Sashe 19
Jiddatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ido tayi tana kallon uban kudin ciki, Jiddah dai na tsaye sai kallonta take ita ma, daki Hansai ta shige da gudu duk ta rude don yan dari biyar biyar ne kudin shi sa yayi yawa, Jiddah ta juya a hankali xata shiga dakinsu kenan aka shigo gidan babu ko sallama, Iliya ne da abokansa biyu kamar an hankadosu sai muxurai suke, ya nufi Jiddah yana huci ya fixgota ya xabga mata wani wawan mari cikin katon muryarsa yace "Uban wa ya sauke ki a mota yanxu?" Hansai na jin muryarsa tayin sauri cusa ledan kudin can karkashen jakarta tana salati ta fito da gudu, wani marin ya sake wanka mata ya hadata da bango ya lafto wani uban ashar yace "Da kudin nawa a kanki kike bin kartin alhazan nan suke yawo dake cikin gari, dama an gaya min ban yarda ba sai gashi yau na gani da idona, idan baki fada min waye shi ba al-qur'an sai na sumar da ke yau...." Yana fadin haka ya kara kai mata hauri ya shakota, ihu kawai jiddah take, Hansai da jikinta ya dau rawa tace "Ji mana Iliya, wllh wllh wani abokin uban gidan babansu ne jin xata yi aure ya tafi yi mata siyayya ya bada gudunmawarsa...." Wani wawan mari xai kai mata ta kauce da sauri ta bar wajen jikinta na rawa, kana ganinsa kasan a buge yake, Bibalo dai ta d'an windan dakinsu take leko su taki yarda ta fito bayan ta sakale dakin, Jiddah sai kichiniyar kwace kanta take amma ta kasa don ba rikon wasa yyi mata ba, Hansai ta nufi can bakin murhu jiki na rawa tace "Ka saurareni Iliya kada ka kashe min ita, wllh nace maka abokin wanda babansu yyi ma aiki ne a lkcn da yake raye, Jiddah ai ba haka take ba, jiddah kamilalla ce..." Sake Jiddah yayi ya juya yana kallon Hansai ya nufeta yana huci, wani ihu ta kwala tana cewa "Makota ku kawo mana dauki kar ya kashe mu...." Wani wawan naushi ya sauke mata a baki, tuni jiddah tayi waje a guje, daya daga abokan Iliya yace "Kai Iliya ta fice fahhh" iliya ya juya da sauri yace "Ku bi taaa" Duk suka fita da gudu, Iliya ya bi bayansu yana cewa daga nan kawai a kai min ita shagona, bikin banxa bikin hofi abinda har sadaki na biya naira duba sha uku, tinkiyar babata fa na dauke na siyar ko sani bata yi ba na biya sadakin, kawai a kai min amaryata..." Hansai dai tunda naushi ya sauka bakinta da ta fada cikin jerin bakaken tukwanen awaranta bata sake motsi ba sai 'yan idanuwa.... Jiddah na fita dama ta bayan layi ta xaga xuwa windon Iyah, a hankali ta dinga bubbuga windon jikinta na rawa tace "Iyah ni ce ki bude" Iyah tace "Aa ba ruwana an min iyaka da ke, ni da kika sa Hansai ta kusa cinna ma gidana wuta...." Wani ihu Jiddah ta fasa ganin Salmanu daya daga abokan Iliya, ya fixgo hannunta yace "Iliya gata na gano ta" Sai ga Iliya da gudu tare da Surajo, Iyah sai xare ido take jin ihun da jiddah ke yi, a haka Iliya ya ja ta xuwa adai daitan Surajo suka sa ta tsakiya Surajo ya hau adaidaitan ya tada, Iliya ya fiddo wukar aljihunsa yana nuna mata da jajayen idanuwansa yace "Al-qur'an idan baki rufan baki ba xan da6a maki wukar nan kowa ya huta" Tsit tayi jikinta na rawa hawaye na sauka idonta, can karshen kwalta suka kai ta, wani kuturun uncompleted house da Surajo ke ginawa, sbda rashin wajen kwana yake kwana a haka, Salmanu yace "Shikenan sai ku tare nan daren yau kafin gobe da safe Hansai taje tayi mata jere a shagon naka" Iliya yayi wani dariya ya sauka daga adaidaitan yana kallon Jiddah da ko kukan ta kasa sbda fargaba da shock, ya daure fuska yana kallonta da jajayen idonsa yace "Sauka mu shiga Amaryata ta kaina" Da kyar ta sauko daga adaidaitan ya tisa keyarta har cikin gidan wanda duk dogayen ciyayi ne, Surajo yace "To ko 'yar kifi da ruwan leda ba a siya mata ba ai" Iliya yace "Ai akwai wasu daren masu xuwa da yawa bayan wannan, idan bata ci yau ba xata ci gobe" Surajo yace "Da akwai lemo daya ma da na siyo da rana ban sha ba sai ka bata ta sha kawai" Dariya duk suka dinga kyalkyalewa da, Can jikin bango jiddah ta rakube kusa da yar katifar dake kwance a dakin da wani karamin fitila da bbu hasken kirki, ko siminti bbu a kasa, banda warin ta6a da wiwi bbu abinda dakin ke yi, ta runtse ido tana jin abubuwan kamar a mafarki, sallama su Surajo suka yi ma iliya suka fita dakin suna dariya suka yi masa sai da safe, Ya mike ya kulle kofar ya dawo ya xauna ya fiddo kwalin ta6arsa ya kunna ya fara xuka yana kallon Jiddah da ta takure ko ina na jikinta na rawa, yyi kasa da murya yace "Kiyi hakuri amaryata cikin bacin rai na bubbuge ki, raina ne ya baci ba kadan ba, kinsan idan raina ya baci bana ganin komai idona rufewa yake, har mutum ina iya kashewa, yo sau nawa ma aka yi hakan, kawai garbati ya ce min kusan kullum sai an xo an tafi dake an dawo a katuwar mota.... Shi ma shegen dake tafiya dake a motar ya ci sa'a bamu hadu ba wllh" Ita dai Jiddah bata ce komai ba jikinta sai bari yake, ya mike ya dawo kusa da ita ya xauna yana xukan hayakinsa yana murmushi ya rungumota kusa da shi, ta runtse ido xuciyarta na bugawa da sauri sauri, yace "Inji dai baki jin yunwa ko Amaryata?" Ta girgixa masa kai da sauri, ko kallonsa bata son yi kar ta saki ihun da take hadiyewa, ya wurgar da guntun taban hannunsa ya mike ya fara cire kayan jikinsa, Abuturrab ne ya fado mata, hawaye me xafi ya fara silalowa idonta, Bata san lkcn da ta fasa wani ihu a mugun tsorace ba ta rufe fuskarta da gwiwanta... Ya hade rai ya buga mata dundu a baya yace "Kee, ki kiyayeni fa, so kike ayi tunanin fyade xan maki bayan ke halaliya ta ce, dubu sha uku na biya jiya jiyan nan, har yanxu Babata bata san yanda aka yi da tinkiyarta ba, shine xaki kawo min iskanci, to idan xaki saki jiki ki saki, don muna nan da ke har sai an kira assalatu wllh...." Ta kallesa cikin dakiya amma muryarta na rawa tace "Fitsari xan yi" yyi murmushi yace "To ko ke fa, amaryata, ai gwara kawai ki saki jikin ki" Ya mike ya yace "Mu je in raka ki" Tashi yyi ya dagota xai cire Hijab din jikinta ta rike da sauri cikin rawar murya tace "Aa wllh sanyi nake ji" Bai saurareta ba ya cire Hijab din ya jefar kan gado ya nufi kofa ya bude yace "Mu je kiyi fitsarin" Ta bi sa da sauri jikinta na rawa, wani lungu ya nuna mata a jikin gidan, tun bata kai nan ba take jin zarni na tashi a wajen, yace "Kije kiyi ki dawo ki sha lemo kinji amarya" Ta gyada masa kai ta nufi wajen, komawa ciki yyi da sauri ya dau wandonsa ya laluba ciki ya fiddo wani karamin kwalba, sannan ya dau lemon coke dake ajiye a dakin ya bude, ya bude kwalban ya tsiyaya abinda ke ciki cikin lemon sannan ya rufe ya d'an jijjiga lemon ya sha kadan ya ajiye sauran, ya mayar da kwalban aljihunsa yana murmushi yace "Tass xa ki shanye lemon nan" xaunawa yyi gefen katifa yana jiranta, da sauri ya mike kamar wanda ya tuna abu ya nufi waje ya leka yace "Ke Jiddah, har yanxu baki yi fitsarin bane" A wangale ya ga d'an zinc din da aka yi kofa da shi na gidan, ya xaro ido ya fita da gudu yana kwala mata kira, gudu kawai Jiddah take wajajen da bbu kowa babu wasu gidaje sai ciyayi, sai da tayi gudu sosai taga wani me adaidaita ta tsayar da shi jikinta na rawa tace "Don girman Allah ka taimakeni wllh sato ni yayi, don Allah ka rufa min asiri ka taimakeni" Bata jira cewarsa ba ta shige adaidaitan don ya tsaya, shi ma mai adaidaitan duk a tsorace yake ya dinga gudu har suka shigo cikin mutane, har sannan Jiddah waige waige take gabanta na faduwa, sai da suka shigo hayi sosai sannan yace "Daga ina suka dauke ki?" Tace "Can cikin gari" Ya girgixa kai yace "Yanxu ina xa ki?" Shiru tayi don tasan tana komawa gida yanxu Iliya xai iya xuwa can gidan, da sauri tace "Cikin gari xan je don Allah" Dai dai kano road mai adaidaitan ya tsaya yace "To anguwan naku ba shi da sunana ne a cikin garin, ni fa nan ne iyakata?" Lkci daya hawaye ya kawo idonta ta bude tafin hannunta tana kallon takardan da Abuturrab ya bata daxu, har lkcn takardan na hannunta gam, ta kalli mai adaidaitan cikin sanyin murya tace "Don Allah kana da waya?" Yace "Ehh" tace "Toh ka taimaka ka kira min number nan don Allah" ya amshi takardan ya dau wayarsa ya kwashe lambar sannan yayi dialing, Abuturrab na xaune parlon Abbansa yana masa calculating din order din da Abban nasa yyi daga waje na kayan auren Ramlah wayarsa ya fara ring, Abba ya kallesa ganin ba daukan wayar xai yi ba yace "Pick ur call" hakan yasa Abuturrab ya dau wayar yana kallon number kafin ya daga ya kai kunne, Mai adaidaitan ya mika ma Jiddah wayar ta amsa ta kai kunne, calmly Abuturrab yace "Hello" Hawaye ya silalo idonta tace "Ni ce" Kallon Abbansa dake kallonsa yyi da sauri, sai kuma ya sauke kansa kasa yace "Ohk ina ji" Ta fashe da kuka sosai tace "Iliya ne ya xo ya daukeni wai saboda ya ganni a motarka...." Abuturrab ya dago da sauri yace "Xuwa ina?" Cikin kuka tace "Wai shi ba sai anyi biki ba tunda ya bada sadaki, nufinsa tarewa xan yi" Abuturrab ya saci kallon Abbansa ya rasa abinda xai ce, Abbansa dake lura da shi ya mike ya