← Book details Hooriyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 17

Sashe 9

Hooriyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abiee ne tuntube shi sannan ya turo musu number Daddy'n su Hooriyah tunda ya sanar da shi zai turo masa baƙi ya basu dama suzo Ranar Asabar.

Ranar Asabar bayan La'asar suka je bayan ƴan gaishe gaishe suka sanar da shi abinda ya kawo su yaji daɗi sosai dan Yasan Zaaheed tun da daɗewa yaron kirki ne nan ya amince yace a turo shi...

♡♡♡
♡♡♡
✭✭✭
♡♡♡
♡♡♡

A bangaren Hooriyah komai yana tafiya dai-dai yanzu bata da wani damuwa ta fawwalawa Allah komai ta ɗauki ƙaddara sai tayi two weeks bata je gida ba sai dai suyi waya dasu Mami kowa so yake ya faranta mata suna zaune lafiya da Aunty Sajeedah.

Tunda Aunty Sajeedah tace mata Yayan ta na neman ta take jin wani iri sau uku tana attempting tafiya side ɗin sa sai ta kasa ta rasa dalili har aka idar da Sallah bata je ba. Turo kofar ɗakin aka yi "Yanzu dama ba kije kiran da yake Miki ba, kina zaune a inda na barki, maybe ko Sallah ma baki yi ba"

"Har anyi salla?"

"Tun ɗazu gani nayi ba kya Palour kuma shima bai dawo daga Masallaci ba nasan kina ɗaki baki je ba"

"Tsoron Zuwa nake, kawai ji nake gabana na faɗuwa"

"Allah yasa ba Su Mami ne suka ce na koma gida ba, wallahi bana son Komawa"

"Ke da baki je kinji mene ba har kinyi hukunci"

"Amma ke zaki rakani gaskiya, in yace in koma Dan Allah ki sa baki ya barni"

"To naji, tashi kiyi salla"
Jiki ba ƙwari ta tashi ta nufi Toilet Alwala tayo tazo ta tada Sallah bayan ta idar ta kalle ta
"Tashi muje Koh"

"Jeki zanzo daga baya"

Rau tayi da ido sannan tace

"Amma ai ba muyi haka da ke ba My Aunty"

"Haba Hooriyah sai abu kike kamar ƙaramar yarinya ko Fudail ba zai yi haka ba"
Bata rai tayi da kyar ta lallaɓata ta tafi ita kuma tayi gurin yaran ta"

✿✿✿✿ ✿✿✿✿

Zaune ta same shi yana karanta Jarida Sallama tayi ta nemi guri ta zauna a ciki ya answer bai ce mata komai ba. kana ganin ta kasan a tsorace take sai da tayi gurin minti Goma sannan yace

"Sai yanzu kika ga damar zuwa kenan"

"A'a naga an kusa tada sallah ne Shiyasa na zauna sai da nayi Sallah sannan na taho"
Jinjina kai kawai yayi

"Daddy ne yace gobe kije yana son ganin ki"

"Shikenan abinda nake gudu ya tabbata" take faɗa a ranta

"Me kike gudu?" Ya jefo mata tambaya, da sauri ta lalle shi "yaya ba magana nayi ba"

"Magana ce akan Auren ki ba wani abu ba, karki saka wa ranki damuwa, Dan har Iyayen yaron sunzo sun tambaya kuma Daddy ya basu dama"

A firgice ta kalle shi ɗan bata taɓa kawo maganar Aure a ranta ba ta riga data soke shi a rayuwar ta ba zata ƙara kula kowa ba balle har a samu damar yi mata Abinda Zaid da Anisah suka mata magana ta fara yi masa

"Yanzu Yaya har zaku iya ƙara bawa wani dama kuce yazo gurina, kun manta abinda su Zaid suka min dududu wata nawa da har zaku manta"
"Ni a ganina ba zaku ƙara bawa wani dama yazo gurina ba"ta faɗa Muryar ta na rawa........✍️

# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯

Jiya nace zanyi posting amma ban samu dama ba ɗan Yayana ne Allah yayi masa rasuwa Allah ya jikan shi ya gafarta masa tare da Al'ummar Musulmi baki ɗaya👏

Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan

Follow My Pages

Arewa Books: https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1

Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1

09047574404

WhatsApp only

Comments & Share Fisabillah🥰👏

𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️
[5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: https://chat.whatsapp.com/InjFDl8g9KiCk5F8oos5Yz

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡

𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽

𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷

тԋє ɯɾιтєɾ σϝ

*ʂιʅαɾ ɯαყα*

𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡

Follow My WhatsApp Channel

https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466

بسم الله الرحمن الرحيم

𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️

𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟑𝟏&𝟑𝟐

__________________________________________________________________

Tausayin ta ne ya kama sa duk sai yaji babu daɗi da Daddy ya sani sun fara tuntuɓar ta kafin ya amince magana ya fara mata cikin kwantar da murya

"Daddy ne ya yanke shawarar, Kiyi haƙuri ki bi umarnin sa kinji Allah yasa haka yafi alkhairi, Yace gobe in Allah ya kaimu kije" magana zata yi masa yayi saurin ɗaga mata hannu

"Hooriyah ya isa haka tashi kije da safe sai ki shirya in sauke ki kafin in tafi aiki"

Tohmm kawai tace ta tashi ta fice.

Da safe Gurin goma ta gama shirin ta tana zaune jiran sa da ganin ta kasan tana cikin damuwa yana gamawa suka fice Yana sauke ta ko shiga cikin gidan bai yi ba ya tafi sai ya dawo zai shigo.

💫💫💫💫 💫💫💫💫 💫💫💫💫

Cikin Gidan ta shiga ba kowa a Palour da alamun mutanen gidan duk suna ɗaki basu fito ba Motsin da taji a kitchen ne yasa ta nufar gurin Mai Aiki ce kaɗai a ciki tana ta kai kawo

"Baaba Barka da Safiya, Ina su Aunty?" Tace mata

"Kece tafe da safiyar nan, Barka kadai, Mami tana Bangaren Alhaji, Aunty kuma tana Ɗaki bata daɗe da shiga ba" ta bata answer.

"Thom idan sun fito kice musu ina cikin ɗaki" cewar Hooriyah

"Insha Allah zan sanar musu" ta faɗa mata, wucewa ciki tayi. Ɗakinta ta nufa shiga tayi ta nemi guri ta kwanta bata jima ba ta tashi waya ta ɗauko kira ta shiga yi ringing biyu aka ɗaga gaisawa suka yi

"Na zata ba zaki ɗa ga ba ai, ya fadil?"

"Ashe kin san laifin naki, Fadil yana nan qlau" cewar Khaleesat

"Anjima zan shigo"

"Kinzo gida yau kenan, Ashe kina son Goge laifin naki"

"Ban daɗe da zuwa ba, mun kwana biyu bamu gaisa ba, sai na shigo"

"To Allah ya kawo ki lafiya"

"Amin, sai anjima" ta kashe wayar.

Tashi tayi ta fito palour ta samu sun fito suna zaune da alamu ita suke jira itama zama tayi ta fara gaida su

"Ashe Da wuri ya kawo ki" Aunty ta faɗa

"Ehh Da zai fita muka taho tare inya dawo yace zai shigo"

"Ai Yayan ku baya fashin zuwa kullum sai yazo"

"Bari mu baku guri, in kun gama kizo za muyi magana" cewar Aunty

"Insha Allah"

🤙🤙🤙

Zaune take a gaban Daddy magana ya fara mata:

"Da fatan Ya sanar dake abinda yasa na kira ki"

"Eh Daddy"

"Na ba shi dama yazo ku ga juna Lecturer ne a makarantar ku yace anan ma ya ganki, Mahaifinsa Abokin na ne a da"
"Daga yanzu zuwa kowane lokaci zaki iya ganin kiran sa"

"Allah ya bani ikon yi maka biyayya" kawai tace

"Amin, Allah yayi Miki Albarka, Ni zan fita in kin shiga ki sanar da su"

"Ameen Daddy, tohmm sai ka dawo Allah ya tsare Hanya"

Ameen yace

❉❉❉❉ ❉❉❉❉❉ ❉❉❉❉

ABUJA

Zaune suke ita da wata budurwa daga gani kasan ƴar ta ce kamar su ɗaya ranta a ɓace daga ni kasan wata maganar suke yi wadda bata jin daɗin ta

"Ammi na faɗa Miki ba tun yau ba ki ƙyale su kinki, Ni banga amfanin abinda kike yi ba"

"Husna nace ki ƙyale ni dasu, wai kamar ni a ce zai dawo ba'a sanar min ba, sai na Kashe shi kowa ya huta" ta faɗa tana yin kwafa

"Ammi baki haife shi ba, mahaifiyarsa na raye ba mutuwa tayi ba, dan zai dawo dole sai an sanar da ke?. Ki daina irin furucin nan kar wani yaji ya zame mana matsala, Ɗan uwan mune fa, wallahi bana jin dadi in kina faɗin zaki kashe shi"

"Husna Ni kike faɗa wa waɗannan maganganun?, Na kira ki ne dan ki kwantar min da hankali amma kinzo kina faɗa min wasu maganganu marasa daɗin ji"

"Tashi ki fice min daga nan" ta faɗa tana nuna mata Hanyar fita

"Ammi ban fadi wata magana dan na ɓata Miki rai ba, Kiyi haƙuri in na faɗi abinda bai Miki daɗi ba"

"Ba zaki fitan ba kenan?, To Ni bari in bad Miki ɗakin" ta faɗa tana ƙoƙarin mike wa, da sauri ta tashi ta fice mata a ɗakin. Ta rasa me yake damun mahaifiyar nan tata da komai na gidan sai an sanar mata in ba'a faɗa mata ba ta Ringa ƙorafi "ya kamata in fara binciken mene dalili" take faɗa cikin zuciyar ta............✍️

# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯

Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan

https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I

Follow My Pages

Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1

Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1

09047574404
WhatsApp Only

Comments & Share Fisabillah🥰👏

𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️
[5/9, 4:10 PM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡

https://chat.whatsapp.com/InjFDl8g9KiCk5F8oos5Yz

𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽

𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷

тԋє ɯɾιтєɾ σϝ

*ʂιʅαɾ ɯαყα*

𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡

Follow My WhatsApp Channel

https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466

بسم الله الرحمن الرحيم

𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️

𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟑𝟑&𝟑𝟒

_______________________________________________________________________________________

Tana barin gurin Daddy ta nufi ɗakin Aunty suna zaune a Palour'n ta da Mami

"Magana dama zamu yi dake Hooriyah" Mami ta faɗa mata

"Mami inaji"

"Yayan ku ya faɗa Miki Maman ku Safiyya tazo?"

A rikeɗe ta kalle ta gumi na keto mata
"Tazo? Me tazo yi kuma?"

"Tabbas Ta ƙara zuwa, Maganar Auren ki da Sulaiman ce ta kawo ta, tace ba zata taɓa haƙura ba har sai kin Aure shi. In Kuma ba ki Aure shi ba dole kiyi Aure a kankanin lokaci"

"Sulaiman kuma Mami? Ai na zata an gama maganar, Mami ya zata ce haka bafa ita take riƙe Ni ba"

"A gurin kine ta wuce amma ita a gurin ta tana nan, Kuma ta taso da ita" shiru tayi Aunty ce ta cigaba da magana

"Hooriyah wannan yaron da yazo Indai na gari ne ki amince masa kafin ta ƙara dawowa"

"ki bashi dama kinji"Aunty ce tayi Maganar

"In Sha Allah Aunty zan bi duk abinda kuka zaɓa min, Allah ya sa Haka ne yafi Alkhairi"

"Ameen, yanzu ki huta Kafin Yayan ku ya dawo ku tafi" cewar Mami

"Ina so Zanje Gidan Khaleesat bayan La'asar mun daɗe baku haɗu ba"

"Khaleesat yarinyar kirki Last week ma ta shigo ai, Allah ya kaimu" Aunty ta faɗa

"Bama ta faɗan tazo ba, Amin"

"Ai nasan ba lallai ta sanar Miki ba"

Miƙe wa tayi tana cewa"Bari inje in taya Baaba Aiki"
Chapter 9 · 0% Book details