Sashe 102
Jiddatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yan acaba suma ai duk kabu kabun ce, to kuma waye shi Allah na tuba" Su dai basu ce mata komai ba suka fita dakin, sai a snn Maimoon ta mika ma Jiddah wayar tace "Yousuf" Jiddah ta amsa ta daga sannan ta kai kunne, murya kasa kasa Maimoon tace "Don Allah kice ya xo ya daukemu basu da nisa sosai daga nan" Tana fadin haka ta wuce bangaren Ummi, Jiddah ta nufi parlor, cikin sanyin muryarta tace "Ina kwana" Yace "Lafiya lau, me Maimoon take rada maki?" Murmushi tayi ta xauna saman kujera tace "Aa babu komai, ya ciwon kan yayi sauki?" Yace "Alhmdlh, ya su Umma?" Tace "Umma tana gida" Yace "Ku kuna ina?" Tace "Umma ta aiko mu gidansu Aunty Ramlah" Yace "Ohk, yaushe xaku koma gida?" Tace "Karfe biyu xa mu tafi Islamiyya" Yace "Baxa ku dade ba kenan?" Tace "Eh" yace "Toh in xo in maidaku gida?" Ta d'an yi shiru, yace "Kin fa ce kin daina taurin kai" D'an murmushin tayi ta kwantar da kanta jikin kujera dai dai nan suka yi ido hudu da Abuturrab dake xaune dinning area din parlon da laptop gabansa, wani faduwa taji gabanta yayi, Yousuf yace "Kinyi shiru" Ta dago kanta tace "Toh sai ka xo" Yace "Good, in few minutes time xan iso yanxu in sha Allah" Cikin sanyin murya tace "Toh" Katse wayar yayi, ta dinga kallon screen din, can ta saci kallon Abuturrab taga laptop dinsa yake dannawa, ta mike ta wuce part din Ummi, ya bi ta da ido. Karfe daya saura Yousuf ya iso kofar gidansu Abuturrab, ganin xa a tada sallah ya sauka ya shiga masallacin kofar gidan, bayan an idar ya kira number Maimoon, Maimoon ta mika ma Jiddah, Jiddah na kai wa kunne yace "Ina waje ku fito" Jiddah tace "Toh" Katse wayar yayi, suka yi ma Ummi sallama a bedroom dinta sannan suka fita, gaban Maimoon ya fadi ganin Abuturrab da ya fito daga masallaci, amma taki yarda su hada ido, Jiddah kam bata ma gansa ba ta kalli Maimoon tace "Ke da kike son ya xo ya daukemu ai ke xaki yi jagora" Maimoon tace "Don Allah ke dai mu je" Jiddah ta fara tafiya Maimoon na biye da ita, ta bude front seat ta shiga, Maimoon ta shiga baya, sai a sannan Jiddah ta ga Abuturrab da ya tsaya yana kallonsu, Yousuf da ya gansa shi ma yace "Ba yayan nan naku bane wancan" Maimoon ta kirki murmushin karfin hali tace "Ehh, kaje gu gaisa ya Yousuf sai kace masa Umma ce tace ka xo ka daukemu" Ta madubi ya kalleta ta kara kirkiran murmushi, Jiddah dai taki yarda ta sake kallon wajen motar, Yousuf ya bude motar ya sauka ya nufi gun Abuturrab da ya kara waya a kunne roaming about the gate, hannu ya mika masa hade da sallama yana kallonsa, Abuturrab yyi stretching nasa hannun, nan suka gaisa sannan yousuf ya juya ya koma gun motarsa, yana shiga motar Maimoon da duk hankalinta ya tashi tace "Kace masa Umma ce tace ka xo ka daukemu?" Yousuf yace "He don't have any business with that" Maimoon bata kuma cewa komai ba, ya tada motarsa suka bar anguwar. Hansai ce xaune da aminiyarta Zulai gaban wani katon mutumi da babu riga jikinsa, Hansai duk ta baxa kunnuwa da idanuwa tana jiran jin abinda xai ce bayan ya gama dube dubensa, Mutumin ya kalleta da idanuwansa da aka lafta ma uban kwalli yana girgixa kai cikin katon muryarsa yace "Babu wani aure a kan yarinya, amma tana can cikin kwanciyar hankali da daula... Bata da wani matsala a rayuwa, ba abinda ta rasa..." Hansai ta sharce wani bakin xufa a goshinta tace "Toh Malam babu abinda xa ayi da xai sa hankalinta ya karkato ta dawo gida, idan ya so sai a maida min Bibalo can, wllh Malam ina fama da bakar talauci yanxu, jarin babu shi babu dalilinsa kamar dai kar ta bar wajen yarinyar, ga basussukan jama'a a kaina suna min tonon asiri har na fara tunanin in siyar da d'an gidan da muke ciki in biya bashi sai mu kama haya da sauran, in sake jan wani jari, to amma gidan fa duk ya ru6e, wa xai siya da mutunci" Mutumin wanda da alama ya gaji da surutunta yace "Ki fadi abinda kike so ayi a takaice" Hansai ta gyara xama tayi kasa da murya tace "Kaga Malam so nake kayi duk abinda xai dawo min da ita duk inda take, ta dawo wajena ni ban k'i ko karuwanci ma ta xo ta min ba mu samu na rufa ma kai asiri, nasan dai yanxu karya ne ace bata san maxa ba, dama gata da kyau ga farin jini wllh kasuwa xa mu yi sosai" Zulai sai gyada kai take, Mutumin yace "An gama, dubu hamsin kudin aikin ki" Zulai ta dafe kirji tace "Dubu ashirin fa Malam, ina nagansa? Bani da shi bani da dalilinsa wllh, ko dubi daya na kaina bana magani yanxu" Yace "Toh ku tashi ku tafi duk ranan da ku ka shirya ku dawo" Xata yi magana cikin tsawa yace "Ku fita nace sai kun shirya" Da sauri suka mike suka fita a d'an dakin, Hansai ta fashe da kuka tace "Yanxu ya xanyi Zulai, kema kinsan bani da ko dubu biyu na kaina wllh, duk na siyar da kayan dakina babu komai balle in dauka in siyar" Zulai tace "Daga karshe dai gidan nan kawai xaki siyar in dai bukata xai biya, in har Jiddah ta dawo ai sai kin kera wanda ya fi wannan a cikin gari, dama ba sai an 6ata ake gyarawa ba, kawai mu je a sa gida a kasuwa..." Hansai ta share idonta tace "Toh shkkn, in sha Allahu baxan ji kunya ba" Daren ranan Jiddah na karatu a dinning kamar yanda ta saba bayan magrib aka bude kofar parlon, Hajja ce ta shigo sakale da jakarta tace "Assalamu alaikum" Jiddah ta amsa sallaman tana mata sannu da xuwa, Hajja tace "Ina Ramlan take?" jiddah ta mike tace "Tana daki bari in mata magana" Hajja tace "Toh yi maxa wancan d'an daban sai ya iya tafiya ya kyaleni, kinsan dama da kyar ya kawoni sai da uban ya sa baki" Jiddah dai bata ce komai ba ta tafi dakin Umma, ba a dau lkci ba Umma ta fito sanye da Hijab da murmushi tace "Sannu da xuwa Hajja" Hajja tace "Yauwa Ramlah daxu naga abun arxiki shine nace bari dai in taso in xo da kaina inyi godiya, don mu a Masar haka ake, Allah yayi maki albarka ya kara arxiki sai dai tafiyar ma ta lalace don wannan yaro Aliyu gobe xa a kai kudin aurensa kuma ina nan har sai anyi komai idan Allah ya yrda" Umma tace "Allah sarki, ai da kinyi waya na xo kawai Hajja ba sai kin fito da daddaren nan ba" Hajja tace "Aa barni na xo, banda me sonka wa xai tuna da kai har ya baka tsaraba haka..." Tana kai wa nan ta mike tace "Toh ni dai bari in koma ni da wancan d'an kabu kabun ne muka xo kar ya tafi ya barni in rasa tudun dafawa" Umma tace "Tare da Aliyu ku ke?" Hajja tace "Ehh wllh, sai da ma ya xageni a hanya muna tahowa daga nace masa ba jirgi fa yake figa haka ba, ni dai bakina alaikum naki biye masa ya kunyata ni a kasar mutane" Umma tace "Amma yace wani abu, shine baxai shigo ya gaisheni ba??" Hajja tace "Ahaf ai wannan mutumi dai daga d'an iska sai shi, baya ganin kowa da gashi" Umma ta kira Huraira a daki tace "Tafi kice ma Abuturrab ina kiransa a waje" Tace "Toh" sannan ta fita, Hajja ta koma ta xauna tace "Gwara dai kiyi masa soso da sabulu sannan ki hadani da d'an arxiki ya maidani gida kar kasheni a hanya" Umma dai bata ce komai ba, Maimoon ta fito tare da Safiyya suka gaidata, Hajja tace "Allah maku albarka, ya baku ilimi me amfani" Jiddah dai tuni ta koma ta ci gaba da karatunta a dining, Ba a dau lkci ba Abuturrab ya shigo parlon kansa a kasa, Ya karaso ciki ya gaida Umma da ladabi tace "Saboda ka isa yasa ka xo gidan nan ka xauna mota baka shigo gaisheni ba?" Ya ki kallonta a ido, yana kame kame yace "Aa waya nake yi a motar dama xan shigo Umma" Hajja tace "Karya yake algungumi har cewa yayi minti biyar ya bani wllh, ni dai ki hadani da me hankali ya maidani gidan d'a na don Aliyu abun tsoro ne, babu uwar da na hada dashi balle ya cuceni, gashi uwar tayi ta xuba masa ido kamar tana tsoronsa bata fada masa gaskiya, ita kuma yar Benuen can tayi kane kane a kan lamarinsa, ai ni ina ganin iftila'i tunda ja sauka gidan Usman, abubuwa suke babu tsari kamar dai gantalallu" Abuturrab dai sai kallonta yake ta gefen ido, Umma tace "Toh ka kyauta, from henceforth i don't want to see ur legs in my house again, get out" Bai ce mata komai ba ya juya ya nufi kofa ya fita, Jiddah ta bi sa da kallo, Hajja ta ajiye jakanta ta cire mayafinta ta linke ta ajiye, ta gyara xama tace "Dama idan babu me mayar dani gida sai dai in kwana a nan kawai, baxan bi mutumin can ba abu ya lalace min" Maimoon ta fashe da dariya Hajja ta marairaice tace "Allah kuwa ke baki ga yanda ya wani fita kamar Zaki ba daga fadan gaskiya" Umma tace "Kiyi xamanki kawai a nan Hajja" Hajja tace "Toh a kai min kayana daki" Karfe tara da rabi Umma na dakinta tare da Jiddah dake gyara mata press din kayanta, Umma tayi dialing number yayarta, nan kuma ta sanar mata duk abinda Aliyu yayi mata daxu, Ummi tace "Kiyi hakuri Ramlah, Ni yayi ma ba ke ba, kinsan wannan xancen auren da ya kirkiro ma kansa da Hafsah kawai suke sabgarsu, ban san komai a kai ba, uban ne ma yace min gobe xa su kai kudi, wllh bai ce min komai ba shi har yanxu" Umma tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Yaya ina