← Book details Jiddatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 109

Sashe 79

Jiddatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abuturrab na dawowa masallaci ya ga kiran Ahmad a wayarsa, ya xauna sannan ya kuma dialing number sa ya kai kunne, daga daya bangaren Ahmad ya daga yace "Ya kwana biyu?" Abuturrab ya shafa kansa ya mike ya koma dakinsa, a hankali yace "Alhmdlh, how is work?" Ahmad yace "Alhmdlh, baka yi piloting xuwa Abuja bane yau" Abuturrab yace "Ina Abuja" Ahmad yace "Alright, ya na ji ka so calm dude?" Abuturrab bai ce masa komai ba, Ahmad yace "Xan shigo after isha" Abuturrab yayi kasa da murya yace "Ka taho da paracetamol or any pain reliever" Ahmad yace "Ko har Aneesar ta je ne?" Abuturrab ya katse wayar, ya ajiye yana tunanin where he is going to start from, sure yasan yana son Aneesah sosai baya son komai da xai bata mata rai, But why did all this happen, why did things turn out this way.... Shafa kansa kawai yayi knowing the only way out now shine ya tura gidansu in few days time, wayarsa ya sake dauka har xai yi dialing numberta ya fasa. Abuturrab na xaune parlor bayan ya dawo isha yana jiran xuwan Ahmad, karfe takwas da few minutes Ahmad ya danna bell, ya mike ya bude masa kofa, Ahmad ya shigo parlon, xaunawa yayi saman kujera yace "After leaving me all my self with my wedding preparation, still u have d gut not to ask how everything is going.... right?" Abuturrab yace "Ohk ka fara shirye shirye ne?? Sure juma'ahn sama ne koh? I'm sorry na manta wllh, what are u up to now? Kasan ba haduwa muke yanxu a kadunan ba kamar da" Ahmad yyi dariya yace "Ya xa mu hadu kuwa, tunda ga ka ga amaryar ka Jiddah" Abuturrab ya tsura masa ido, can yace "Is there anything i will gain idan na maka karya Ahmad?? But don Allah ka gaya min me yasa kake ganin har ynxu matata ce ita?" Ahmad yace "Toh gashi nan ba sai na fada ba, da fa duk na shigo kd sai mun hadu, infact kai ma kake xuwa gidanmu ynxu kuwa kana gidanka, idan ba wanda yyi sabon aure ba, giyan auren na dibarsa waye ke yin haka??" Abuturrab yace "Ka dai jira xanyi auren kwanan nan sae kaji dadin fadin duk abinda ke ranka, amma yanxu kam i am a bachelor just as u, sae sabon title da na samar ma kaina na xama Uba, i am more like a father or guardian now" Ahmad yyi murmushi yace "Toh ka bani ita inyi ta biyu da ita Captain" Abuturrab ya kallesa, kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Are you for real?" Ahmad yace "I'm serious wllh in dai Umma xata yrda i will" Abuturrab yace "Ohk, but.... How are we going to open up all this to our parent? Kasan dai ynxu banda Aunty da kai, sai ita yarinyar babu wanda yasan babu auren nan" Ahmad yace "We will cross the bridge when we reach there, yanxu dai ka amince min kai?" Calmly Abuturrab yace "In da gaske kake na amince, nima burden xai sauka kaina, if not for her da banyi making mistake da nayi daxu ba" Ahmad yace "Wani mistake?" Abuturrab ya dau remote din TV yana canxa channel yace "Ba ruwan ka" Ahmad yyi murmushi yace "Everything is settled now tunda ka amince" Kafin karfe tara Jiddah tayi bacci bayan tayi wanka, Hijab din Aneesah dake gidan ya bata tayi sllh tun magrib. Abuturrab na xaune har sannan a parlor tare da Ahmad sae dai hankalin sa baya tare da Ahmad, bai yi tunanin Ahmad xai kai har 10 a gidan ba, Can dai Abuturrab yace "Wai kana kallon agogo kuwa?" Ahmad yace "Ohh ta kusa xuwa kenan, anyway ko baka fada ba dama yanxu xan wuce sai da safe" Daga haka ya mike ya nufi kofa Abuturrab ya bi sa da kallo, mikewa yyi ya bi bayansa yace "Ka ajiye ni eatry let me get something to eat" A tare suka fita gidan, sai kusan karfe goma da rabi Abuturrab ya dawo, yana shigowa parlor ya kulle gidan sannan ya wuce dakin da Jiddah take, tayi nisa baccinta, Ya ajiye ledan abincin ya nufi gadon, buga gadon yayi ko motsawa bata yi ba, yayi hakan ya kai sau uku ganin bata tashi ba ya dau bottle water ya bude, sai kuma ya fasa xuba mata ruwan ya ajiye sannan ya kai hannu kafarta yana tashinta, bude ido tayi a hankali, yace "Tashi ki ci abinci" Ta girgixa masa kai tace "Na koshi" Yace "C'mon tashi nace" Mikewa xaune tayi da kyar tana kallonsa da idanuwan bacci tace "Na koshi" Ya hade rai yace "Sakko nace" Xamowa tayi ta sauka kasa tana lullumshe ido, ya bude mata tuwo da veg soup din, ta tashi tana rurrufe ido yace "Ina xa ki?" Tace "Xan wanke hannu" Bai ce komai ba ta tafi ta wanke hannun ta dawo, tun da ta fito yake kallonta, Kana ganin yanda Hijab din yayi a jikinta xaka kasan bata saka komai ba a ciki, dama kuma hijab din har kasa yake ja mata, xaunawa tayi ta jiginar da kanta jikin gadon ta lumshe ido, buga gadon yayi ta bude ido da sauri ta kalli abincin gabanta sannan ta kai hannu ta fara ci a hankali, juyawa yayi ya fita dakin.... Washegari da safe Abuturrab ya fita yayi mata shopping din few clothes, karfe goma kuma ya nufi airport tare da ita, babu abinda ya sanyaya masa jiki sai yanda kiran Aunty ya dinga shigowa wayarsa babu kakkautawa, shi kuma yaki dagawa, Jiddah na ganin inda suka xo hankalinta ya tashi, marairaice masa tayi tace "Ni fa bana son hawan jirgin wllh" Yana kallonta yace "Sai me xa ki hau?" Tace "Motar" Wani kallo yayi mata yace "Sai ki hau motar inda kika gansa ai" Lkci daya hawaye ya kawo idonta bata kuma ce masa komai ba, tun bata kai ga shiga jirgin ba taji kanta ya fara juya mata, Tana rike da wayansa da ya bata ta nemi kujera ta xauna a business class, sai waige waigen inda xata gansa ta mika masa wayar take, to ina shi yake xama ne a cikin jirgin, tunawa tayi a inda ta gansa jiya bayan jirgi ya sauka, and she assumed a wajen yake xama shi, jin taku a gefenta Jiddah ta juya, buda ido tayi sosai ganin wanda suka shiga jirgi tare da shi a rana na farko, seat dinsa ya nufa ya ajiye karamin jakar hannunsa a sama sannan ya xauna, da sauri ta dauke kanta gabanta na faduwa, wata mata ce ta xauna kusa da ita tayi mata sannu, murmushi kawai Jiddah ta mata tana juya wayar Abuturrab dake hannunta, bayan wani lkci jirgin ya tashi, suna keta hazo ta cire seat belt dinta da sauri ta mike bayan ta ajiye wayar Abuturrab, hanyar lavatory ta nufa sai a sannan Yousuf ya ganta ya bi ta da kallon mamaki, ba a dau lkci ba ta fito, matar dake kusa da ita tace "Did u feel nauseous?" Jidderh tayi mata murmushin karfin hali ta xauna, Ta d'an saci kallon Side din da Yousuf yake suka hada ido, sunkuyar da kanta tayi, throughout the short journey to kano bacci tayi a jirgin, snacks da aka kawo mata ma bata ci ba, Matar dake gefenta tayi tapping dinta tace "Ki saka seat belt dinki" Bude ido Jiddah tayi ta fara saka seat belt din, runtse ido tayi da jirgin ya fara sauka bayan ya samu izinin yin hakan, matar da ta lura she is very uncomfortable ta riketa, tace "It's just for a few seconds, sorry dear" Jiddah bata ce mata komai ba har jirgin ya sauka, rufe bakinta tayi kar ma tayi ihu, matar na Kallonta tana murmushi tace "it's all over" A hankali Jiddah ta cire seat belt din, bayan da jirgin ya tsaya ta mike ta dau hand bag dinta ta fara fita kamar yanda ta ga sauran nayi, da kallon mamaki matar ta bi ta, tana mamakin to ko kurma ce dai, Yousuf ya mike ya dau jakarsa ya bi bayanta da sauri, a hankali take sauka daga matakalan jirgin iska me sanyi na kadawa a filin airport din, tana sauka kasa kamar ance ta juya taga Yousuf yana saukowa shi ma, murmushi ya sakar mata har ya iso inda take yace "Jiddahh" Ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, mika mata hannunsa yayi yace "Bani wayar taki in sa maki number na tunda Allah ya sa kin taho da shi yau" Ta buda ido sosai tace "Ba wayata bane, na yayana ne" Da mamaki yake kallonta yace "Yayanki? Yana ina?" Ta kalli cikin jirgin tace "Kaman yana ciki, ni dai ban gansa ba" Yace "Ina ku ke xuwa tare da shi ko da yaushe a jirgi?" Tace "Nima dai ban sani ba" Yace "Baki sani ba kamar ya?" Tace "Allah ban sani ba ne" Yayi shiru yana kallonta walking slowly together with her, can yace "Me ku ka je yi a Lagos?" Ta kallesa da sauri tace "Lagos?" Yace "Ehh" Tace "Nan ne Lagos din don Allah?" He couldn't help it but left his mouth agape yana kallonta with surprise, ta dauke kanta tana ci gaba da tafiya yace "Wait Jiddah, are you kidding me, or you just don't want to give me an answer" Bata ce komai ba, calmly yace "I am talking Jiddah..." Tsayawa tayi tana kallonsa tace "Ni fa ba wani turanci nake ji ba" Sake baki ya kuma yi yana kallonta, bai san lkcn da yace karya kike.... Tace "Wllh ba karya nake maka ba" Sincerely ta fadi hakan, ya shafa kansa yana sake kallonta daga sama har kasa yana naxarin abinda tace wai bata jin turanci, but how?? tsadadden abaya ce jikinta blue da ya mugun haskata, ko kwalli babu a idonta, wanda kuma bai kalli lips dinta da kyau ba, sai yayi assuming pink lip gloss ta saka coz after being pinkish har sheki lips din nata yake, ga manyan idanuwanta farare tasss kamar madara, hancinta kuwa have the perfect shape a nose should have snn ga tsayi, ya d'an mata murmushi yace "Na yarda Jiddah, yanxu ina xa ki?" Tace "Nima ban sani ba yayana nake
Chapter 79 · 0% Book details