← Book details Hooriyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 17

Sashe 16

Hooriyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin data isa gidan babu kowa shiru gidan a palour kawai ta zauna tana jiran mutanen gidan su fito bata wani jima ba sai ga Aunty ta fito daga ɗakin ta zama tayi tana Facing ɗin ta fuskar ta fess bata nuna komai ba

"Safiyya yau kece a gidan namu da rana tsaka"

"Nice kamawa tayi zuwan, da fatan wanda nazo gurin sa Yana nan"

"Yaje ɗaurin Aure bai dawo ba"

"To bari in jira ya dawo" ta faɗa tana hararar Aunty. Ita ma tashi tayi ta bata guri dan tun lokacin da suka samu labarin ita ta raba auren Hooriyah take jin ba daɗi a lokacin taso Daddy ya barta taje mata da ƴan sanda an kama ta amma yaƙi, bata da lokacin raba hali yanzu ga ƴan ɗaurin Aure da zasu dawo kar a shigo da ɓaki taji kunya dan Safiyya ko a jikin ta indai abin kunya ne.

Har bayan Uku tana zaune jiran shigowar Daddy amma babu shi babu alamar sa ga matan gidan yau iskanci suke ji ko ruwa ba'a kawo mata ba tashi tayi ta ƙara duba ƙofa a karo na barkatai ko zasu shigo sai ga ƙarar Horn ɗin su wata bahaguwar ajiyar zuciya ta sauke fita tayi ta tsaya a ƙofar palour yadda yana shigowa zaici karo da ita suyi Maganar da zasu yi ta wuce suna parking ya hango ta bai kawo komai a ransa ba ya fito ya ƙara so kusa da ita

"Yaya sannu da dawowa tun ɗazu nake jiran dawowar ka" ta faɗa tana tsugunawa ƙasa
"Ina wuni, fatan mun same ku lafiya"
Shi abin ma dariya yaso bashi Safiyya da ko abu tazo nema bata tsuguna wa ta gaishe sa amma yau har da tsuguna wa

"Tashi mu shiga daga ciki Koh" ya faɗa yana wucewa

Dariya Khaleel dake kallon su ya kwashe da ita Abduljawwad ne ya juyo yana cewa "lafiya" "yaya wani abin dariya na gani, Aunty Safiyya ce da durkusawa yau dan zata gaida Daddy"
"Ina ruwan ka, in ta hango ka fa ga jama'a tazo tayi ta rashin mutunci, ka wuce muje" ya faɗa yana nuna masa hanya. Sim-sim ya shige girgiza kai kawai yayi shima ya bishi.

A cikin palour kuwa Aunty Safiyya ce zaune a ƙasa Daddy yayi yayi da ita yau ta hau kujera amma taƙi tace gaba yake da ita yana sama tana sama ai ba zai yiwuwa ba dole ta bashi girman shi {😂😝}

"Yanzu yaya sai ka Aura wa Hooriyah wani bare bayan kasan Sulaiman yana sonta" ta faɗa tana share kwalla

Kallon ta ya sake yi shi ya rasa abinda zai faɗa ma tun da ya shigo take share masa hawaye can sai yace "Ke yanzu Safiyya baki ji kunyar zuwa gida na ba, har da wani zancen Sulaiman kike?"

"Yaya dan zanzo gidan ka sai inji kunya sai kace wadda tayi wani abu" cewar Aunty Safiyya

"Bari kiji yau duk abinda kika yi wa Hooriyah an sanar min na sharrin da kika yi mata, na ɗauka ko wani kika ji ya fadi haka zaki yi masa faɗa Hooriyah ƴar kice amma baki ɗauke ta a matsayin dana ɗau Sulaiman ba. Ki tashi ki bar kin gida bana son na ƙara ganin ki balle ƴaƴan ki a cikin gidan nan"

A firgice ta kalle shi dan bata yi tsammanin abinda tayi zai dawo kunnen sa ba "wallahi Yaya ba haka bane Sulaiman na matuƙar son Hooriyah, sharrin Shaidan ne kayi haƙuri nayi nadama"

"Haƙuri! Safiyya hakuri kike so nayi to bazan haƙura ba ki bar min gida yanzu" ya fada yana fita daga Palour.

Ji take kamar ta kurma ihu ko zata ji sassauci a zuciyar ta bata yi tsammanin zai samu Labarin ita ta rusa auren ba gashi yanzu ta Auri wanda basu taɓa harsashe ba ina zata saka kanta ita Safiyya dama shine yake taimaka mata yanzu yace babu shi babu ita Sulaiman ba wani abin arziki yake yi mata ba shima wani lokacin ita ke taimaka masa. Da kyar ta tashi ta nufi gidan ta dan ji take kamar zazzaɓi ya kama ta.

*Dama Hausawa sunce in zaka gina ramin mugunta ka gina shi dai-dai da kai. yanzu wa gari ya waya?*

💫💦🖤

ABUJA

Sajeedah ce ta turo ƙofar ɗakin a kwance ta tarar da ita tashi tayi ta zauna ganin Sajeedah ce ta shigo da sauri ta ƙara so kusa da ita rungume ta yi bata san lokacin da kuka ya kufce mata ba tana jin tausayin ta sosai. Ɗago ta tayi daga jikin ta ganin fuskar ta da hawaye yasa ta ce mata " me ya faru Aunty?, Ko wani ne ya mutu?"

"Kukan daɗi nake Hooriyah, Yau dai Allah yayi Hooriyah Aunty ta zama Amarya" ta faɗa tana share hawayan

"Amarya kuma, like how?"

"Yes kamar yadda kika ji"

"Ban gane ba Aunty"

"Zaki gane ne soon, ki shirya zamu bi Flight ɗin 6 zuwa Kano, gobe zamu dawo" ta fadi tana tashi tazo buɗe Ƙofa ta ƙara ce mata

"Kano kuma? Kuma gobe mu dawo"

"Kin fiya tambaya fa, ki bari in munje zaki ji komai ai"

# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯

Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan

https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I

Follow My Pages

Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1

Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1

09047574404
WhatsApp Only

Comments & Share Fisabillah🥰👏

𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️
[5/31, 10:01 AM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡

https://chat.whatsapp.com/L3tt0Q6Zcqe3eeCa3cXcAG

𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽

𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷

тԋє ɯɾιтєɾ σϝ

*ʂιʅαɾ ɯαყα*

𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡

Follow My WhatsApp Channel

https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I

بسم الله الرحمن الرحيم

𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️

𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟓𝟕&𝟓𝟖

Second to the last Page

————————————————————————————————————————

A bangaren Kareema kuwa ƴaƴan ta ta zaunar su bata shawara yadda kowa zai yarda da ita a gidan a daina zargin ta Shawara ta gari suka bata ta fara zama da kowa lafiya a gidan ba tashin hankali.

🤍💥🖤

Suna sauka daga Airport direct gidan Daddy suka yi gidan cike yake da ƴan uwan ta da matan yayyanta da ƙannen ta gaisawa suka yi ta shige ciki ba wanda yayi mata Allah ya sanya alkhairi dan duk sun san bata sani salla tayi ta kwanta ba jima wa sai ga Khaleesat ta kira ta sun daɗe suna waya sannan ta katse cigaba da kwanciyar ta tayi dan babu abinda zata yi.

Gurin goma sai ga Aunty ta shigo sai a lokacin suka gaisa dan da suka zo bata nan ita da Mami suna part ɗin Daddy. Ce mata tayi tazo inji Daddy sai da taji wani iri dan indai ba magana nace mai muhimmanci Daddy baya yin ta da daddare sai da safe tashi tayi suka tafi.

A palour ta tarar da duka Yayyan ta da Mami suna gurin Daddy gaishesu su tayi bada ɓata lokaci ba Daddy ya fara magana da cewa
"A'isha"

"Na'am Daddy" Tunda taji ya kira sunan ta ta faɗa kanta a ƙasa

"Menene matsayi na a gunki" ya faɗa

Maganar taji ta wani iri amma ta daure ta amsa da "Daddy Kaine Mahaifina"

"A'isha na zaɓa miki kuma kika karɓe shi Allah bai yi za'a yi auren ba yanzu ma mun ƙara zaɓa miki wani har mun Aurar da ke yau"
Wani dumm taji kanta yayi "Aure Daddy yace sun min fa" Waye Mijin? Sulaiman mana zuciyar ta ta bata "kai ina Daddy ba zai taɓa aura min Sulaiman ba" ta bawa kanta amsa ji tayi Daddy ya cigaba da cewa

"A'isha kibi mijin ki sau da ƙafa, kinga duk ƴan uwan ki kowa yana zaune lafiya a gidan sa kece babba acikin su amma sai yanzu Allah yayi naki auren kar inji kar in gani A'isha"
Nan su Mami da Aunty ma suka yi mata nasiha Yayyan ta ma haka. Ta yiwa Daddy alkawarin zama da duk wanda suka zaɓa mata a matsayin miji.

Washegari
Ba wani taro suka yi ba ƴanuwa da abokan arziki ne kawai suka zo sukuku ta yini tana ɗaki sai da rana ne ta fito da aka kira ta da yamma aka shirya amarya da duk wanda yake son zuwa ta sha kukan rabuwa da su.

Tsaya wa faɗa muku tsarin gidan ma ɓata lokaci ne kyawun sa da tsaruwar sa ɗakin ta aka kaita dan Ammi tace a barta gobe sa so gaishe ta yanzu ta huta. A nan gidan Amarya suka kwana washegari zasu yi bikin su a nan da safe suka shirya ta suka kai ta gurin mai martaba sannan aka wuce da ita gurin Ammi suna tare da Mommy da wasu daga cikin matan gidan sun karɓe su an musu tarba ta mutunci sun dau Amanar ta da alkawarin kula da ita. Da rana yini suka yi da daddare aka yi dinner dole anan dangin amarya suka ƙara kwana ba dan sun so ba washegari da safe suka wuce, ita kadai suka bari har lokacin bata san waye mijin ba.

💃💥🥰

Bai shigo gidan ba sai ranar da daddare tunda aka ɗaura auren ya bar gidan ko dinner da suka yi bai je ba iya mata kawai suka yi kayan su.

Yana shigowa direct part ɗin Ammi yayi ba abokin daya rako shi bashi da abokan ma balle su rako shi bata palour sai hadimar ta kawai ya tarar shiga yayi nasiha tayi masa sosai tare da addu'a har kwalla sai da yayi duk da ba barin gidan zai yi ba part ɗin sa yana gidan sai da ta kore shi sannan ya tafi.

Zaune ya tarar da su a ɗaki ita da su Husna ne Sannu da zuwa suka yi masa sai Zainab ta cewa
"Yauwa Yaya dama kai muke jira mu tafi, sai da safe"
Raka su yayi yana kulle kofar ya dawo tana nan zaune alwala ya sata tayi salla raka'a biyu suka gabatar,addu'a mai tsaho suka yi ta neman alkhairi da samun zaman lafiya da haduwar kai a tsakaninsu sannan ya waiwayo ya kama kanta ya karanto addu'ar da annabin rahama ya koyar da mu
'' *Allahumma inni as'aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha alaihi,wa a uzu bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alaihi*'',da salatin annabi ya rufe musu suka shafe tare.

Noor
Chapter 16 · 0% Book details