← Book details Jiddatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 109

Sashe 80

Jiddatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

jira, kilan yana saman jirgin har yanxu" Yace "Yayanki... iyayenku daya da shi?" Shiru tayi can kasan ranta kuma tana tunanin abinda xata fada masa, yace "Ki gaya min gaskiya Jiddah" Ta kallesa still bata ce komai ba, yace "Ina sauraranki" ta kwantar da kai tace "Me yasa kake son sani?" Yace "I just..." Shiru yayi kamar wanda ya tuna abu, sai kuma yace "Kawai ina son sani ne" Tace "Ba iyayenmu daya ba amma yayana ne" A hankali yace "Ko dai saurayin ki Jiddah" Ta wani xaro ido, sai kuma ta kyalkyale da dariya tace "Saurayi na? Saurayina fa kace? Aa ni ba saurayina bane shi wllh, saurayina sunansa Umar amma mun rabu yanxu" Yace "Umar?" Tace "Ehh, shi wannan kawai yayana ne" Wayar hannunta ya amsa da sauri tace "Nace maka nasa ne wayar" Bude screen din yayi don wayar a bude yake, ya dinga kallon hulan pilot dake jikin screen din wayar, karban wayar tayi hannunsa, xuwa lkcn bbu kowa haraban parking din jirgin sai ma'aikatan airport, Yousuf ya daga kai yana kallon Abuturrab dake saukowa daga jirgin yana kallonsu babu ko kiftawa, har sannan pilot uniform ne a jikinsa, Jiddah ta daga kai ganinsa ta kalli Yousuf tace "Shine yayan nawa" Yousuf ya d'an yi murmushi yace "Shine matukin jirgin... i guess right" Juyawa Jiddah tayi da sauri tana kallon Abuturrab, Yousuf ya karasa gunsa ya basa hannu suka gaisa yana murmushi yace "I guess you did the landing..." Abuturrab na kallonsa ya d'an yi murmushin gefen baki kamar wanda aka tilasta ma yace "Yea, i did" Yousuf yace "Nice landing...." Abuturrab yace "It's a pleasure flying you" Yousuf ya masa murmushi sannan ya juya ya bar wajen, yana isa inda Jiddah take yace "Ina jiran kiranki kamar yanda kika yi alkawari ranan" Yana fadin haka ya wuce, Jiddah ta kalli Abuturrab da ya hade girar sama da ta kasa yana kallonta.... A motarsa suke tafiya xuwa hotel din da suka sauka a kano, har sannan babu abinda yace mata, sai dai fuskarsa bbu ko digon annuri, har suka isa hotel din, kulle dakin hotel din yyi after going in together with her, yana kallonta fuskarsa a tamke yace "Waye wannan mutumin da na ganku tare?" Tace "Wai da gaske kai ne kake tukin jirgin in ji sa? Ni dai nace masa ba kai bane ae baxa ka iya ba" fixgota yyi, tayi wani kara xata durkusa ya dagota yace "Tambayar ki nake waye shi??" Kamar xata yi kuka tace "Toh ba q jirgin muke haduwa ba" ganin taki tsayawa cikin tsawa yace "Baxa ki tsaya ba" Kin tashi tayi tace "Toh don Allah ka sakeni" kallonta kawai yake yi, can ya saketa, xamewa tayi ta xauna kasa, yace "Waje daya ku ka xauna da mutumin?" Tace "Aa, kawai da na sauka jirgin shine ya bi ni yana min magana" Shiru yayi yana kallonta ita dai bata yarda ta kallesa ba, can ya juya ya bude kofar dakin ya fita. Bayan la'asar suka bar kano xuwa kaduna a motarsa, Jiddah na kallonsa after the 20 mins silence tace "Meyasa muke ta shiga jirgi bayan ga mota, kyauta ake tafiya a jirgin ne?" Ya mata wani kallo yace "Kyauta? Tsoronki ake xaki shiga jirgi kyauta?" Tace "Toh Iyah ta ta6a ce min kudin jirgi yana da tsada kusan miliyan ne" Ya d'an kalleta yace "Haba??" Ta wara ido tace "Wllh, kasan ta ta6a xuwa makka sau daya, yaranta ne suka biya mata, toh ni na xata masu kudi ne kawai ke hawan jirgi" D'an murmushin da bai shirya ba yyi yace "Ni ba me kudi bane kenan?" Ta d'an xaro ido tana kallonsa tace "Aa bance haka ba, amma wannan motar taka ce?" Bai ce komai ba, a hankali tace "Kayi shiru..." Yace "Aa na Abbana ne" Tace "Toh gidan fa?" Yace "Wani gida?" Tace "Wanda muke ciki?" Yace "Shi ma na Abbana ne" Tace "Kenan shi ne ya biya kudin jirgin da muka shiga?" Yace "Ehh" Tayi shiru tana kallonsa, ta gefen ido ya kalleta, ta sauke idonta, bayan few seconds tace "Abbana ya ta6a ce min watarana xan shiga jirgi, amma Makka yace xanje" Ya kalleta yace "Haba" Ta gyada masa kai, tace "Kuma gashi na shiga amma ban je makkan ba" Yace "Toh idan kina da kudi ki kawo in biya maki Umrah ki je" Ta buda ido tace "Kudi?? A ina xan ga kudi ni ba sana'a nake ba" Yace "Ohk kina son kiyi sana'a ne? Ko awaran xaki siyar a bakin layin gidanmu?" Dariya ta fara yi, ya dinga kallonta don bai ta6a ganin dariyarta ba, tayi me isarta sannan tace "Idan kace inyi sai inyi in dai xa a siya" Da mamaki ya d'an kalleta kafin ya maida dubansa kan titi yace "Xa kiyi kenan idan nace kiyi" Tace "Ehh, sai in yi har da wainar flawa da dankali" Yace "Toh bari mu je a samar maki waje a bakin titin ko?" murmushi ya ga tayi tace "Toh" Ji yayi kamar ya fixgota ya rankwasheta, tace "Toh amma kudin xa su taru har in je makkan kuwa?" Yace "Wannan ke xan tambaya ai, babarku ta tara kudin ya isheta har taje makka?" Shiru tayi tana kallonsa, can tace "Toh ai abinci muke ci da kudin sana'ar, wannan kuma baxan siya abinci da kudin ba tunda akwai abinci a gida koh" Shafa millionaires belt dinsa yyi still wondering if yarinyar nan xata ta6a wayewa, though ya ma yi mamakin yanda har ta fara iya dressing ko don kayan da ya siya mata sunyi correlating da mahadinsu ne, sannan bai ga tana irin kwalliyan nan na masu talla ba, a ja gira a shafa barbada kumatu, a shafa gazal, babu wanda xai kalleta yace she is local or even an illiterate sai ya ji xancen dake fita daga bakinta, mamaki ma yayi yanda ta bude baki take creating conversation da kanta yau, muryarta yaji tana cewa "Idan kudin ya taru da yawa kai ma sai in biya maka tunda ka taimakeni koh?" Ya d'an kalleta da sauri sannan yace "Haba?" Tace "Ehh, ko kuma in biya ma Umma" Murmushin gefen baki yayi yace "Ashe na taimake ki?" Tayi shiru tana kallonsa, sai kuma ta gyada masa kai a hankali, Bai kuma cewa komai ba, kuma bai kalleta ba, jin tayi shiru bayan kusan minti goma sha biyar, breaking the silence yace "Bayan awaran da dankali babu wani sana'ar da xa ki yi?" Ya d'an kalleta da yaji bata amsa masa ba, bacci yaga tana yi, xuwa lkcn sun fara fita outskirt din garin kano, ya kai hannu a hankali ya kwantar mata da kujeran motar, snn ya kara Ac din motar, har suka shigo garin kaduna bayan magrib bacci take, amma ta farka yyi sau biyar a hanya, mai gadi na bude masa gate yayi parking a parking space, ya sauka motar yana stretching kansa, coz he is very tired bayan tukin jirgi ga na mota, jingina yayi da motar ya rungume hannunsa, har ya mance rabonsa da workout, tun sanda burden din Jiddah ya hau kansa, xagawa yyi ya bude side dinta ya bubbuga motar slowly, a hankali ta bude ido ta fara kalle kallen inda suke, yace "Sakko" sauka ta fara yi daga motar ya koma gefe tana fitowa ya kulle motarsa. Bayan sun shiga gidan xata wuce dakinta yace "Ki tabbatar kinyi sallah" Wanka jiddah tayi sannan ta dauro alwala bayan ta idar da sllh ta saka kayan baccinta ta kwanta. Karfe tara ya shigo dakin da abinci, tunda ya kalleta sau daya ya dauke kai, kawai ya ajiye ledan ya fita. Washegari da ya kasance ranan juma'ah Jiddah na idar da sallan asuba ta sauko kasa ta hada shayi ta dumama abincin da ya kawo mata jiya da daddare ta wanke tukunyar da ta bata ta koma dakinta, duk kafin ya shigo gidan daga masallaci, don sai ya gama azkar dinsa yake shigowa gida, bata mance warning din da yayi mata ba, ganin har karfe sha biyu Abuturrab dake xaune parlor bai ga ta sakko ba, lkci lkci kuma ya ke kallon sama, daga karshe ya mike ya haura stairs din sannan ya bude kofar dakinta, bacci ya sameta tana yi, yayi knocking kofar da karfi wanda hakan ya farkar da ita ta mike xaune da sauri, ya wani daure fuska yace "Baki da hankali har yanxu bacci kike?" Tace "Aa nayi wanka na gyara dakin" Ganin hararan da yake mata ta dauke kanta, yace "Ohk kin fi so ki kwanta daki kullum in fita in siyo maki abinci in kawo maki anjima kice ai bani da kudi?" Buda baki tayi tana kallonsa tace "Ni yaushe nace baka da kudi?" Ya rungume hannunsa yace "Jiya a mota" Tace "Aa ni fa kudin jirgi nace baka da shi tunda ya kai miliyan daya, kuma kace min Abbanka ne ya biya ai ko??" Yace "Ehh abincin da kike ci ma ai duk shi yake siyowa in kawo maki ko" Tayi shiru tana kallonsa, can tace "Toh me yasa baka son kayi sana'a, kaga Umar yana fita kasuwa kullum, don kawunsa na da shaguna uku a kasuwan bacci..." Kallonta yake ko kiftawa baya yi, tace "Kai ma xa ka iya ce a neman maka waje a kasuwa tunda Abba na da kudi ae" Ya shafa fine beard dinsa yace "Haka ne kuma, amma ya aka yi kika san bana sana'an komai" Ta sakko da kafafuwanta daga saman gadon tace "Naga to ko da yaushe kana gida, idan baka son ka xauna a gidan kuma sai ka tafi kano, to ko sana'a kake xuwa yi a kanon?" Ya girgixa kai da sauri yace "Can ma kawai xama nake a gida, ai ba a bani sana'an da xan yi ba" Tayi shiru, sai kuma ta kallesa tace "Amma lkcn da kake xuwa hayin rigasa a ina kake samo wannan kudin da kake bani in ba Babarmu?" Yace "Abbana ke bani" Tace "Toh, shkkn" Yace "Yanxu kasuwan xan fara xuwa nima kenan" Tace "Eh ka gaya ma Abbanka ya bude maka shago" Yace "Sai ni dake mu dinga xama a ciki ko?" Kallonsa tayi ta fashe da dariya sosai dimples dinta na lotsawa, ya dinga kallonta, second time da yake ganin dariyarta kenan, tayi me
Chapter 80 · 0% Book details