Sashe 25
Jiddatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washegari da asuba bayan an idar da sllh Ahmad ya fito rike da karamar jakarsa, dakin Ummansa ya shiga ya gaisheta tace "Da asuba xaka tafi Ahmad?" Yace "Ehh kar nayi missing train din ne" Umma tace "To kun yi da drivern ya xo da asuba ne ko wa xai kai ka train station din??" Yace "Aa Abuturrab xai kai ni" Umma tace "Abuturrab kuma? yana garin ne? Lafiya bai koma aiki ba" Ahmad yace "Ehh satin nan yana nan yace min" Umma tace "Toh Allah ya tsare, kayi addu'a dai" Yace "Ameen Umma, in sha Allah" Har ya kai kofa tace "Har xaka tafi gashi ka mance da drugs din nawa" Juyowa yayi da sauri yace "Oops, kiyi hakuri Umma Abuturrab xai kawo maki anjima in sha Allah" Tace "Toh Allah ya kai mu, Allah ya kiyaye hanya" sallama ya kara mata ya fita dakin, yana fita compound ya dau wayarsa ya shiga kiran Abuturrab, Abuturrab ya daga yace "Gani na shigo layin yanxu" Ahmad yace "Alright" Sai da suka yi nisa Abuturrab ya d'an kalli Ahmad yace "Medical report din da nace xaka min din fa?" Ahmad yace "Idan aka yi how will it reach you?" Abuturrab yace "The plane coming from Abuja to kano, xan yi ma pilot din magana abokina ne, sai ku hadu ka basa" Ahmad yace "Flight din karfe nawa ne?" Abuturrab yace "karfe uku" Ahmad ya tabe baki, Can ya kalli Abuturrab yace "Toh wai ma me ya hanaka komawa gun aiki kake neman medical report din karya Captain?" Abuturrab yace "That is none of ur interest, kai dai kawai kayi min medical report" Ahmad yace "Toh baxa ayi ba" Abuturrab bai kuma ce masa komai ba har suka iso Station din, Ahmad yace "Yauwa pls captain i will text some drugs now to you, na umma ne, xaka siya ka kai mata, i forgot to do so yesterday" Abuturrab yace "A hakan xan siya magani in kai mata? Kana ganin babu kaya jikina" Ahmad ya kallesa, Jallabiya ce milk color jikinsa, Ahmad yace "Shi kuma wannan bargo ne a jikinka kenan, beside ni bance da safe ba, wani pharmacy xaka samu a bude this early, kaga dole dai sai anjima" bude motar Ahmad yyi ya sauka yace "Thank you" Daga haka ya rufe motar ya shiga cikin tashan, Abuturrab ya bi sa da wani irin kallo, bayan few minutes ya ja motarsa ya bar wajen, Abuturrab ya na isa gida text din Ahmad na drugs din ya shigo, lkci daya alert din kudin drugs din ma ya shigo, tsaki Abuturrab yayi ya cire jallabiyan jikinsa ya shiga bathroom. Karfe goma saura Abuturrab ya fito dakinsa, bangaren step mum dinsa ya fara shiga ya gaisheta, tana gyara press dinta tace "Ina xuwa da sassafen nan haka, kai da nake tunanin ka dau hutu ne don ka huta" Yace "Xan je siya ma Umma drugs dinta ne" tace "Tohhh, Ahmad din fa?" Yace "Ya koma gun aiki" Tace "Toh nima ka siyo min Panadol night..." Yyi murmushi yace "Toh in sha Allah" Ya juya xai fita tace "Captain shiru shiru kuma baka turo abun ba, kada a siye wajen ne fa" Yace "Ehh ina son in sanar ma Ummi ne...." Da sauri tace "Sai ka sanar mata captain? Ina ce yanda ka dauketa haka ka daukeni?" Ya d'an yi shiru, sai kuma yyi murmushi yace "Toh nawa ne kika ce?" Tace "1.7m" yace "Toh xan tura in sha Allah" Tace "Yauwa ko kai fa, idan ka dawo anjima ka shigo da akwai wata maganan kuma" Yace "In sha Allah" daga haka ya fita, bangaren Ummi ya shiga, waya ne kare kunnenta, hakan yasa ya jingina da kofa ya jira har ta gama sannan ya risina ya gaisheta, tace "Lafiya lau..." yace "Jiya na shigo kin yi bacci" Tace "Ehh da wuri na kwanta" Yace "Ohk, sai na dawo" Daga haka ya fita dakin ta bi sa da ido. Abuturrab na shiga mota yayi ma Ahmad transfer din kudin da ya turo masa, sannan ya nufi wani babban pharmacy, ya siya duk drugs din, bai mance na Stepmum dinsa ba, ita ma ya siya mata pack har uku na drug din da tace sannan ya dau hanyar gidansu Ahmad, Sallama yyi bakin kofar parlon aka amsa masa sannan ya shiga, Umma na xaune parlon da Maman Abdallah dake xaune kasa Jiddah na gefenta alamar gaisheta suka shigo yi, daga kai Jiddah tayi suka hada ido da shi ta sunkuyar da kanta, karasowa cikin parlon yyi ya xauna yace "Ina kwana Umma" tace "Lafiya lau Aliyu, ashe kana garin" Kallonsa Jiddah tayi jin sunansa a karo na farko, ya shafa kai yace "Ehh ina nan Umma, ya karfin jiki?" Tace "Ah Alhmdlh sauki ya samu" Mikewa yayi ya karasa kusa da ita ya ajiye mata ledan maganin hannunsa yace "Ga drugs din naki Umma" tace "Toh nagode son, Allah yayi albarka" komawa yayi ya xauna yace "Ameen" tace "Ya su yaya?" Yace "Suna lafiya..." Tace "Toh a kawo maka breakfast?" Tana fadin haka ta mike, yace "Aa umma nayi breakfast a gida" Umma tace "Toh ga awara da Maman Abdallah da mai sunan yaya suka yi da safe, u will like it" Ya d'an kalli Jiddah da kanta ke kasa, Umma ta mike ta nufi kitchen, Abuturrab ya girgixa kai da sauri xai yi magana sai kuma yyi shiru ya sauke boyayyen ajiyar xuciya, Maman Abdallah na kallonsa da fara'a tace "Ina kwama abokin Dakta" Babu yabo babu fallasa yace "Lfya lau" Jiddah bata dago ba ita ma tace "Ina kwana" yace "Lafiya lau" Umma ta fito kitchen, sai ga mai aiki rike da karamin tray me dauke da awara da sauce da pepper soup din naman rago a rufe a wani warmer din, dinning ta kai ta ajiye, Umma na kallon Abuturrab tace "Gashi can a dining area son" Ya d'an yi murmushi yace "Nagode Umma" Tace "Ko a kawo maka nan?" Ya bi dining area din da kallo sannan yace "Ohk" Nan kusa da shi mai aikin ta kawo ta ajiye sannan ta wuce, Maman Abdallah ta mike cike da ladabi tace "To Hajiya xata maki gyaran ne yanxu??" Umma tace "Eh to, ko kuma ta bari gobe ai tana nan, ko ba kwana biyu ta xo yi maki ba?" Maman Abdallah tace "Tana nan tukun wllh Hajiya, don bata ma sa ranan tafiya ba" Umma tace "Toh shkkn gobe sai tayi min gyaran" Maman Abdallah tace "Toh shkkn Allah ya kai mu Hajiya" Mikewa tayi tana kallon Jiddah tace "Toh mu je gobe sai kiyi aikin ko" Umma tace "To ki bar ta tayi kallo mana, tunda ke ba kallo kike ba" Maman Abdallah tayi dariya tace "Ehh kuma haka ne, tunda xan je maki kasuwa yanxu, ina fita hijabi kawai xan sa in tafi dama" Umma tace "Toh ki bar mata Abdallah ko baxai xauna ba" Maman Abdallah tace "Baxai xauna ba Hajiya, kiwuya ya gallabesa ai" Umma tayi murmushi tace "Toh sai kun dawo" Ko kadan Jiddah bata so haka ba duk da ba wai tana da niyyar bin ta kasuwan bane saboda tsoron kada wani da ya santa ya ganta a hanya amma xaman parlon ma bata so, Umma na lura da ita taga alamar she isn't comfortable, hakan yasa tace "Ko kuma ku tafi kasuwan kawai tare kada ta xauna shiru" Maman Abdallah da har ta nufi kofa tace "Dama tare nayi niyyar xa mu je, da kika ce ta xauna tayi kallo ne yasa nima nace ta xauna Hajiya" Sosai gaban Jiddah ya fadi, Maman Abdallah tace "Toh taso mu tafi kasuwan" Abuturrab dake xaune parlon yana sauraronsu yace "Tunda kallo take yi ki bar ta tayi kallonta mana" Kallonsa Umma tayi da mamaki, that's very odd of him, shi mutanen cikin gida ma baya shiga sabgarsu yayi masu magana balle wanda bai hada komai da su ba, Jiddah ta dago kanta amma bata ce komai ba, Umma ta d'an yi murmushi tace "Toh tayi xamanta" Maman Abdallah ta fita parlon bayan ta ce ma Umma sai ta dawo, Mikewa Umma tayi ta tafi kitchen sae gata ta dawo da karamin flask da mug ta ajiye ma Abuturrab tace "Kilan ta manta ne bata kawo maka ba..." yayi murmushi yace "Nagode Umma" Tace "Kana son madara?" Ya girgixa mata kai, tace "Yauwa nayi tunanin hakan, Ahmad ma bai fiye shan madaran ba" Sama ta nufa tace "If u are done ina daki" Yace "Alright" Bayan few minutes da tafiyarta ya daga kai ya kalli Jiddah, kanta na kasa tana wasa da hijab din jikinta maimakon kallon da aka barta tayi a parlon, ya bude flask din gabansa ya xuba ruwan Lipton cikin mug, wanda ya xuba ko rabin mug din bai yi ba, sae kamshi ruwan shayin ke yi, Calmly yace "Baki da wani damuwa a inda kike?" Ta dago ta kallesa sannan ta girgixa kai, bayan few seconds a hankali tace "Sai dai Baabarmu xa tayi ta nemana a gida" Kallonta yayi a takaice yace "Toh a mayar da ke wajenta kenan?" Shiru tayi tana kallonsa, can ta sauke idonta cikin sanyin murya tace "Iliyan xai iya sake biyo ni, ita ma xata iya kai ni wajensa" Abuturrab ya hade rai yace "Shine kuma xaki ce min Baabarki xata nemeki?" Bata ce komai ba, ya fara shan shayin hannunsa a hankali, tv ya dinga kallo kafin murya can kasa yace "Amma idan aka sauya maki shi wanda xai aureki yanxu da wani daban xaki amince da auren?" Kallonsa take babu ko kiftawa, yace "Ko baxa ki amince ba?" a sanyaye tace "Toh ai ban san waye shi ba" yace "Toh ni nasan sa" Tace "Toh in dai baya shaye shaye" Ya dinga kallonta sannan yace "Kina dai son kiyi aure kenan dama?" Hawaye ne ya kawo idonta tace "Baabarmu ce ke son inyi auren, kuma ai ba makaranta nake xuwa ba kawai sana'a muke yi" Bai kuma ce mata komai ba ya ci gaba da shan shayinsa, ta goge hawayen idonta, ya d'an kalleta yace "Wanda xan hada ku baya shaye shaye" A hankali tace "Toh" bude warmer din awaran yayi yana kallo yana d'an yatsine fuska, sai kuma ya bude na pepper soup dinma, lkci daya