← Book details Jiddatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 109

Sashe 15

Jiddatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

tass sannan Hansai ta maka uban gyatsa ta mike ta shige daki tana cewa "Bibalo ke da yar yabi sai ku bibbi gobe ku kai cingam da sweet din sa ranan da aka yi, har yau ba a ba jama'a ba" Bibalo ta mike ta bi bayan uwarta tana cewa "Yo ai cingam din kwali daya ya rage..." Jiddah ta jingina da bango hawaye ya kawo idonta a hankali tace "Kuma bai kawo min piya piyan ba" Washegari lahadi Abuturrab ya fito gida misalin karfe sha daya na safe, Waya ne kare kunnensa yana driving a hankali don bai fita layinsu ba, girgixa kai yyi yace "No kai dai ka samu adaidaita ni na riga da na fito da mota, sai ka fadi inda xan sameka" Murmushi yayi bayan few seconds yace "Okay then, tunda kasan hospital din ba sai ka tafi ba" Yana fadin haka ya katse wayar hannunsa. Dai dai inda suka yi xai dau Ahmad yyi parking yana jiransa, bayan kusan minti goma Ahmad ya iso wajen da adaidaita ya shiga motar yana kallon Abuturrab yace "Amma ba yau xaka bar kaduna ba Captain" Abuturrab yace "probably.... Akwai abinda xan yi yau din" Ahmad yace "Ni train xan bi in sha Allah yau xan koma Abuja..." Abuturrab bai ce komai ba har suka isa wani hospital domin duba wani frnd dinsu da aka yi admitting, fruits iri iri suka siya masa a hanyarsu ta xuwa wajen, suna shiga ward din da yake suka tarar da abokansu hudu su ma sun xo dubiya, bayan an gaisa, wani frnd dinsu Umar na kallon Abuturrab cike da tsokana yace "Captain ko dai a hayin rigasa kake gini ne? Or probably neman aure...." Da mamaki Abuturrab ke kallonsa har ma da sauran abokansu, Ahmad yayi dariya yace "Haka yace maka Umar?" Umar ya gyara xamansa yace "To for the past 4 days kullum sai na ga motarsa a hayi" Abuturrab ya xaro ido yace "Ni kuwa?" Umar yace "Kai mana, yawanci kana ta daya side din nake ganinka, kai akwai ranan da ma na kiraka ina jin ka bar wayar a mota and u didn't even follow my miss call" Abuturrab yace "Subhanallah on a serious note ban lura ba...." Umar yace "To airport xa a bude mana a hayi ne kullum muke ganin Captain a can" Murmushin yake kawai Abuturrab yyi yana kallon Nasir dake kwance da drip a hannunsa yace "Barrister guda a gadon hospital, so how are u feeling now?" Nasir ya jefa masa wani kallo yace "Kai ma baka wuce a kwantar da kai gadon asibitin ba ai" Dariya kawai Abuturrab yyi, sun fi minti ashirin a dakin suna labarin duniya, daga karshe Ahmad ya sanar masu xa su koma bayan sun ma Nasir addu'an samun lfya, a tare suka fito da Umar daga ward din don shi ma wucewa xai yi, Abuturrab ya d'an kalli Ahmad dake bayansa suna magana da wani abokinsu da ya fito rakasu, ya kalli Umar da har ya kusa fita reception din hospital, ya kara pace dinsa har ya isa gunsa yace "Kai me kake xuwa yi hayi har kake ganina?" Umar yyi murmushi yace "A can fa Mahaifiyata take, so kusan kullum nakan je can din" Abuturrab yace "Ohhh Allah sarki..." Umar yace "To kai wajen wa kake xuwa?" Abuturrab ya d'an shafa kansa ya saci kallon Ahmad dake tahowa yace "Aboki nayi nima a can din" daga haka ya fiddo wayarsa ya d'an yi gaba kamar xai yi answering call don bai son Umar ya ci gaba da maganan gaban Ahmad. Abuturrab yana kallon Ahmad bayan sun hau saman titi yace "Gida xan sauke ka?" Ahmad yace "Yeah..." Driving kawai Abuturrab ke yi, Ahmad dake kallonsa yace "Wajen wa kake xuwa a hayi Captain?" Abuturrab ya kallesa da sauri cos the question came unexpected, ya dake yace "Ka yarda da Umar kenan, he was just pulling my leg idan ba dai a train station ba ya gan ni wa gareni a hayi da xanje? Wa na sani a hayi? Kawai dai idan mun hadu dole sai ya tsokane ni ne..." Ahmad na gyara xama yace "To na sani ko budurwa kayi a can baka sanar min ba kake boye min, ai idan tayi tsami ma ji" Wani kallo Abuturrab ya jefa masa yace "In rasa inda xanyi budurwa sai anguwar nan???" Ahmad na kallonsa da mamaki yace "Meye da su 'yan anguwan, ba mutane bane su din? Or sai da aka halicceka specially sannan aka halicce su aka ce maka? What's wrong with u Abuturrab? Why do u sometimes behave like...." Abuturrab yace "Illiterate right?" Ahmad yace "Of course" Abuturrab yace "Fine, but do not forget everyone is entitled to his or her opinion, ra'ayinka daban ra'ayina daban, kai xaka iya budurwa a can infact har ma ka aureta ku xauna a can din, it's ur opinion, ni kuma last thing da baxanyi ba kenan a rayuwata, and this is my opinion, so stay entitled to urs, and i stay entitle to mine also" Ahmad yace "Baxa ka iya aure a can ba sbda kafi su a wajen Allah ko??" Abuturrab yyi masa wani shegen kallo yace "Wai Ahmad ance maka ni kai ne?? Ni fa ina da class ina da taste, as in i am far beyond that ka daina yi min irin wannan maganan bana so wllh" Ahmad yyi d'an murmushi bai kuma ce masa komai ba, Abuturrab yyi tsaki yace "Haka kawai sai kace kowa sai ya bi ra'ayinka, kai mace ko min kazantarta da locality dinta xaka iya aurenta ku xauna lafiya, ni kuwa it's a big No for me, bana walakanta 'yan adam kai shaida ne, sannan kasan ko kai baka kaini tausayin d'an Adam ba, idan naga mutum na cikin damuwa ko wani yanayi more especially mace ina bakin kokarin ganin nayi duk abinda xan iya yi ko a ina ne kuwa, even with my last card i can help, amma sai ka dinga hadani da su kana wasu maganganu marasu ma'ana" Ahmad bai kuma ce masa komai ba har suka iso gidansu, Abuturrab yyi parking, Ahmad ya juya yana kallonsa still bai ce komai ba ya bude motar ya sauka ya rufe masa motarsa, tsaki Abuturrab yyi, yyi reverse ya bar layin kallon agogonsa dake nuna masa sha biyu da rabi yyi ya nufi gida kawai....
Chapter 15 · 0% Book details