Sashe 9
Jiddatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
sakko mata ta kasa ce ma Abban nata komai, amma taji hankalinta ya kwanta sosai, da kyar ya ci gaba "In sha Allahu wannan takadirin ba mijin ki bane Jiddah..." ta gyada masa kai tana gyara masa kwanciyar kansa, ya lumshe ido yace "Tashi ki je kiyi wanke wanken da ta sa ki kar ta dawo kin ji" Ta goge idonta cikin sanyin murya tace "To Abbana Allah ya baka lafiya" Yace "Ameen Jiddah" Mikewa tayi ta tafi gun uban kwanukan da Hansai ta tula bakin kwararo k'uda sai fareti suke a kai, sbda yawan kwanukan sai kusan la'asar ta gama ta mike ta dau buta ta xuba ruwa jin ana kiran sllh ta ajiye inda Abbanta ke alwala ta koma kusa da shi ta durkusa tace "Abba ka daure ka tashi kayi alwala" Jin yyi shiru ta kai hannu jikinsa tace "Abba la'asar yyi...." hannunsa taga ya xamo kasa daga jikinsa, ta kamo hannun tace "Abba...." Shiru bai amsa ba, komin bacci ko rashin lafiya shi din ba me nauyin bacci bane, hakan yasa ta sake kiransa nan ma shiru, jijjigasa tayi taga dayan hannun ma ya xame, bata san lkcn da ta kwala wani ihu da karfi ba kan kace me mutane suka shigo gidan da sauri jikinta na rawa tace "Ku taimakeni Abbana yaki tashi" Wani makocinsu wanda har da shi ya shigo ya kai hannu jikinsa lkci daya ya saki salati yace "Isuhu ai rai yyi halinsa" Daga wnn Jiddah bata sake jin komai ba ta dai bude ido ta ganta kwance saman tabarma dare yyi ga mutane cike tsakar gidan. Bayan kwana uku, Jiddah na xaune tsakar gida da idonta da yyi bulu bulu ga wani rama da tayi don har sannan bata iya cin komai, Hansai sai faman yankan awara take tana cewa "Ke kadai aka ma mutuwa idan ba munafurci ba, Ita Bibalo ba ubanta ne ya rasu ba halan, munafuka kawai me neman suna, kin taso kin fita da kayan awara bakin titi ko sai na taso na nakada maki shegen duka, idan bamu yi awara ba yau ubanki xa mu kwakulo a kabari mu ci?" Hawaye kawai Jiddah take ta mike ta dau kaskon awara da coal pot da wasu kananun kayan ta fita xuwa bakin titi, Hansai tace "Ni wllh idan ba binsa kabarin kika yi ba bansan kina yi ba, bayan mutuwan da yyi ya bar ni da wahalan yi maki kayan aure duk da dai katifa da robobin kitchen kadai Allah xai hore min inyi maki, to ince me wnn wahalan da ya bar ni da shi, ina ta sintirin xuwa gidan Saude xaman makoki miji ya rasu ashe nima nawa na kan hanya xai tafi ya bar ni da wahala, to banda dai dama ya gaji da duniyar daga tashin hawan jini sai mutuwa Allah na tuba, shi dai yaji da munafurcinsa kawai dama ya gaji da duniyar ne, to ba dai ya mutun ba dai ai shkkn, yanxu ga aurenki dake ta karatowa ya gudu ya bar ni da wahala" A haka jiddah ta dawo ta sameta tana ta kumfar baki ta dau robon awaran ta fita, har sannan jiddah taki dawowa dai dai, gani take kamar mafarki take xata farka taga Abbanta bai rasu ba, har yau da aka yi uku abincin kirki ta kasa ci, don ma Iyah na tsareta sai ta sha kunu, banda tsine ma Hansai babu abinda yan anguwan ke yi ganin Jiddah bakin titi tana tuyan awara, daga mutuwar miji da kwana uku har ta ci gaba da awaranta wnn wani irin xuciya gareta, yawanci duk Jiddah ake tausayi don shkkn ta xama marainiya gaba da baya yanxu.... Abuturrab na kallon Ramlah dake yankan ma Umma Fruits yace "Umma ta ci abinci kuwa?" Ramlah tace "Aa bata wani ci ba, Amma Aunty Zainab taje gida xata yi mata tuwo yanxu" Ummi dake xaune kan farin kujera a ward din tace "Ga farfesun hanta ma da nayi mata bata ci ba" Abuturrab ya kalli Umma dake kwance da drip a hannunta yace "Umma ko a siyo maki awara?" Ta d'an yi shiru kafin a hankali tace "Toh Allah ya sa in iya ci, bana jin dadin komai a bakina" Ummi tace "Toh wannan ai dole ne Ramlah... Kawai daurewa xaki yi kici ko kadan sai kiji jikin ya maki kwari" Abuturrab yace "Toh bari in je in siyo maki yanxu" Daga haka ya fita, Slowly yake driving din har ya karasa hayi, dai dai u turn din wajen ya juya ya nemi waje yyi parking yana kallonta ta glass din motar, kanta a kasa tana juya awaran cikin man kaskon a hankali, ya sauke glass din motar yace "Ki bani awaran dari biyar" Dago kai tayi tana kallonsa, kallon idanuwanta da suka kumbura yyi, bata ce komai ba ta saka masa awaran yanda yace snn ta mike ta isa gun motar tana mika masa ledan, bai amsa ba yace "Kukan me kika yi haka??" Ta sauke idonta kasa, lkci daya xuciyarta yayi mata rauni wasu sabbin hawayen suka cika idonta, da mamaki yake kallonta, bata san lkcn da ta fashe da kuka sosai ba tace "Abbana ne ya rasu" Daga nan kuma kamar warce aka tunxura ta jingina da motar ta dinga rera masa kuka, a hankali underneath his breathe yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Kuka kawai take so painfully, ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya ya bude motar ya sakko ya xagayo yace "Yaushe ya rasu?" Cikin kuka sosai tace "Yau aka yi uku" Da mamaki yace "Shine kika fito suyan wannan abun" Cikin rauni tace "Baabarmu ce tace sai na fito" Dauke kansa yyi, can yace "Awaran na nawa ne gaba daya?" Ta juya ta kalli roban awaran cikin shessheka tace, wai na dubu biyar tace min" Ya girgixa kai bai ce komai ba, can ya juya ya bude motarsa, kudin da ya ciro xa ayi masa delivering eye glasses da yyi ordering online ya dauko a motar, kamar wanda ya tuna wani abu ya fasa fito da kudin a haka sai da ya saka a wani ledan turare snn ya juyo yana kallonta, har sannan kuka take sosai, ya mika mata ledan kudin yace "Gashi ki kai mata kice ance kada ki sake fitowa sai an kwana biyu" Kallon ledan ta dinga yi da yyi mata dishi dishi sbda hawayen idonta ya kamo hannunta ya mika mata ledan ya amshi ledan awaran ya saka a mota yace "Allah ya gafarta masa" daga haka ya xaga ya shiga motarsa ya tada ya bar wajen, share hawayen idonta tayi ta leka ledan taga dari biyar sababbi dal a rafe, sosai gabanta ya fadi, ta kasa kwakkwaran motsi, wani almajiri ne yace "Awaran ki na konewa" Da sauri ta juya ta sauke awaran, ta xauna xuciyarta na bugawa da karfi, muryar Hansai taji a bayanta, Hansai ta ajiye bokitin wani awaran tana cewa "Ta dari biyar ce wnn, gaba daya ya kama dubu biyar da dari biyar...." ganin awara ya kone a mai tayi tsit tana xare ido, lkci daya ta saki salati da karfi tace "Na shiga uku awaran kika kona min Jiddah???" A mugun tsorace Jiddah ta mika mata ledan kudin tace "Baabarmu wllh wani ne ya xo ya kawo min wnn wai in kai maki kar mu sake fitowa sai bayan kwana biyu...." Hansai ta karbi ledan tana duba ciki da sauri, xaro ido tayi tana kallon tulin kudin cikin ledan, lkci daya ta dinga bin anguwan da kallo, murya can kasa tace "Daga ina yake?" Jiddah ta buda hannu har sannan jikinta na rawa tace "Wllh ban sani ba" Hansai tace "Dauko jarkar man da roban awaran mu wuce gida ai ya kare ma" A haka Jiddah ta kwashi kayan awaran ta bi bayan Hansai dake tafiya da sauri da sauri, A bakin kofar dakin Hansai Jiddah ta makale tana kallonta tana ta faman kirgan kudi duk ta hada xufa, har ta gama kirgen tana xaro ido tace "Dubu dari a wannan marran ni Hansatu, Allah yyi ma bawan Allahn nan albarka, yanda ya taimaki marayu Allah ya taimakesa haka shi ma, kaiii a duniyar nan ma dai xaman wasu toshe hanyar alkhairi kawai yake, banda haka daga rasuwan Isuhu kamar daga sama Allah ya jefo bawan Allah ya bamu dubu dari cif cif, yaushe rabon inga dubu ashirin da idona ni Hansatu" Jiddah dai ta sunkuyar da kanta xuciyarta na mata xafi bata ce komai ba, Hansai tace "Maxa ki sa ruwa kiyi wanka kema ko kya ji dadin jikin ki, kinga dai mutuwar nan alkhairi ne garemu sai kiga Allah yyi ta bude mana hanyoyi iri iri, aa ni dai wllh gwara da ya bamu hanya mu san me muke ciki a duniyar, to da ya baki kudin sai yace maki me?" Cikin sanyin murya tace "Yace kar in sake fitowa sae bayan kwana biyu" Hansai ta fashe da kuka tace "To dama banda talauci me xai sa mijina ya mutu in fara awara a ranan da aka yi sadakan uku, ai sai dai talaucin dama" Ta kara rushewa da kuka tana matsar kwalla da bakin xaninta, juyawa jiddah tayi a hankali ta bar bakin kofar tana dada jin mutuwar mahaifinta kamar a mafarki wanda hakan yasa hawaye kawowa idonta.