← Book details Jiddatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 109

Sashe 39

Jiddatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

relieve, Muryar Alhaji Lawal yaji yana cewa "Gobe asabar ka tare kawai da matarka, Allah ya sanya alkhairi, not too long sai ku shirya da ita ku tafi gaida mai martaba a bauchi" Abuturrab bai samu courage din ce masu komai ba, but he is boiling inside, dama taimako na iya xama fitina da tashin hankali haka bai sani ba??? Alhaji Ibrahim yace "Sai a kira Hajiya Hauwa ita ma aji ta bakinta tunda tana da right a kansa ko?" Abba ya dau waya ya kira Ummi, har da Aunty, Abuturrab ya ji dadi da Abba ya kira har Aunty don yasan she will stand for him, ba a dau lkci ba suka shigo parlon, duk suka yi ma 'yan uwan mijin nasu sannu da xama don tun xuwansu gidan suka gaisa, Alhaji Lawal ne yayi masu bayanin shawaran da suka yanke, Ummi dai ta kasa cewa komai, ita babban tashin hankalinta asalin yarinyar nan ba wai tana kin auren bane, ba a san wacece ita ba gashi yace uwarta da ubanta sun rasu sai kishiyar uwar, Aunty ta mike tana girgixa kai cikin tashin hankali tace "Haba fisabilillah, an ta6a aure dole ne? Tunda yace bai so, yayi auren nan ne kawai don taimako to a barsa ya datse wannan kaddararren auren mana, ai ya gama taimakon da yayi niyya, to meye kuma xa ayi ta cusa masa yarinya kamar ku ka aura masa ita, wannan ai kamar neman suna ne ku ke yi, banda haka wllh ko mahaukaci baxai amince da irin wannan auren ba, yarinyar da bata da asali ku ke burin d'an ku ya xauna da?" Alhaji Ibrahim yace "Ke kinje kinyi bincike kinga bata da asali Hafsah?" A fusace tace "Banda yanxu da na kawo maganan asalin ai babu wanda ya damu da hakan, haka kawai xaku yi ma yaro dole kuce sai ya xauna da yarinya yana ce maku baya so?" Alhaji Lawal na kallonta da kyau yace "Tunda ni ko d'an uwana ko Ibrahim babu wanda ya ja Abuturrab ya kai sa aka daura masa aure he just have to dance to his music, ko yaki ko ya so haka xai hakura ya xauna da yarinyar, mu ba kananun mutane bane, yanda bai yi shawara da mu ba yaje yayi abu gaban kansa bai isa yace yanxu ma xai juya mu ba, Allah ya basu xaman lafiya" Abba ya gyada kai cikin gamsuwa, Aunty na masu wani kallo gaba daya tace "Ai ko baxan ta6a xuba ido Abuturrab ya cutu ba in dai ina numfashi..." Daga haka ta fice daga parlon fuuu, Ummi ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh Allah yayi abinda ya fi alkhairi, ya sa mu dace" Alhaji Lawal yace "Ameen Hauwa" ta mike ta fita parlon ita ma, Abuturrab dai kansa na kasa, Abba na kallonsa da kyau yace "Kafin gobe kayi duk abinda xaka yi a gidan nan ka tare da matarka, kamar yanda Alhaji Lawal ya fada maka, idan an kwana biyu kuma ka kai ta ku gaisa da mai martaba" Still Abuturrab ya kasa cewa komai, sai da suka yi masa ixinin fita sannan ya mike ya fita xuciyarsa na tafarfasa, Alhaji Lawal yace "This should serve as a lesson for him, next time baxai sake yin abu gaban kansa ba" A bedroom dinsa ya tadda Aunty tana ta jiransa tana girgixa kafa, a sanyaye yake kallonta, Tace "What next now?" A hankali yace "I don't really know Aunty, but ni nasan baxan yi rayuwa da ita matsayin matata ba wllh" Aunty tace "Toh dama ina hakan xai yiwu, a ina xaka xauna da ita bayan ga Aneesah, uban me xaka ci da ita?? kuma idan ka saketa sani xa su yi?" Ya girgixa kai yace "That's what i have in mind Aunty, xan saketa babu wanda xai san hakan sai ke a gidan nan, quite alright xan tare da ita gobe din amma ba matsayin matata ba wllh" Aunty tace "Ai xaman naku ne bana so kwata kwataaa Abuturrab" Yace "Aunty a hankali ake bin komai" Tace "Toh da dai ya fi, don wllh abun dariya xaka xama gun colleagues dinka da yan uwanka, wa ka ta6a jin yayi irin wannan auren? Auren ma na yar talaka" A sanyaye yace "Na sani Aunty" Ta nufi kofa tace "Ba dai tarewa suke so ba, xaka tare din da ita sannan ni xan san abun yi" Daga haka ta fice a fusace, ko ba komai Abuturrab na samun relieve tunda akwai warce ke supporting dinsa dai. Daren ranan Umma ta kirasa yana kwance sai tunane tunane yake yana imagine yanda lkci daya Jiddah ta shigo rayuwarsa tana neman tarwatse masa farin cikinsa da kwanciyar hankali, a hankali ya dau wayar ya kai kunne bayan ya daga, cikin sanyin murya Umma tace "Kana ji na Aliyu?" Yace "Ina ji Umma" Tace "Kayi hakuri ka bi abinda iyayenka suke so sai kaga haske sosai a lamarinka, Yaya ta kirani ta min bayanin komai, ka janye batun saki, kaga dai yau jiddah kwananta uku ko sama da haka a gidan nan, amma har yanxu ban ga aibun yarinyar nan ba wllh Aliyu, gata da hankali da nutsuwa da sanin ya kamata ga uwa uba kawaici da hakuri, baxa kuma a dau lkci ba xata waye don na lura tana da kwakwalwa, taka kaddarar ce a haka ka amsheta hannu biyu Aliyu, kada ka mance Allah ne ya tsaro maku hakan kayi hakuri ka yarda da kaddara my son, duk sanda xaka koma wajen aiki sai ka dinga kawo min ita nan ina gwada mata abubuwa, daga nan din ta dinga xuwa boko da islamiyya, wllh lkci daya xata dawo dai dai taste dinka, nasan damuwarka kenan, in sha Allah xaka yi mamakin wayewar da Jiddah xata yi" Abuturrab yaji baci ransa kawai yake da wannan shawaran da ake basa, ya ma rasa abinda xai ce mata, how on earth suke tunanin xai iya rayuwa da yarinyar nan matsayin mata idan ba cutarsa suke son yi ba, ina duk burinsa na auren wayayyiyar mace me tsafta 100%, ji yayi kamar ya fara mata kuka wannan wacce irin kaddara ce haka ake forcing dinsa ya amsa, a ransa yace no way sai dai duk suyi hakuri, he just have to disappoint them because no amount of their sugar quinted mouth will convince him to live with that girl as wife, he will only live with her as a guardian.... Jin shirun yayi yawa Umma tace "Are u there son?" Ya runtse ido yana jin ransa na dada baci, cikin dakewa yace "Ina ji Umma, nagode Allah ya kara girma" Tayi murmushi tace "Ameen my son, Yaya tace min Abbanka yace ku tare gobe ko?" Cijen lips dinsa yayi yana jin wani mugun takaici, amma ya daure yace "Ehh haka ne" Tace "Toh Allah ya kai mu goben lafiya son, may Allah reward u abundantly for this deed" Ya bude idonsa da ya kada sosai.... forcing his self yace "Ameen" Sallama suka yi ya jefar da wayar kan gado xuciyarsa na tafarfasa ya mike xaune ya rike kansa. Washegari Saturday Umma na xaune dakinta tana kallon Jiddah dake juya kayan hannunta ta kasa sawa, jira take ta sa kayan ta gyara mata gashinta da ta sa ta wanke, murmushi Umma tayi da ta lura kunya ce yasa take hakan, sabon kaya ne da ta dinka ma Ramlah, sae ya kasance Ramla bata xo gidan ba har sannan shine ta ba Jiddan ta sa, mikewa tayi ta fita dakin, Jiddah ta bi ta da kallon gefen ido, sae a sannan ta fara sa kayan da sauri, wani kunya na musamman Allah yayi mata ita kam, komai da Umma ta bata ta saka sabo ne, sosai riga da skirt din ya amsheta kamar don ita aka dinka, kallon kanta ta dinga yi a madubin dakin tunda take iyakar atamfar da ta ta6a sa wa na dubu biyu ce, lkcn ko Ahmad ya kawo mata atamfa me tsada sae Hansae ta amshe ta siya mata roba roba ko half cotton, yau kam ga tsadadden atamfa ta saka duk da bata san me tsadan bane ba ma, bayan wani lkci Umma ta dawo dakin, sosai hankalinta ya kwanta ganin powder kawai jiddah ta shafa a fuska sai kwalli, ta bar mata har kayan kwalliya kawai don taga irin kwalliyan da xata yi sae gashi alama ya nuna iyakar kwalliyarta kenan ba irin na yan kauye take yi ba a lafta ja gira da jan baki, ta madubi take ta kallon jiddah da ta kasa kallonta, Jikin Umma yayi sanyi ganin irin kyan Jiddah, wai ma tun bata waye ba kenan, kuma jikinta bai fara samun hutu yanda ya kamata ba, ae balarabiyan Africa xa ayi a nan, a hankali Jiddah ta juyo tana kallon Umma, Umma ta sakar mata lallausan murmushi tace "Kinyi kyau my daughter" Jiddah tayi murmushin karfin hali, Umma ta xauna tace "Taho ki xauna in gyara maki gashin" Jiddah ta karasa ta xauna ta janye hulan Siyama dake kanta, Umma tace "Idan kin wanke gashi bari ake ya bushe kafin a sa hula kin ji?" Kai kawai Jiddah ta gyada mata, Unma ta fara taje mata dogon gashin nata, murmushi Umma tayi ganin tsayin gashin Jiddah a ranta kuwa tunani take ko ruwa biyu ce dai ita, sosai gashinta ke da kyau da tsayi sai dai babu gyara, Umma ta xuba mata man kai me yawa a gashin da ya dinga sheki da kamshi sannan ta yi mata parking da ribbon, mikewa Jiddah tayi tace "Nagode" Umma tace "Ki daura dankwalin yanxu" Jiddah ta dau dankwalin amma ta kasa daurawa, Siyama Umma ta kira tayi mata daurin, Siyama sae murmushi take tace "Kinyi kyau" xuwa yanxu har Maman Abdallah tasan matsayin jiddah a gidan, sae kusan karfe sha daya Umma ta bar gidan xuwa gidan yayarta da Jiddah, well ironed Hijab ne nude colour har kasa jikin Jiddah, kasancewar akwai kalan a jikin atamfar jikinta, sanyayyen kyau tayi, Hijab din yayi matukar amsarta, Driver ne ya kai su gidan don Ahmad kin amincewa yyi he knows definitely Abuturrab will be mad at him wato da shi xa a kai masa mata......
Chapter 39 · 0% Book details