Sashe 65
Jiddatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
now" ya ja hancinta yace "And ke kin fiye ma mutum jan aji ne" Rungumesa tayi cike da shagwaba tace "Wallahi ba haka bane, ae kai din ne sai ka xo Abuja kake neman mutum" ya cire hulan kanta yace "Ohh really??" Dariya tayi tace "Aa wasa nake my captain ni kadai...." yyi murmushi yace "In few days time su Abbanmu xa su je gidanku in sha Allah" ta wara ido tace "Da gaske my captain?" Yace "In sha Allah" Rungumesa tayi tace "I can't wait Babynah" ya d'an hade rai yace "Baby kuma?" Dariya tayi sosai tace "Au.. to yi hakuri na manta baka son sunan, amma fa kada wataran ka xo kayi ta rokana in kiraka da Baby" yace "Sai kace wani jariri" Dariya kawai take tana kallonsa don tun ba yau ba tasan bai son irin wannan soyayyan da yawanci yake kiransa da na yarinta, ta daura kanta saman shoulder dinsa tana jin wani sabon sonsa na fixagarta... Karfe daya saura few minutes Abuturrab ya fito bedroom dinsa bayan yayi wanka ya shirya cikin jallabiya, xaunawa yyi parlor yyi dialing number ya kai kunne, sae da ya katse ba a dauka ba sannan ya kalli agogo, ajiye wayar yyi ya kwanta saman doguwar kujera ya lumshe ido... Throughout week din nan Jiddah bata ji kadaici sosai ba don ranan laraba ma sai da Maimoon ta xo gidan, A ranan kuma Abuturrab yyi niyyar dawowa amma cikin ikon Allah sai bai samu dawowan ba, ranan alhamis Maimoon ta kara xuwa tare da Ramlah da abinci wanda Umma ta basu su kawo ma Jiddar, sosai Jiddah ta sake da su don ba kadan suke debe mata kewa ba, Ramlah ta dinga mamaki kamar yanda Ahmad yyi ganin ashe dai Jiddah na magana haka, ga dariya kamar me, xuwan su ya sa har ta samu confidence din fita suka xaga cikin gidan gaba daya tare da su, a nan ne ma tasan da mai gadi da matarsa a gidan, sai bayan magrib Umma ta aika driver ya je ya daukosu, Jiddah ranta fess ta ci sauran abincin da suka rage sannan tayi wanka tayi isha ta shirya ta kwanta, nan da nan bacci ya dauketa. Karfe tara saura Abuturrab dake xaune hotel room dinsa a kano yyi dialing number nata, har ya gama ring bata daga ba, da mamaki ya dinga kallon wayar, ya sake kira nan ma no answer, sake kira yyi ya sake ringing ya gama ba a daga ba, da yamma ma ya kira sau biyu no answer, a lkcn kuma Jiddah na can compound tare da su Ramlah, ajiye wayar yyi, can ya mike ya shirya within few minutes ya dau makullin motarsa da jakar laptop dinsa ya fita dakin, abinda bai ta6a yi ba xai yi ranan, wato driving to kaduna at night, dama da asuba yyi niyyar komawa kaduna sbda throughout gobe ba shi da duty, amma yanxu yyi deciding din tafiya kawai, sai kusan sha biyu da wani abu Abuturrab ya shiga gida yyi parking mai gadi ya taho da sauri yyi masa sannu da xuwa, amsawa yyi ya wuce ciki, makulli ya ciro ya bude kofar dake a kulle, Jiddah bata mance warning din Ahmad na cewar duk wanda ya xo kar ta mance kulle gidan da makulli bayan ya tafi ba sannan ta boye makullin, bin parlon ya dinga yi da kallo, ya kashe wutan dake a kunne ya wuce sama, kofar dakinta ya bude, kwance ya ganta tana bacci cikin nutsuwa, karasawa cikin dakin yyi still looking at her da wani expression can ya juya ya fice daga dakin ya tafi bangarensa. Washegari da safe bayan Jiddah tayi wanka ta shirya ta fito daga dakinta, cak ta tsaya jin kamar tana jin murya a can daya part din, to ko tv ne a kunne, ko ma ita ce ta ta6a abu da ya kunna tvn ranan da ta shiga dakin bata sani ba, gabanta na faduwa ta fara tafiya xuwa can din a hankali, har ta isa sannan ta bude kofa cikin nutsuwa tana lekan parlon, babu wani tv dake a kunne ta dinga bin parlon da kallo, sai taji ba tv bane karatun qur'ani ne, har xata juya ta d'an yi jim kamar me shakkar shiga ciki, can dai ta karasa ciki tana kallon kofar bedroom din da ba a rufe ba gaba daya, tunani ta dinga yi ko ita ta bar kofar haka jiya, a hankali ta kutsa kai ciki, wani kara tayi a tsorace ganin mutum kwance with short and singlet yana bacci, ta juya da sauri ashe ta mayar da kofar ta ci karo da kofar, wani ihun ta kuma yi ta dafe forehead dinta....