← Book details Hooriyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 17

Sashe 3

Hooriyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga lokacin Hooriyah da Anisah suka zama ƙawaye bata da wadda ta fita a cikin ƙawayen ta, ko a gidan su an san labarin Anisah amma basu taɓa haɗu wa da ita. matsalar Anisah ta zama tata komai ita take musu tana tausaya musu sosai, ta zama kamar ƴar gidan su kullum ita take maida Anisah gida, duk wata tasa Daddy'n ta kawo musu kayan abinci, in ana yi mata magana abinda take yayi yawa sai tace musu "Allah ne ya haɗa wannan ƙaunar ba mai iya raba ta" "ba kwa jin Tausayin su ne?" ita ce amsar ta kullum a gurin wanda yayi mata magana.

Hooriyah ta nace Anisah sai taje gidan su, Anisah ta shirya Weekend da basu da lecture taje, bata yi tunanin kuɗin su Hooriyah ya kai haka ba, raina kanta tayi da Ajin ta, Kamar Hooriyah ta zauna kula ta gaskiya tayi mamaki. Tun da ta koma gida take bawa Maman ta labarin gidan su Hooriyah har sai da ta gaji sannan ta daina bata.

Sun cigaba da ƙawancen su har yafi na da dan yanzu ita ma Anisah tana zuwa gidan su sosai.

#𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯

Follow My Pages

Arewa Books: https://arewabooks.com/fatimaintisar1

Wattpad: https://wattpad.com/fatimaintisar1

09047574404
WhatsApp Only

Please Share & Comments 🙏

𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ✍️
[5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡

https://chat.whatsapp.com/CmyP8hlqbHtGyhdQ7FVc2w

𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽

𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷

тԋє ɯɾιтєɾ σϝ

*ʂιʅαɾ ɯαყα*

𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466

Follow My WhatsApp Channel

https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I

بسم الله الرحمن الرحيم

𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️

𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟗&𝟏𝟎

𝐌𝐮𝐭𝐚𝐧𝐞𝐧 𝐀𝐦𝐚𝐧𝐚 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐜𝐨𝐦𝐦𝐞𝐧𝐭𝐬 𝐝𝐚 𝐫𝐞𝐚𝐜𝐭𝐢𝐧𝐠 𝐈𝐧𝐚 𝐠𝐨𝐝𝐢𝐲𝐚✯

✫✫✫✫

Zaune suke a palour cards ne a gaban su suna dubawa "Khalisat ya kamata a fara raba IV's ɗin nan Kinga saura sati biyu kar muzo muji kunya"

"Nima tunanin da nake kenan ko gobe mu fara,bari Hooriyah ta ƙara so muji yaushe take da time mu fara fita"

"Yanzu sai mun jira zuwan ta, kawai ki ɗauko mota mu tafi gidan su"

"Mu bari ta ƙara so kawai, Ni ban fiya son driving ɗin nan ba, amma ita bata jin zuwa ko ina driving baya mata wahala"

"Allah ya kawo su lafiya, amma da mun tafi mu tsara da wuri yadda zamu gama da wuri"

"Let me call her, in ba su taho ba kawai sai mu tafi"

"Hakan ma yafi"

Wayarta ta ɗauka ta kiranta ta fara yi a handsfree ta saka ta

"Amarya ba kya lefi, ko in kashe ɗan masu gida, ya akayi?"

"Kin fiye zolaya, ba abinda akayi, kuna ina"

"Gamu a cikin street ɗin ku, mun kusa ƙara so wa"

"Ok sai kun ƙara so" ta kashe wayar

"Da tini kin samu wahala mun tafi bayan suma ga su nan"

"Su ƙara so ɗin dai" duba cards ɗin ta cigaba

Sallama suka yi suka shigo neman gurin zama suka yi

"Hala dai Mommy bata nan"

"Ba kiga gidan kaca-kaca ba, ai kenan kin san bata nan" "Wai harda Amaryar da saura sati biyu Aure amma bata iya gyara gu ba"

"Sarauniyar tsafta ai sai ki gyara, Ni ba wannan ba cards ne ya kawo shine nake tunanin ko gobe mu fara rabo"

"Zumuɗin me kike saura sati biyu fa, gobe fa muna da lectures sai dai ko jibi"

"Me tayi na zumuɗi, kar mu manta da wani a ce bamu da kirki gwanda kowa yazo,Ai da gobe da jibin duk ɗaya Allah ya Kaimu"

"Ameen dai" Miƙa musu cards ɗin suka yi suka cigaba da dubawa.

Sunyi rabon kati lafiya an gama lafiya har an fara shagalin biki anyi Ladies Night ranar Alhamis juma'a da Rana aka ɗaura Aure da daddare dinner sai Ranar Asabar yini da kai Amarya.

✫✫✫✫

Tafiya ta ke yi tayi kyau cikin less ɗin ta babu kwalliya ko ɗigo a fuskar ta amma tayi kyau sosai buɗe motar ta tayi ta shiga Da sauri Zainab ta riƙe murfin motar "Haba Hooriyah ya zaki tafi ke kaɗai bayan kin san kece best friend ɗin ta ai kamata yayi kina motar amarya"

"Kin san bana son harka irin haka Koh?, Abokan Ango su riƙa yi maka kallon raini"

"Sai aka ce Miki duk irin su ɗaya kowa da halin sa, dan anyi mana a wani gurin ai ba lallai ayi mana a nan ba, Kin san AndulFatah yana da kirki ai sai muyi wa Abokansa shaidar ma ai na gari ne"

"In kina son Abu kin dinga kare shi kenan, in na biku inyi Yaya da mota ta? Wa zai maida Anisah gida? Kin san Mama bata barin ta kaiwa dare"

"Ni zan tuƙa motar in zamu dawo sai ki maida ta gida sai ki wuce" "it's okay" fitowa tayi ta mika mata key ɗin motar "Take care, sai mun haɗu, ki kula da Anisah please"

"ok karki damu" ta wuce "Mtwsssss sai kace wata yarinya kullum a kula da Anisah, kamar wata jaririya" motar ta kulle ta koma ciki gurin su, idan sun gama sai su tafi.

Zaune suke a cikin Mota suna jiran Ango da Abokinsa su tafi "Kinga irin abinda bana so, an zo an shanya mu bacin basu gama shirya wa ba"

"kiyi hakuri ayi masa uziri mana kin san mutane ne suka riƙe shi amma da tini mun tafi"

"Mene amfanin ake biki ba'a ga Amarya ba, ni in ana biki na da wuri zanje kowa ya zo akan idona"

"Ce Miki akayi zasu tafi, Allah dai ya Kaimu lokacin in zaki iya" buɗe motar akayi Ango ne ya shigo da abokin nasa "Me ya farunaga duk kunyi shiru"

"Gata nan faɗa takeyi kun daɗe, harda cewa ranar bikin ta kowa a gaban ta zaizo" dariya suka saka gaba ɗayan su

"Hooriyah ayi mana afuwa mana, Wannan tsohon tuzurin ne ya ɓata mana lokaci, Ya kamata kaima kayi Auren nan fa"

"Kaima yaushe ka fita daga sahun tuzuran, Ni ma dai ina ganin na kusa Auren nan dan na samu matar Aure yau"........✍️

#𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯

Follow My Pages

Arewa Books: https://arewabooks.com/fatimaintisar1

Wattpad: https://wattpad.com/fatimaintisar1

09047574404
WhatsApp Only

Please Share & Comments 🙏

𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ✍️
[5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: https://chat.whatsapp.com/CmyP8hlqbHtGyhdQ7FVc2w

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡

𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽

𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷

тԋє ɯɾιтєɾ σϝ

*ʂιʅαɾ ɯαყα*

𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466

Follow My WhatsApp Channel

https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I

بسم الله الرحمن الرحيم

𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️

𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟏𝟏&𝟏𝟐

𝐌𝐮𝐭𝐚𝐧𝐞𝐧 𝐀𝐦𝐚𝐧𝐚 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐜𝐨𝐦𝐦𝐞𝐧𝐭𝐬 𝐝𝐚 𝐫𝐞𝐚𝐜𝐭𝐢𝐧𝐠 𝐈𝐧𝐚 𝐠𝐨𝐝𝐢𝐲𝐚✯

✫✫✫✫

"Haba, a ina take"

"Gata a kusa dani, amma da alama sai kun taya Ni campaign"

"Ba sai mun taya ka campaign ba ma zaka samu shiga Insha Allah" dariya yayi, Ita da yake yi don ita ko ƙala ba tace Ba balle ta ɗago chatting ɗin ta take yi

"Allah yasa"

Tunda suka je yake liƙe da ita duk inda zata yana bayan ta kamar jela har aka tashi daga bikin. Fito wa suka yi daga ciki Zainab ta kalla "ina key ɗina Kinga anyi Isha'i ya kamata mu koma gida, zan ajiye Anisah a gida"

"Ai tare da ke zamu koma, yadda muka zo tare" wani banzan kallo ta watsa masa ɗauke kanta tayi daga gare shi, Zainab ce tayi magana"gashi za'a mai da ke gidan su Khaleesat ɗin ba sai mu haɗu a can ba sai ku tafi"

"Ai daga nan zamu rabu, na gaji sosai wallahi"

"Mu yanzu yaya zamu yi in kika tafi da motar a me zamu koma"

"Da zamu taho ai baki yi wannan bayanin ba, kuzo sai in rage muku hanya sai mu wuce"

"Ai ko baki isa ba, ki samu za'a kai ki Sannan kice A'a" juya wa tayi gurin su Khaleesat "Khaleesat kizo ku saka baki ta biku mana, ma haɗu acan sai ta karɓi Motar"

"Kin san in ta nace akan abu sai tayi ki bata key ɗin sai mu tafi tare tunda ku biyu ne, Babe ka shiga gaba sai mu zauna da su a baya Koh"

"Ya ma fi ai, dan wannan ƴar darun in ta nace sai tayi Abinda take so" suka saka dariya

"Ungo Key ɗin ki, Gobe ma Rana ce" ta miƙa mata "Yafi dai, Good Night bazan shigo da wuri ba gobe, Anisah muje koh"

"To, Sai da safe" mota suka shiga suka tafi. Maida kallon sa yayi kan Ango

"Wallahi Auwal ka kwafsan ban so haka ba gashi sun tafi ko number ta nan karɓa ba"

"Haka yafi maka, Kabi komai a sannu mana"

"Nabi mu tafi Koh" Mota suka shiga duk suka tafi.

Washegari kamar yadda ta faɗa bata zo da wuri ba sai bayan La'asar tazo bayan sun gaisa waje ta fito ta zauna bata daɗe ba sai ga Anisah tazo a kusa da ita ta zauna "Anzo ɗaukar Amarya fa"

"Sai sun dawo, ba zuwa zan yi ba daga baya naje"

"Haba dai, wai me yasa kike haka ne"

"Minti nawa ne a je an dawo" jayayya suka yi tayi daga ƙarshe dai ta haƙura ta tashi ta bita suka fito compound ɗin gidan Duk masu zuwa gidan Amarya sun fito dan Amarya har ta shiga Mota ma Rukayya ce ta ƙara so gurin su"Khaleesat sai neman ki take yi amma dai zaki je Koh" ɗaga mata kai tayi kawai "Amma dai ba'a motar ki zaki ba dan Allah, muje tare mu dawo tare" kallon ta Kawai tayi ta wuce "Yau ciwon ya tashi Kenan, kin dame ta ne Koh" "Eh, da kin zuwa tayi sai da kyar ta tashi" "Allah ya Kyauta, amma in Hooriyah tayi Miki wani abin kamar ki dake ta, muje Koh" Buɗe mota tayi ta shiga kawai ta rufe suma shiga suka yi Basu dade ba suka tafi sun kai Amarya ba jima wa suka taho bayan Ango yazo.

Har compound ɗin gidan aka dawo da su buɗe kofar yazo yi taji ta a lock kallon sa tayi "Malam buɗe min mana" "Zaid nake, magana zamu yi ba zata wuce ta ten mins ba"
Chapter 3 · 0% Book details