Sashe 68
Jiddatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
na faduwa, yace "Ta ina kike fita har take ce maki yau baki fito ba?" Ta xaro ido tace "Ai kofar a rufe kake barinsa, ni bana fita ko ina, ban ta6a ganinta ba ni sai yau" kallonta kawai yake ta Sunkuyar da kanta, ya xauna saman kujera, ita dai bata yadda ta sake kallonsa ba, yace "Ina gyaran gashin da aka maki?" Cire Hijab din jikinta tayi sannan ta sauke hular tana kallonsa, da mamaki yace "Daga nan xan gani" A hankali ta duka kasa ta matsa kusa da kujeran da yake xaune ta juya masa kan nata, kallon bakin gashin dake ta sheki yake, yace "Ta haka xan ga gyaran an daure gashin?" Ta juya ta kallesa sannan ta xame ribbon din gashin ya sauka kasa, bayan few seconds jin bai ce komai ba ta juya ta kallesa suka hada ido, hade rai yyi yace "Tashi ki tafi" Tashi tayi ta mayar da hulan sannan ta wuce sama dakinta. Mikewa yayi ya dau makulli ya fita don xuwa can gida ya gaida su Ummi, Tana jin an bude gate ta mike ta isa bakin window ta tsaya tana lekan compound din har ya fita da mota, turo baki tayi ta koma bakin gado ta xauna, can ta kalli wrist dinta sai kuma ta mike ta fita dakin ta tafi can bangarensa da sauri, a hankali ta bude kofar parlon ta shiga ta karasa bedroom da sauri ta isa gaban madubin tana duba bracelet dinta bata gani ba, bin dakin ta shiga yi da kallo bata ga alamarsa, juyawa tayi ta fita ta koma dakinta ta kulle kofa ta kwanta. Da daddare Abuturrab na bedroom dinsa yana operating laptop wayarsa ya fara ring, dauka yyi ganin me kiransa ya katse ya kirata, daga daya bangaren tace "Hi ya Abuu, Grandma want to vid call with u, na kira naga baka online" Yace "Ohk, how about zoom?" Tace "Aa ta WhatsApp dai" katse wayar yyi ya bude datansa ya hau online sannan ya kirata vid call din, Hajja ta hakikance gaban screen da katon eye glass dinta, yyi dariya yace "Ina wuni Hajja" Tace "Aa ba ruwana, meye kuma ina wuni, kai baka kiran mutane sai dai a kiraka kawai don kana matukin jirgin sama, baka da wani bambanci fa da me jan motar haya wllh, naga kamar wani jin kanka kake, ga Saleem kullum sai ya kira Farida ya ga fuskata, haka ma Bashir, ko daxu sai da Bashir ya kira muka ga fuskar juna, to kawai don bana kasar sai kayi watsi da ni, sai kace ba ni nayi wahala da kai ba, ko uwarka ce tace ka fita harkata, don dai har yau bamu san xuciyar matar nan ba" Abuturrab na shafa kansa yana murmushi yace "Ya gidan Hajja" Tace "To lafiya lau, ai naji Baban farida xai taho Nigeria ni dai nace tare xa mu taho don na gaji, babu wani abinci a nan banda gurasar alkama, to ina dalili duk na kanjale na xata wajen arxiki ne ashe ba haka ba, basu da komai sai alkama da madara" Abuturrab yace "Yaushe xa ku taho kenan?" Tace "Aa ni dai kawai ji nayi xai taho, amma ban san yaushe ba" Yace "Toh Allah ya kai mu" Tace "Kana nan kana tukin jirgin har yanxu dai ko? Don duk na sanar ma abokan arxiki da nayi a kasar nan cewar jikana tukin jirgin sama yake, bbu kamarsa duk Nigeria" Abuturrab yyi murmushi kawai, tace "Aa ba batun murmushi ba, ko sun koreka a aikin ne nake nan nake ta tsuga karya?" Yace "Ke fata kike a koreni" kiran Aneesah ne ya shigo wayar, hkn yasa vid call din yyi still, ya daga kiran, daga daya bangaren cike da fara'a Aneesah tace "Guess what My captain?" Ya jawo pillow ya kwanta ya lumshe ido cikin calm voice dinsa yace "I am not a good guesser u know...."