ta farka zamuji" daga haka suka cigaba da hirar abinda ya faru.

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Sai da akay kiran sallah sannan suka tashi daga hirar suka nufi masallaci , domin yin sallah har suka dawo daga sallah Fatima bata farfad'o ba, dan haka Ahmad ya bar Fatima a hannun Dr Sadeeq ya nufi unguwarsu dake cikin wata GRA dake garin Kaduna.
🌹🌹🌸🌸🌹🌹🌸🌸🌹🌹

Tangamemen gate mai kalar ruwan madara masu gadin gidan su ka bud'e , hancin motarsa ya danna cikin gidan, ma'aikatan gidan sai kai kayo sukeyi , masu ban ruwa suna ta bawa furanne ruwa , duk inda ya gifta masu aiki na ta gaida shi yana amsawa cike da fara'a akan fuskarsa duk kuwa da cewar a zuciyarsa ba haka bane ba saboda yana tunanin me zai tarar a cikin gidan uwa uba kuma Fatima dake gadon asibiti.

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Shin wai meke faruwa ne a chan k'auyen Darki ne bayan Fatima ta baro 'yan biki da inna Asabe?

Ana ta aikin biki har safiya tayi , inna Asabe ta shiga cikin rububin mutane , hakan bai Sanya an farga da cewar amarya ta gudu ba har sai da hantsi ya fara fitowa ana ta shirye shiryen d'aurin aure ganin har wannan lokacin Fatima bata fito ba ya sanya inna Asabe ta aika Abu da ta kirawo mata Fatima domin ta shirya saboda an kusa fara d'aurin auren , a lokacin Abu nada juna biyu dan har ya fito sosai , lek'awa tayi cikin d'akin cike da gatsali " dalla chan ai saiki fito banza kin wani zo kin zauna a d'aki kin bar mutane , " shiru taji dan haka cike da bala'i ta chusa kai , wayam ta gani dan haka ta fito da gudu ta nufi d'akin inna Asabe..........

Please
Share
&
Comments

To be continue........
🌸🌸🌸🌸🌹🌹🌹🌹

🌿🌿🌿 NUSSAD🌿🌿🌿

🌸🌹 KISHIYAR UWA🌹🌸
(True life story)

🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
NA SADAUKAR DA LITTAFINA GA MASOYA LITTAFIN KISHIYAR UWA.

SHAFI NA 17_18

D'akin Inna Asabe ta nufa ko sallama babu," ! Inna , ta kwad'a mata kira da k'arfi , juyawa Asabe ta yi ," ke lafiya" , ta tambaya ta mik'ewa tsaye, " inna fa Fatiman ba ta nan fa" wani ihu inna Asabe ta zuba , tana duban mutanen d'akin da su ka zuba mata idanu, Abu fa kamar wasa k'aramar magana ta zama babba , tun kafin mutanen wajen y'an d'aurin aure su hallara ake nemanta duk inda aka san za'a ganta an nemeta amma shiru , nan fa aka ba za ma ko Allah zai sanya a ganta , amma shiru , lokacin da iyayen ango su ka zo aka Sanar da su , sosai hankalin ango ya tashi na b'atan amarya Fatima , aka yi nema aka gaji hakan ya sanya aka hak'ura da d'aurin auren aka ba ri sai an ganta tukunna , zancen fa ya cika k'auyen Darki na cewa Fatima ta gudu, wad'ansu na cewar dama bariki ta ke yi shi ya sanya zaman k'auyen ba zai yi mata ba dole ta shiga duniya , haka dai aka hak'ura duk da cewar y'an uwan marigayi malam Iliya sun koka na rashin Fatima amma suka hak'ura, wannan kenan.

KADUNA STATE
Chapter 10 · 0% Book details