Sashe 18
Jiddatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hansai ta shiga kame kame tace "Gashi babu ma wajen xama a nan Alhaji, ko xa ka shigo daga ciki a shimfida maka tabarma" Yace "Aa nagode, hakan ya isa..." Tana murmushi tace "Allah sarki... Da yake jiddar na daurayan kwanuka shine nace 'yar uwarta ta fito, jiki kam alhmdlh taji sauki sosai, duk ta shanye magungunan nata..." Abuturrab ya sauke idonsa kasa yace "Allah ya kara mana lafiya gaba daya" Hansai tace "Ameen, bari dai kawai in shiga in turo ta ku gaisa, ai yanxu nasan ta gama" daga haka ta shige gida ganin dai babu alamar Abuturrab xai bata komai, jiddah ta nufa da sauri, murya can kasa kasa tace "Tashi ki dau hijabinki ki saka ki fita yana nan kila ya fi gane ya baki, kada ki kuskura ku tsaya kofar gidan nan ki ja shi can karshen layi sbda yan sa ido, gashi iliya na gari, daga nan ma sai ki sanar masa bikin ki sati me xuwa ne idan Allah ya kai mu, kinga idan da akwai wani alkhairin da xai maki sai ya maki, kowa dai yasan ke marainiya ce ba uwa ba uba" Bibalo da ke tsaye kansu tana sauraron abinda suke cewa tace "To Baabarmu idan yaji xata yi aure fa kilan shkkn baxai sake dawowa ba, dama ba sbda awaran da take yi bakin titi bane yake tausaya mana yake bamu kudi?" Hansai tayi shiru, can tace "To kuma aure ae dole tayi abu saura sati daya dai har an gama komai, kawai ta gaya masa.. sannan ba ga ki ba, ai ke xaki ci gaba da yin awaran a bakin titi" Bibalo tace "Cabdijam, wllh baxan yi awara bakin titi ba kawayena da samarina na ganina, haka kawai?? sai dai ke ki dinga yin kayanki ni dai baxan yi ba, to ni ma ba sai a min auren ba kawai" Tana fadin haka ta shige daki tana gunguni, Hansai ta rike ha6a tace "Ikon Allah, yau naga jarababbiya, a maki aure? Duka nawa kike xa a maki aure, ita ma Jiddar ai don iliyan ya dade yana sonta ne kuma ya mana hidima ba kadan ba, ko so kike ya mana tijara yace sai mun biyasa? A gidan uban wa ma xan samu abun biyansa? ke kuma da nake da burin in samar maki makaranta cikin gari ki fara xuwa kya kawo xancen a maki aure, a can din sai kiga Allah ya hadaki da miji dai dai ke, nan banda yan kato da gora, da yan adaidaita sahu, ga leburori, ga yan gwangwan sai yan iskan anguwa, to waye sa'an auren ki duk cikinsu? Ai babu sa'an auren ki wllh, ke da kike matar babban mutum" Hansai ta kalli Jiddah da kanta ke kasa har lkcn tana sauraronta, ta hade rai tace "Baxa ki tashi kije ba kin bar bawan Allah tsaye a waje" Jiddah ta mike a hankali ta dauraye hannunta ta shiga daki ta dau Hijabinta ta sa, ta saka takalminta sannan ta fita Hansai ta bita da sauri murya can kasa kasa tana cewa "Ku bar kofar gidan ku je can bayan layi kada a samu me kai ma Iliya rahotu" Ita dai bata ce komai ba har ta fita, yana tsaye ya rungume hannayensa, a hankali ta karasa can jikin wani tsohon adaidaita da aka yi parking gaba da gidan nasu, ya bi ta da kallo sannan ya bi bayanta, jingina tayi da adaidaitan tana kallonsa cikin sanyin murya tace "Sakon da kace xaka kawo min fa?" Yayi shiru yana dubanta, ta fashe masa da kuka tace "Kasan baxa ka kawo min ba me yasa kace xaka kawo min?? Alkawari fa ka min" Ya rungume hannunsa yace "Ohk abinda kika ce xa ki sha??" Ta gyada masa kai hawaye na sauka idonta, yace "Yaushe xa a daura maku auren?" Tace "Sati me xuwa, don girman Allah gobe ka kawo min, naje na tambaya a shago ance min ba dari biyu bane, kuma ni dari biyu gareni" Bude baki yayi yana kallonta da mamaki, can yace "Yaushe kika je kika tambaya?" Cikin rawar murya tace "Jiya" Ya sauke idonsa yace "To ai ni nace xan kawo maki ko? Kuma ban manta ba" Tace "Toh baka sake xuwa ba ai tun ranan" Yace "Toh gobe xan kawo maki" Ta gyada masa kai tana goge hawayen da ya ki tsaya mata, Sauke idonsa yyi kasa yace "Wa kika sani a kaduna bayan Baabar nan taku?" Ta girgixa masa kai a hankali tace "Ba kowa" Yace "Wa xai daura maki aure?" Cikin rawan murya tace "Kawu Jibril" yace "Waye shi?" Tace "Kawun Baabarmu ne shi" Shiru yyi na kusan minti daya sannan yace "Ki koma kice da Baabarku xan yi magana da ita" Juyawa tayi ta koma ciki, Hansai na xaune tsakar gida tana fifita tana jiranta, ganinta ta mike da sauri tace "Ya aka yi kika dade, nawa ya baki?" A hankali Jiddah tace "Yace xa ku yi magana da shi" Hansai ta hade rai tace "Bai baki komai ba?" Jiddah ta gyada mata kai, Hansai tace "Toh ba naje ba mun gaisa, maganar me kuma xa mu yi" Bibalo ta leko tace "Ke dai kije ki ji abinda xai ce maki kawai" Hansai ta nufi kofar gida da sauri, tana ganinsa ta sunkuyar da kai tana d'an murmushi tace "Cewa tayi kace xa mu yi magana ko?" Yace "Eh, yanxu take gaya min sati me xuwa xa ayi aurenta" Hansai tayi kasa da murya tace "Wllh kuwa, tun uban na da rai ya ci bashin da ya fi karfinmu, bamu da halin biya, to dai kusan auren biyan bashi ne, tunda mu dai bamu da kowa duniyar nan banda Allah, bamu da kowa bamu da komai sai rubabben gidan can, to ya xan yi??" Tana fadin haka ta fara matsar kwalla, kallonta kawai Abuturrab yake da mugun mamaki, can yace "Nawa ne kudin bashin?" Goge idonta ta dinga yi tana tunanin kudin da xata lafto, can dai tace "Dubu dari ne da ashirin wllh" Yace "Ina shi me kudin?" Nan fa hankalin Hansai ya tashi, cikin rawan baki tace "Ehh to ba garin yake ba, kawai sai dai a kai masa, noma kawai yake yi a nan amma ba d'an garin bane" Abuturrab yace "Ohk, shi ne xai aureta?" Tace "Ehh, Aa ba shi bane gaskiya, d'an sa xai aura ma, ehh babban d'an sa xai aura ma" Abuturrab yace "Ohk, dama akwai wani aiki ne da nake son in bata ta dinga yi, duk wata xa a dinga biyanta dubu dari biyu, kinga idan tayi aure baxai yiwu ba, naga kuma ta fi 'yar uwarta kwazo, dama tana farawa da wata biyu sai a kawo yar uwartata, kafin nan ita ta kware sai ta dinga sa 'yar uwar a hanya" tuni xufa ya fara keto ma Hansai tana kallonsa tace "Dubu dari biyu fa kace Alhaji?" yace "Ehh haka albashin yake, amma dai yanxu xan je in ciro kudi in bata sai ta kawo maki ki biya bashin... Xancen auren kuma sai a fasa shi" Hansai na share wani xufa da kyar tace "Toh ai shkkn Alhaji, Allah ubangiji ya kara maka girma da daukaka, yanda kake rufa mana asiri haka Allah xai rufa maka asiri kai ma" Yana kallonta yace "Ameen, amma kina ganin auren xai fasu idan aka biyasu bashin su?" Da sauri Hansai tace "Ba dole ba, dama ai sbda kudin ne suke son rabani da diyata" Yace "Toh xan je in ciro kudi yanxu..." Hansai tace "Toh turo maka ita xa ayi kuje tare?" Yace "Ehh" juyawa tayi da sauri ta koma ciki, Jiddah na daki ta hade kanta da gwiwa Hansai tace "Jiddah tashi xa ku je ya baki kudi ki kawo yanxu, duk abinda yace maki kar ki kuskura kice ba haka bane, komai yace kice masa ehh haka ne, kinji me nace??" Kallonta kawai Jiddah ke yi, Hansai ta hade rai tace "Baxa ki tashi ba an bar sa a tsaye" a hankali Jiddah ta mike ta fita dakin, yana nan tsaye ta samesa, Sai da ya kalleta sannan ya fara tafiya, bin bayansa tayi har suka isa bakin titi inda motarsa yake, Bank ya tafi a can cikin garin don cire kudi a Atm machine, ta bi sa da kallo bayan ya sauka motar, bayan wani lkci ya dawo ya shiga motar ya dau karamin leda ya xuba kudin a ciki ya ajiye, bayan few seconds yace "Tace auren biyan bashi xaki yi" Ba tare da ta kallesa ba tace "Ba haka bane" ya kalleta da sauri yace "To ya ne?" Hawaye ya kawo idonta tace "Kawai aure take son yi min da iliya sbda yana kawo mata abubuwa daga legas idan xai dawo" Abuturrab yace "Shi a ina yake xaune a kaduna?" Tana share idonta tace "Nan hayi yake shi ma" Yace "Xa ki nuna min gidansu?" Ta d'an yi shiru kafin ta gyada masa kai, tada motar yayi suka bar wajen, sai da suka shigo hayi yace "Ina ne gidan nasu?" Tace "Can gaba ne amma hanyar bbu kyau mota baxai shiga ba kuma da akwai nisa, dole sai da adaidaita" Yace "Ohk..." Ta gyada masa kai kawai, dai dai layinsu ya tsaya, ta dinga jiran ya bude mata motar ganin bai bude ba ta kallesa, yace "Yanxu idan aka fasa auren naki xaki hakura da kashe kan naki?" Shiru tayi tana kallonsa, ya d'an hade rai ganin kallon da take masa yace "Ina sauraron ki?" Sunkuyar da kanta tayi tace "Ehh" bude mata motar yayi ya mika mata ledan kudin ta amsa, xata sauka yace "Jira" Komawa tayi ta xauna tana kallonsa, yace "Kin iya amfani da waya?" Ta kallesa sannan ta girgixa masa kai alamar A'a, kunna fitilan motar yyi ya dau pen da wani karamin jotter ya rubuta numbersa ya mika mata yana dubanta yace "Idan da akwai wani abu ki nemi me waya ki kirani" Ta gyada masa kai, yace "Sauka" Ba musu ta sauka motar ta rufe masa ta fara tafiya.... Hansai na ta xaune tsakar gida tana jiran shigowar jiddah, sauro duk ya cijeta sai soshe soshe take, ganin jiddah ta shigo ta mike da sauri tana kallon ledan hannunta ta karasa kusa da ita ta amshe ta bude.... xaro