Sashe 30
Jiddatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abuturrab ya dauke idonsa hade da daure fuska yana tafiya, murya can kasa Jiddah tace "Ina yini" Bai kara kallon inda take ba balle ya tanka ta, tafiyarsa kawai yake kamar bai ji ta ba, Ta kalli Ahmad da ya shigo compound din shi ma, ta sauke idonta tace "Ina yini?" Murmushi yayi yace "Lafiya lau, sannu da aiki" Juyawa tayi tana kallon ruwan da take jiran ya cika, Ahmad ya bi bayan Abuturrab da har ya kusa main entrance din gidan, babu kowa parlon da Ahmad ya shiga sai kamshin girki dake tashi alamar ana girki a kitchen, bedroom dinsa ya nufa ya tadda Abuturrab a kwance idonsa a lumshe, ya karasa ciki ya kulle kofar yana kallonsa yace "Are you alright?" A hankali Abuturrab ya bude idon sae dai bai ce komai ba, cike da karfin hali ya mike xaune looking so dumbfounded, Ahmad ya xauna yana facing dinsa with seriousness yace "Tell me what is happening Captain, you look disturbed" Abuturrab ya shafa kansa ya lumshe ido wishing all this nonsense would turn out to be a dream, kara bude ido yyi, gathering much courage yace "I am in trouble Ahmad" Tuni yanayin Ahmad ya sauya, ya kafe sa da ido, can yace "Tell me what is it, me ya faru??" Cikin sanyi Abuturrab yace "Yes i will, amma kuma mafita nake nema a wajenka don Allah, and this should be a secret between just i and you for now plsss" Shi dai Ahmad kallonsa kawai yake waiting to here what is this that's weighing down his frnd har haka, Abuturrab yayi kasa da murya da kyar ya fara magna yace "Yarinyar da kake siyan awara wajenta a hayi, u remember her right?" Bude ido Ahmad yyi sosai yana kallonsa yana jiran jin abinda ya sameta, A hankali Abuturrab ya shiga basa labarin tun daga xuwansa siya ma Umma awara sanda bata da lafiya, abinda ya faru a ranan, har ixuwa yanxu da suke xaune tare da Ahmad a daki, Abuturrab ya share xufan goshinsa yana kallon Ahmad da ya bude baki for almost five minutes now ya kasa rufewa, Abuturrab ya hade rai yace "Don Allah ka daina kallona haka Ahmad ka bani mafita, find a way out for me, i am stuck, ban ta6a shiga rudani iya rayuwata kamar na wannan lokacin ba, what have i done to my self daga taimako??" Sae a sannan Ahmad ya kulle bakin da sauri, wato kawai sae yake ganin labarin da Abuturrab ya basa kamar tatsuniya, or is he dreaming?? Ya kifta ido kusan sau hudu sannan ya kafe Abuturrab da ido, he is finding it hard to believe all what Abuturrab said now, as if counting his words yace "Wait Captain... Wllh kamar fa ban fahimce wannan gajeran labarin nan naka ba, i am confus...." Captain yyi tapping dinsa on a serious note yace "You just have to believe all what i said, duk abinda na gaya maka hakan yake stop confusing ur self" Ahmad na nunasa da yatsa cikin wani expression yace "Are you for real Aliyu??" Abuturrab ya kafe sa da ido regretting everything from the start, Ahmad ya buda ido sosai yana kara digesting din lamarin with shock, he knows Abuturrab have a soft heart, a very soft heart kuwa, yana damuwa sosai da matsalan da ba tasa ba, he prioritized damuwar wasu kan nasa, but he never thought ya kai wannan extent din, bai ta6a tunanin Abuturrab can go this deep ba, what is baffling him more is yanda this time around taimakon nasa yyi sa ga talaka sosai, don Ahmad bai ta6a ganin yayi stressing kan lamarin local people ba, tsakaninsa da su sadaka if the need arize, babu wani magana me tsayi dake hadasa da su, Abuturrab ya hade rai ganin irin kallon da Ahmad ke masa yace "Nayi kuskuren gaya maka damuwata ne da ya sa ka min shiru Ahmad? Don't u have anything to say to me pls?" Lkci daya yanayin Abuturrab ya kara sauyawa gaba daya, sai yake jin wani sabon xaxxabi xai rufesa, da kyar Ahmad na nunasa yace "You mean you are married now without our knowledge Captain??" Cakumosa Abuturrab yyi a fusace yana huci yace "Wannan kake kira da aure? Haka ake auren dama? Mahaukaci ne ni da xan amince nayi aure yanxu" Ahmad yyi iya kokarin ganin bai yi dariyar da ya taho masa ba ganin how furious Abuturrab was, Turasa Abuturrab yyi ya mike yana jin xufa na keto masa yace "Ka gaya min meye abun yi ynxu, i have never been this confused all my life, what have i done to my self, taimako fa kawai nayi kokarin yi...." Lkci daya idonsa ya kada ya dawo ya xauna ya rike kansa, Wani tausayinsa Ahmad ya ji har ransa, hakan yasa kawai ya kawar da dariyar dake cin sa gaba daya a xuciyarsa, ya kwantar da murya yace "let's talk brother" Abuturrab ya dago da idanuwansa da suka yi ja yana kallonsa, Ahmad yyi shiru yana tunanin yanda Abuturrab yayi making fool out of him, ko da wasa bai ta6a gaya masa abinda yake yi ba sai da abu ya 6aci, har da raina masa wayo wai shu murhu yake gani a hayi, wani boyayyen ajiyar xuciya ya sauke yyi kasa da murya yace "before i say anything just tell me what u have in mind now about this issue?" A hankali Abuturrab ya kai hannu aljihunsa ya fiddo farar takarda da biro yana kallon Ahmad, Ahmad ya buda ido sosai, lkci daya ya girgixa kai yace "Nooo.... This isn't a solution, idan ka rubuta takardan nan dole gida xata koma ga axxalumar step mum dinta, kaga anyi ba ayi ba kenan, and at the end wannan mahaukacin kilan yace sae ya aureta..." Abuturrab yace "But I can't sleep in peace again today in har ina tuna auren warce ke kaina, baxan ta6a samun nutsuwa ba matsawar ban aiwatar da haka ba, me of all people fa?? Where will i start from with that girl, me xanyi da ita a rayuwata?? Ko a mai aiki wllh wllh wllh baxan yi employ dinta ba, baxan bata aiki ba a gida na dai, western education zero, islamic education zero, wayewa zero, tsafta zero, mu'amalat zero, kyau zero.... Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ahmad dake ta kallonsa bbu ko kiftawa ya girgixa kai yana d'an murmushi yace "A bangaren kyau kuma ka so kanka Captain...." a mugun fusace Abuturrab ya fixgosa yace "What the heck.... Kyau xan ci?? Tsaftar fa?? Ilimin fa?? Wait wai kai Ahmad kana tunanin no matter what xan iya xama da local yarinyar nan a matsayin matata? Noo plss... God forbid, this is more like an abomination to me, idan na sake kwana da auren yarinyar nan a kaina yau wllh nasan gobe xan iya xarewa a wuce dani psychiatry" Ahmad ya lumshe ido ya bude yace "Duk na fahimce ka, amma idan ka saketa ynxu Captain ka gaya min meye makomarta? Ina kake son taje? Kasan xamanta tare da maigadin gidan nan da matarsa ba abu bane da xai ja lkci coz daki daya ne da su" Abuturrab ya lumshe ido ya bude yace "I don't care anymore, saninta da tausayinta ne duk ya ja min plight da nake ciki ynxu..." Ahmad yace "Ohk Now tell me, after the divorce what next, ya xa kayi da lamarinta? Kaga tamkar ka lalata aikin ladan da kayi ne daga farko har karshe" Abuturrab na masa wani kallo yace "What are you insinuating now? Kar in saketa kake nufi ko me?" Ahmad ya daga hannu da sauri yace "Aa ni bance haka ba" Abuturrab ya ja wani tsaki yace "Xan saketa, kuma xan ci gaba da mata taimakon da nayi niyya" Ahmad yace "Good, ta yaya?" Abuturrab yace "Under my roof" Ahmad yace "Elaborate plss" Abuturrab yace "I'm thinking i will have no choice but to explain everything that transpired to my Dad, xan ma Abbana bayanin komai, xan kuma kai sa har gun me anguwan, i don't want to look foolish, you get? Then he can explain everything to Ummi coz ni baxan iya ba...." Ahmad ya katse sa yace "You are confusing me, kai da kake da intention sakinta yanxu me xai kai magana kuma kunnen Abba?" Abuturrab yace "Don nace xan saketa ba yana nufin ai baxan yi duk abinda nayi niyya a kanta ba, wllh xan saketa without anyone's knowledge, daga ni sai kai ne xa mu san babu aure tsakanina da ita, amma she will be under my care xan kula da ita har sanda xata samu me aurenta" Ahmad da ke ta kallonsa baki bude yace "Under ur care as how?? a gidanku xaka ajiyeta kenan?" Abuturrab ya girgixa kai yace "A gidana dai" Wani tsaki Ahmad ya ja yace "See the way u are talking like an illiterate plss, ba matarka ba ba komai ba xaka ajiye a gidanka kuna rayuwa tare Captain, ko dai nine ban fahimce abinda kake nufi ba, ka min bayani yanda xan gane" Abuturrab ya masa wani kallo yace "Toh me xamanta a gidana xai kara ko xai rage? Did i look like someone that have anything to do with that girl? Haba Ahmad, don dai ta kwana ta tashi tayi girki ta ci abinci ta tafi boko ko islamiyya, xamanta a gidan nan da rashin xamanta duk daya to me, Monday to Friday ina gun aiki, na dawo sunday and Saturday, wait tell me what u have in mind first" Ahmad yace "Gaskiya baxan yarda da wannan rashin tunanin ba, kana cikakken namiji ka xauna gida daya da mace...." Mikewa Abuturrab yyi looking super angry yace "Amma ka gama da ni Ahmad, mace me tsafta iya tsafta ina xulumi da tunanin yanda xanyi tarayya da ita balle wannan, haba.. haba wannan xagina kayi wllh, ta ina xan fara abinda kake tunani, did you know who i am kuwa Ahmad, me xanyi da warce tayi tsaftar yarinyar nan sau biyar ma balle ita" wani kallo kawai Ahmad ke yi masa Abuturrab yace "You just insulted me wllh, and i am seriously not happy about it" Ahmad ya tabe baki ya ki basa amsa, Abuturrab yace "Sabida wannan kaddaran da ya fada min