Sashe 56
Jiddatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar wanda ya tuna abu ya sake juyowa, rarrafawa yaga tayi xuwa gun da hijab dinta yake xata dauka, ya hade rai sosai yace "Ina wayar da na baki?" Ta juya ta kalli gadon dakin, a hankali tace "Ya fada karkashin gadon na kasa daukowa" Da mamaki ya dinga kallonta, ta sunkuyar da kanta, can yace "Wa ya jefar karkashin gadon?" Ta sake kallonsa tace "Xamewa yayi ya shige ban sani ba" cikin tsawa yace "Saboda ke yar yarinya ce ko?" Shiru tayi bata ce komai ba ya juya ya fice daga dakin ya kulle kofar, da kyar ta lallaba tayi shafe shafen mayukanta da turarruka sannan ta dauki wani rigar bacci ta saka tana dingishi ta hau saman gado ta kwanta, mamaki ta dinga yi na yaushe ya shigo gidan bata ji karan shigowar mota ba, ko dai bai dawo da motar bane, kuma ai ce mata yyi sae karshen sati, da wannan tunane tunanen bacci yyi awon gaba da ita. kasa bacci Abuturrab yyi sbda shayi da bai sha ba, don ya fara shan shayin kenan ya bari ya taho, shi kuma idan da abinda ke takurasa rashin shan shayin dare, ji yake yunwa na damunsa indai bai sha shayi ba, and he detest making tea himself, da dai yayi da kansa gwara kar ya sha, rub da ciki yyi ya lumshe ido hoping to force sleep, wajen karfe daya da rabi ya mike ya fito daga bangarensa, downstairs ya sauka ya shiga kitchen ya bude fridge, kallon fridge din ya dinga yi don bai ga alamar ta ta6a komai na ciki ba tun jiya, ya dau Chivita daya ya bude ya dau glass cup bayan ya dauraye ya xuba a ciki, sau biyu ya cika ya shanye sannan ya mayar fridge, da ya hada shayi gwara yyi hakan, fitowa yyi daga kitchen din ya xauna saman kujera a parlon cikin duhu, yana ta xaune har karfe biyu sannan ya mike ya haura sama, har ya nufi part dinsa ya dawo ya bude kofar dakinta, cikin duvet ya ganta ta takure waje daya tana bacci, ya karasa cikin dakin ya janye duvet din, dukawa yyi yana kallon kafarta sannan ya d'an danna kafar, da sauri ta janye ta juya masa baya, sake kai hannu yayi ya kamo kafar, da sauri ta bude ido, ya hade rai amma bai ce komai ba ya mike ya sake dauko man xafin, a hankali ya shafa mata sannan ya mike ya kashe wutan dakin ya fita. Da asuba bayan ya dawo masallaci ya fara tunanin ta yanda xai koma kano babu mota, gashi bai fiye son shiga commercial vehicles ba, karfe bakwai ya gama shiri ya fito daga bangarensa, dakinta ya murda a hankali ya shiga, a kwance ya ganta amma idonta biyu, ganinsa ta mike xaune da sauri... yace "Kafin in dawo ran juma'ah ki tabbatar kin fito da wayata da kika jefar karkashin gado" shiru tayi bata ce komai ba, yace "Sannan kayan marmarin da na xuba a fridge ki tabbatar kar in dawo in sami ko daya" Daga haka ya juya, da sauri tace "Tafiya xaka yi?" Yace "Aa xama xan yi" sai bayan da ya fita ya fara tunanin wayar da xai sake bata, he just need to hand a phone over to her, shi kuma bashi da strength din daga kayan gado da sassafen nan, can dai yyi deciding ya koma dakin ya ga inda ta jefar da wayar tukun, Yana shiga bai ko kalleta ba ya nufi gadon ya fiddo wayarsa ya kunna fitila ya duka yana haskawa karkashin gadon, cikin few minutes ya ciro wayar da hannunsa, ita dai tana tsaye ta rakube gefe da hijab dinta har kasa, ya dago yana kallonta fuskarsa a tamke, ta sunkuyar da kanta, ajiyewa yyi kan gado ya nufi kofa ya fita ta bi sa da kallo, dole commercial car din ya tafi ya hau a park xuwa kano... Jiddah na xaune kasan carpet a parlon hannunta rike da apple biyu, ta kasa ci sbda rashin sabo da shi, tunda take a rayuwarta bata ta6a shiga matsatsi da takura irin wannan ba, duk da ba jin dadin xama take da Hansai ba amma ai xaman bakin titi ma da take ya kan debe mata kewa tana ganin mutane da motoci, amma tun shigowarsu gidan nan yau kwananta nawa bata ga kowa ba banda shi kadai, tunanin hakan ya sa hawaye ya kawo idonta, kallon ma sbda rashin sabo da shi da ta fara xata soma gyangyadi, Mikewa tayi a sanyaye tana goge idonta ta nufi wani window dake parlon ta makale jiki ta bude labulen a hankali tana lekan tsakar gidan, babba ne tsakar gidan da flowers masu kyau xagaye, ta dade tsaye wajen tana ta kallon tsuntsayen dake tashi da sauka a tsakar gidan, kiran sallan azahar yasa ta juya a hankali ta bar wajen tana kallon apples din hannunta kitchen ta koma ta mayar, marairaice fuska tayi tana kallon fruits din fridge din banda ayaba babu abinda ta iya ci a ciki ita dai, tana tafiya a hankali ta fita kitchen din. Hansai ce xaune gaban mai anguwa da Zulai da ta rakota, bayan sun gaisa, ta kunce ha6ar xaninta ta sakar masa kuka tana matsar kwalla da zanin tace "Wllh Mai Anguwa shiru shiru har yau babu yarinyar nan tawa babu labarinta fa, abun nan ya fara damuna duk inda taje ai ya ci ace ta dawo yanxu, yau fa sati daya cur ba ita ba labarinta, na rasa inda xan sa kaina, ga komai nawa ya tsaya kamar ta tafi da shi" Sae kuma ta rushe da kuka, Mai Anguwa dake ta kallonta da mamaki yace "Ikon Allah, ni ai na xata da naji shiru Allah ya sa ta dawo gida, toh ke duk kwanakin nan me yasa kika yi shiru kinsan bata dawo gida ba, sai yanxu xaki taho kice bata dawo ba" Hansai ta marairaice cikin rawan murya tace "Wallahi na danni xuciyata ce don ban debe tsammani ba, ina ta baxa ido amma naga shirun yayi yawa" Mai Anguwa yace "Cabb, amma kina da ganganci Hansatu, anya ke kika haifi yar nan kuwa kamar yanda kika ce?" Hansai ta kara marairaice masa cikin kuka tace "Nice mana Mai Anguwa, ina da kauda kai dai xaka ce kawai" Mai Anguwa yace "Toh, ranan dai na amshi lambar shi mutumin da ya aureta, wato shi matukin jirgin saman, kuma bayan wannan aure da kwana uku ya xo min har nan da mahaifinsa da kawunsa, mahaifin nasa sanannen mutum ne dattako kuwa a garin nan..." Hansai ta hadiye abu da kyar tace "Toh kira mana shi xaka yi yanxu kenan don Allah? Don dai gaskiya na fara xargin kilan ma ya ganta ya tafi da ita ne kawai bamu sani ba, banda haka me yasa xai yi shiru haka babu labarinsa, bayan gashi kace har ya xo da mahaifinsa, to idan haka ne ba sai sanda na ga damar basa matar xai tafi da ita ba, to wllh ni na canxa ra'ayi kan auren ma, ya dawo ya fadi nawa ya kashe ko gidan da muke ciki ne sai in sayar in biyasa, ba ruwana wllh" Mai Anguwa dake ta kallonta, ya d'an yi murmushi yana kara jinjina hali irin nata, ya fiddo wayarsa bayan kusan minti biyar yace "Alhmdlh, na samo lambar" Yana fadin haka yayi dialing number Abuturrab ya sa handsfree, kallon Hansai yayi bayan an sanar wayar baxai je ba, Hansai ta rushe da wani matsanancin kuka tace "To ko dai lambar karya ya baka, ni sai yanxa nake jin ma ban yarda da mutumin nan ba wllh, wa ya sani ma ko d'an yankan kai ne yace mana matukin jirgi ne shi, jirgi abar wasa ce da xai iya tukata bayan an sanar mana turawa ne kadai suka iya daga jirgi sama su tuka, sannan idan ba d'an yankan kai ba mutumi babu dangin iya balle na baba kayi ta kashe mana kudi haka daga jin an mana mutuwa, daga haduwar mu xuwa fa ranan da ya bada sadakinta wllh mutumin nan ya kashe mana yayi kusan rabin miliyan, to akan me? Aa wllh ya xo in biyasa ya maido min da 'ya ta" Mai Anguwa dai tabe baki kawai yake bai bata amsa ba, Hansai ta fara kokarin mikewa tace "Ai dai wayar baxata dauwama a mace ba, don haka ko gobe ma xan dawo sai ka sake gwada kiran lambar don ni bani da waya, haka kawai yarinya ta bace batt kamar yar kaza" Mai Anguwa yace "Allah ya kai mu goben" daga haka ta bar wajen tare da kawarta, Zulai tace "Anya wannan mai anguwan na da gaskiya kuwa Hansai?" Hansai ta kalleta da sauri tace "Atoh, nima shi na gani, baki ji har ya fara cewa Uban yaron sananne ne a garin nan ba, kawai dai sun danna masa uban kudi shi ma shine yayi mukus, to wllh a maido min da 'ya ta babu wani xancen auren karya" Zulai tace "Kuma fa da gaskiyan ki, ko dai wannan yaron d'an yankan kai ne, idan ba haka ba a wnn xamanin ina xai samo rabin miliyan ya kashe maku" Hansai ta tsaya tana kallon Zulai, can ta marairaice tace "Toh kuwa in har haka ne ya kassara ni, wa gareni da muke sana'a tare banda jiddar, ke baki ga ko me nasa Bibalo kin yi take ba sai ta nemi ta xageni, ai jiddah ita ce rufin asiri na a duniyar nan, gashi duk jarin na fatattakar, kuma sana'ar ba wani ciniki nake yi ba yanxu, uwa dai an juya min baya a anguwan" tana fadin haka ta fara matsar kwalla, Zulai tace "Toh da da kike shirin aurar da ita Jiddar ga Iliya fa?" Hansai ta ci gaba da tafiya tace "Toh ai ko daga gidan mijin sana'ar xan dinga bata tana min nufi na" Zulai ta ta6e baki tace "In ko ba d'an yankan kai bane to tana gunsa Wlh, abinda kowa dai ya shaida matarsa ce" Hansai ta share xufar goshinta tace "Toh uban me xai yi da ita wai Zulai, sai kiyi ta wani cewa matarsa, wllh babban mutum ne ko da kudi aka hadasa da jiddah banjin xai amsa balle bbu