← Book details Jiddatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 109

Sashe 73

Jiddatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe biyu saura Jiddah ta sauko parlor sbda yunwan da taji take ji, tun bayan tafiyar su Aunty Abuturrab ya sa ma gidan makulli ya koma parlon bangarensa, wayarsa dake saman center table ne ta ji yana vibrate, kallon wayar ta dinga yi sannan ta karasa ta duka ta dauka tana kallon screen din, Cikin few seconds tayi kokarin hade rubutun screen din wayar, "Blossom" katsewa kiran yyi aka sake kira, kamar ance ta juya suka yi ido hudu da shi a tsaye ya rungume hannu yana kallonta, daburcewa tayi xata mayar da wayar ta ajiye masa nan bakin center table din ya fado kasa, ta mike a tsorace tace "Dama kiran ka ake" karasowa yyi ya dau wayar fuskarsa daure yana duba screen din, juyawa tayi da sauri xata bar wajen yace "Tsaya nan..." Tsayawa tayi amma ta ki kallonsa, Sternly yace "Baki da hankali ne?? Ba na hanaki ma shigowa parlon nan idan ina nan ba? Ko don kinga ina kyale ki??" Tayi narai narai da ido tace "Kitchen xanje sai naji wayar na kara" Tsawa yayi mata yace "Ina ruwanki da wayar? Ko ke kika ajiye min a nan?" Ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, on a serious note without bothering ko ta gane turancin nasa ko bata gane ba yace "Naga kina neman fara wuce boundaries din ki a gidan nan, to bari kiji, daga yau, i mean daga yanxu da kike tsaye nan kada ki sake shigo min parlor idan ina gidan nan, idan kin tashi da asuba kafin in fito da safe dama ki girka duk abinda xaki girka na safe da rana ki kai dakin ki, karfe biyar na yamma ina sama, sai kiyi amfani da wannan opportunity din ki sakko ki dafa abinda xa ki ci da daddare, kafin shidda ki tabbatar kina dakin ki.... Am i clear?" Ita dai kanta na kasa, ya mata wani tsawa yace "Baki ji na ne?" Ta dago kanta hawaye cike idonta tace "Toh" Yace "Get out.. Tafi ki ban waje" Juyawa tayi a hankali ta wuce sama, ya xauna yana sake kallon wayar tasa da screen ya tsage. Abuturrab bai yi mamakim k'in daga kiransa da El-Basheer yyi ba, don ya kirasa ya fi sau biyu yaki dauka, Da yammacin ranan Abuturrab na operating laptop dinsa a parlor aka danna bell, wani faduwa gabansa yyi ya mike yana kallon kofar, bayan few seconds ya isa kofar yace "Who is there?" Muryar Umma yaji tace "Ni ce" Ya d'an buda ido da mamaki sai kuma ya bude kofar, lkci daya kuma yyi pretending as if he wasn't even surprise yana murmushi ya bata hanya, yana shafa kansa yace "Welcome Umma, sannu da xuwa" Ta shigo parlon tace "Unexpected visit... Ban ce xan xo ba ko?" Yace "Ai ba sai kin ce min ba Umma, ya hanya?" Ta xauna saman kujera tace "Alhmdlh, ina jiddar?" Ya d'an kalli sama sannan yace "Tana sama" daga haka ya wuce sama, calmly ya bude kofar dakinta, xaune ya ganta can karshen gado ta takure waje daya, tana ganinsa ta sauke kafarta ba tare da ta yarda ta sake kallonsa ba, kallon idanuwanta da suka yi ja yyi, kana ganinta kasan kuka tayi sosai, ya hade rai yace "Wani abu aka maki da kika xauna kike kuka?" Ta girgixa masa kai kawai, ya dinga mata wani kallo kafin yace "Tashi ki wuce bandaki ki wanke fuskarki ynxu" sauka tayi daga kan gadon ta shiga bathroom tayi yanda yace, yana tsaye dakin har ta fito yace "Dauka Hijab din ki" Ba musu ta dau hijab din ta saka, yana son mata warning ko da umma xata yi mata wani tambaya ta bata positive answers but ya fasa sanin cewar baxa ma ta ce da umman komai ba, kofa ya nuna mata alamar ta fita, ta fita dakin ya bi bayanta, wuce ta yayi, ya riga ta sauka downstairs, Yana kallon Umma da murmushi fuskarsa bayan Jiddah ta sakko parlon yace "Daxu take kuka umma wai in kai ta wajen ki, but yau xa mu wuce kano and ina wani aikin shi yasa ban kai ta ba" Umma dai bata ce masa komai ba sai kallon Jiddah da ta nufo ta tana murmushi a sanyaye tayi, dukawa tayi kusa da ita a hankali tace "Umma sannu da xuwa" Umma na kallonta tace "Me ya sami idonki?" Abuturrab yace "Kuka tayi, wai in kai ta can gida wajen ku, nace ba yau ba" Still Umma bata kallesa ba, Jiddah dai kanta na kasa tana wasa da fingers dinta, Umma tace "Toh je ki dauko abinda xaki dauka mu wuce yanxu" Abuturrab ya bude ido da sauri yace "Umma ta fara karatu fa" Daga kasa Umma ta kallesa har sama sannan tace "Is that so?" Ya sunkuyar da kansa yace "Eh Umma, tare xa mu koma kano da ita" Lkci daya hawaye ya kawo idon Jiddah tana kallonsa, Umma tace "Toh shkkn, Allah ya taimaka, dama anguwan na shigo shine nace bari in karaso mu gaisa, i will take my leave now, tunda na same ku lafiya Alhmdlh" Yace "Umma da wuri haka, ki bari after magrib...." Ta katse sa tace "Ohk da magariban xa ku dau hanyan kanon kenan?" Shiru yayi bai ce komai ba, ta mike tana kallon Jiddah tace "Toh xan koma jiddah" Kasa dago kai Jiddah tayi, Abuturrab yace "Toh mun gode Umma, Allah ya kara girma" Jiddah ta share idonta a hankali tace "Sai anjima Umma" Duk da tausayinta da Umma ta ji sosai amma sai bata wani nuna ba ta nufi kofa tace "In dai xan xo ki dinga kuka gwara kar in sake xuwa, kusan sati biyu ai ya kamata ki sake haka ko..." Jiddah ta bi ta da kallo hawaye na sauka idonta, wani kallo Abuturrab yyi mata sannan ya bi bayan Umma, Umma bata wani sauraresa ba har ta hau motar ta ta wuce, ya shafa kansa ya bi motar da kallo, juyawa yayi ya koma cikin compound din, bai tadda Jiddah a parlon ba, hakan ya sa ya wuce sama ya bude kofar dakinta ya shiga yaga bata ciki, shesshekar kukanta ya ji a bandaki, ya karasa kofar ya murda yaji ta kulle da makulli, ya hade rai yana knocking kofar yace "Ohh har kuka kika samu damar yi kenan, toh bude kofar kar ki bari in bude da kaina" Kin bude kofar tayi ta kara rushewa da kuka kamar an aikota, bude baki yyi da mamaki, duk yanda yayi Jiddah ta bude kofar kin budewa tayi, har dai ya dawo kwantar da murya amma kamar yana dada tunxurata, banda kuka babu abinda take, kallon agogo dake nuna shiddah da few minutes yayi ya xauna gefen gado yayi wani sigh, a ranan ya ke son komawa kano but he just can't go like that.... spare key din bandakin ne ya fado masa ya mike da sauri ya fita xuwa bangarensa, sai bayan da ya dauko ya koma dakin ya fara addu'an Allah yasa ta cire makullin daga jikin kofar, yana sa makullin kuwa ya ki budewa alamar makulli na jiki, rungume hannunsa yayi yace "Baxa ki bude kofar ba malama, kin san kina bata min lkci kano xan wuce?" Bai ji alamar xata bude kofar ba, but kukan nata da ya daina ji yasa yaji hankalinsa ya tashi bayan ya tuna da vow din da tayi kwanki wai xata kashe kanta, ya ga fa kamar ba seti gareta ba, ya kwantar da murya yace "Jeeddarh..." Nan ma bata amsa ba, rasa abinda xai yi yyi, a haka har aka kira magrib, hankalinsa ba a kwance ba ya tafi yyi alwala a parlor sannan ya wuce masallaci, ana idar da sllh da ya shigo gida dakinta ya kara shiga, har lkcn tana cikin bandakin, jingina yayi da kofar a hankali yace "Jeeddarh" bata tanka sa ba, hakan yasa yace "Ohk to ki gaya min me kike so, ni kuma xan maki" Jiddah dake durkushe jikin kofar ita ma, ta daga kai a hankali jin abinda yace, ya kara kwantar da murya yace "Kin ji?" Tana goge idonta tace "Gidanmu nake son in koma" Buda ido yyi da mamaki jin abinda tace, yace "Wani gidan naku?" Tace "In da ka gan ni mana" Rungume hannunsa yyi, bai san lkcn da yayi murmushi ba yace "Can hayin rigasa?" Tace "Ehh" yace "Kin tabbatar?" Hawaye ya silalo idonta tace "Ehh" Yace "Tohh shkkn bude kofar, sai mu tafi" Tana goge idonta tace "Ni ban yarda ba" Yace "Kinga ina karya? Da gaske nake xan kai ki, ba dai har kin gaji da xaman gidan nan ba" Tace "Ehh, na gaji... Wajen Baabarmu xan koma" yace "Toh bude kofar, dare na yi" mikewa tayi a hankali ta bude kofar, ya koma gefe yana jiran ta fito, tana fitowa suka yi ido hudu da sauri ta sunkuyar da kanta, ta wani sha kunu, har hakan ya so bashi dariya, yace "Toh hada kayan na ki" Kallon jakan da Umma ta bata tayi sannan ta nufi gun jakar, yana kallonta ta fara hada kaya, har ta gama ta daga jakar sama, yace "Ina ma kika ce in kai ki?" Tace "Gidanmu nace" yace "Toh tafi parlor da jakar ki jirani" Jan trolley din ta fara yi ta nufi kofa ya bi ta da ido har ta fita sannan shi ma ya fita ya tafi bangarensa, Jiddah na parlor ta xauna kasa tana jiransa, banda wasa da yatsunta babu abinda take har ya sakko rike da makullin motarsa, ba tare da ya kalleta ba yace "Mu je" mikewa tayi tana jan trolley din ta bi bayansa, bakin motarsa ta tsaya ganin ya bude Booth ta saka trolley din a ciki, sannan ta tafi ta bude gaban motar ta shiga, ya tada motar suka bar gidan. Tun jiddah na kalle kallen hanya ko xata ga sun shigo titin anguwar tasu har ta fara ganin daji babu alaman gidaje, driving kawai yake da speed amma kuma da nutsuwa, marairaicewa tayi ganin kamar sun fita gari tace "Ina xa mu je?" Ko tanka ta bai yi ba hakan yasa bata sake ce masa komai ba, sai hawaye, duk da baccin da ta dinga ji har suka shigo garin kano wajajen karfe sha daya bata
Chapter 73 · 0% Book details