Sashe 46
Jiddatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
mata yace "Me xa ki ci nace?" Kasa cewa komai tayi, ya kalli waitress din ya umarceta da ta kawo mata exactly abinda ta kawo masa amma takeaway xata yi, waitress din na wucewa ya soma cin abincinsa, lkci lkci Jiddah ke satan kallonsa, cikin rashin sa'a suka hada ido, da sauri ta kauda kanta, shi dai ya ci gaba da cin abincinsa, Waitress din ta kawo abincin ya amsa ya ajiye kan table dinsa, sai da ya gama cin abincin sannan ya mike ya saka sauran drink din da bottle water a ledan abincin dake kan table din, cash ya ba waitress din har xai fara tafiya ganin jiddah bata taso ba yace "In xo in daga ki ne malama" Mikewa tayi xata wuce ya nuna mata ledan yace "ohk bar masu abincin xa ki yi" bata ce komai ba ta dauki ledan ta bi bayansa, suna isa gida da kansa ya dinga kwasan kayan yana kai wa parlor har ya gama, tana tsaye kamar wawuya bakin kofa sai dai ta basa hanya, har ya gama shigar da kayan yayi xamansa a parlor yyi powering Tv, jin bai ce ta shigo ba taki shigowa parlon, bayan kusan minti sha biyar ya mike ya isa bakin kofar yace "Ke wai baki da hankali ne dama ban sani ba? Meyasa kike behaving kamar yar kauye?? Yanxu me kike yi a nan a tsaye" Kamar xata yi kuka tace "Ai baka ce in shigo ba" Ya mata wani shegen kallo yace "Get out my frnd, sai nace ki shigo, idan kina son xaman lafiyar ki a gidan nan ki daina behaving kamar wawuya" Har hawaye ya kawo idonta ta bi ta gefensa ta shiga parlon, bata san dama kayan da ta bar sa da shi yake ta kwasa tana kallonsa ba ya basa haushi, tsaye tayi parlon tana tunanin ta wuce sama ko ta tsaya, ganin kallon da yake mata ta juya da sauri ta nufi sama, yace "Dawo nan" Dawowa tayi yace "Kwashi duk kayan nan ki wuce da su sama dakin ki" Daukan ledojin ta dinga yi daya bayan daya tana kai wa dakin nata har ta gama, ta dau na karshen xata wuce ya dawo da ita ya nuna mata ledan abincin durkusawa tayi ta dauka sannan ta wuce sama yace "Idan kin je saura ki ajiye abincin ki jirani in xo ince ki ci" Bata ce komai ba a sanyaye ta wuce sama ta shiga dakin ta kulle.