← Book details Hooriyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 17

Sashe 10

Hooriyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ke da zaki huta kyau tafi wani aiki, kije kiyi hutawar ki anjima muyi hirar yaushe gamo" inji Aunty

Dariya ta saka sannan ta ce "Bari dai in taya ta daga baya mayi hirar, nayi missing girkin Baaba" ta faɗa tana ficewa.

Kitchen ta nufa gurin Baaba ta tarar har ta kusa gama Girkin hirar yaushe gamo suka shiga yi tana miko mata abu kawai ta ringa yi in ta buƙata bayan ta gama girkin tayi mata wanke-wanke da kyar ta yarda cewa tayi ta huta ita da ba zuwa take yi gidan ba yau kuma tazo ai sai ta huta ba tayi ta aiki ba. Bayan Sun gama suka sha hirar su da su Mami sai da Uku ta wuce sannan ta shirya ta nufi gidan Khaleesat.

A gidan Khaleesat ma Hirar su suka sha har bayan Isha tana gidan sai da Yaya ya kira sannan ta koma gida Fadil har kuka yayi da zata tafi. Tana shiga gida sallama kawai tayi dasu Mami suka tafi sai faɗa yake tayi dare Bacin yasan ba ita kaɗai zata tafi ba.

✨☆★✨☆★✨☆★✨☆★✨

Bayan Kwana Biyu da zuwan ta gida ya kira ta ya mata bayanin kansa a taƙaice kafin ya zo. Taji ya kwanta mata a rai amma taki amince masa har sai yazo ta Ganshi.

𝗔𝗿𝗼𝘂𝗻𝗱 10:00 𝗣𝗺

Saukowa take daga bene waya take duba wa Palour'n shiru alamun duk yaran sunyi bacci Sajeedah ce kaɗai zaune take kallo zama tayi kusa da ita
"Aunty Sannu da Hutawa"

"Yauwa, Har kin sauko"

"Eh Wlh, Har na kwanta nace bari in zo muyi magana kafin kiyi bacci"

"Maganar me zamuyi"

"Zaaheed da Daddy ya turo shi ne yace zaizo Ni na rasa yadda zanyi"

"Eennyyeeh ashe da gaske yake ya shirya in fara shirin Biki"

"Joke apart Aunty"

"Kawai kice yazo mana, mene a ciki kawai sasantawa za kuyi musha Biki"

"Gani nake kamar shima yaudara ta zaiyi Indai yazo"

"Ai baizo ba Koh Balle ki yanke masa hukunci, ki bari yazo sai mu yanke masa hukunci"

"Zan sanar da shi"

Nan tayi ta bata shawarwari tana ƙara mata wayar mata da kai akan Rayuwa har 12 suna palour sai da Yaya ya sauko sannan kowa ya nufi ɗaki. Ko da ta shiga ɗaki bata kwanta ba salla tayi sannan tayi Addu'a Allah yayi mata zaɓin Alkhairi.

💦◆◇💦◆◇💦◆◇💦◆◇💦

𝟑𝐫𝐝 𝗔𝘃𝗲𝗻𝘂𝗲 𝗔𝘀𝗼𝗸𝗼𝗿𝗼, 𝗔𝗕𝗨𝗝𝗔.

Zaune suke a palour su biyu Tsit sai ƙarar A.C ne kaɗai ke tashi shi da wani Babban Mutum ne a zaune a ƙalla zai kai Shekaru 65-70 Fari ne qal kamar Balarabe da gani magana suke mai muhimmanci nisawa yayi Sannan ya cigaba da cewa

"ARSHAD ina ganin nan zaka dawo da zama, jikin nan kamar bai gama warke wa ba"

"Papi na warke zan iya zama a can Insha Allah" wanda ya kira da Arshad ne ya bashi answer

"Bana son kana zama kai kaɗai a gidan tunda mahaifiyar ka ba lafiya ne da ita ba, ba lallai ayi maka komai da kake so ba"

"A'a Papi na fison in zauna a can, ina son gano wanda ya saka min guba ne, nasan tunda na tashi yanzu yana son haɗa wani abun kuma"............✍️

# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯

Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan

https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I

Follow My Pages

Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1

Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1

09047574404
WhatsApp Only

Comments & Share Fisabillah🥰👏

𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️
[5/14, 10:30 AM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡

https://chat.whatsapp.com/InjFDl8g9KiCk5F8oos5Yz

𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽

𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷

тԋє ɯɾιтєɾ σϝ

*ʂιʅαɾ ɯαყα*

𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡

Follow My WhatsApp Channel

https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466

بسم الله الرحمن الرحيم

𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️

𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟑𝟓&𝟑𝟔

__________________________________________________________________

Ta sanar da shi duk lokacin da ya shirya zai iya zuwa bayan sati ɗaya ya zo. Bayan La'asar ya kira ta gashi ya ƙara so. Sajeedah ce tayi wa maigadi waya ya kaishi guest room mayafi ta saka ta nufi guest room ɗin.
Zaune yake yana Facing ɗin Ƙofa Tayi mamakin ganin sa sosai shanye wa tayi bata nuna ba ko a fuska guri ta nema ta zaune nesa da shi gaisawa suka yi cikin mutuncin nan ya fara magana

"Nasan kinyi mamakin ganina duk da baki faɗa ba"
"Kamar yadda kika sani sunana Zaaheed Lecturer ne a BUK nasan duk kin san wannan" nan yayi tayi mata bayanin sa Ita dai nata ji ne dan har yanzu mamakin sa take daga Ehh sai A'a take bashi answer wani zubin tayi masa shiru, bai jima ba yace mata zai tafi ta raka shi har bakin motar sa sai da ya tafi Sannan ta shige ciki.

💣💥

A palour ta tarar da Sajeedah zaune tana yiwa Fudail aiki zama tayi kusa da ita ta rafka tagumi tun shigowar ta tana lure da ita yanayin ta ya chanja Fudail ta tattara wa Littafin sa tace ya shiga ciki zata zo su ƙara sa aikin

"Meya faru na ganki haka"

"Aunty Lecturer mune fa, gaskiya Ni ba zan iya ba bashi da mutunci ko na kwabo"

"To sai me dan Lecturer kune"

"Wlh Aunty ko Lecture zaiyi ya dinga bata rai ga rashin mutunci Ni gaskiya da kyar in zan iya Auran sa"

"In da ya sake fuska yanzu da yazo zaki kula shi ne cewa zakiyi yafiya kula ƴanmata ya kame kansa ma bai tsira ba"
"Sai Kiyi ta yi ai, karki sake yayanki yaji wannan Maganar balle har ta kai kunnen Daddy dan nasan ranki ne zai ɓaci"

"Yanzu kuma sai inyi shiru a cuceni, ba shi da mutunci ko na sisi Wallahi ban taɓa baki labarin abinda yayi wa Anisah ba, one minutes after ya shiga class ta shigo amma korar ta yayi yana faɗa mata magana"

"Anisah daban ke daban" dafa kafaɗarta tayi sannan ta cigaba da cewa "ki dai bashi dama har yanzu ki na da chance in Kinga halin shi ɗaya ne dana makarantar sai ki sanar da Daddy"

"Ai shikenan, amma"

"Amma me kuma kiyi shiru kawai"
Kwanciya kawai tayi a kujerar ba tare da ta ƙara ce mata komai ba

Befi sau biyu zuwa uku yayi yana zuwa ba aka kawo kuɗi sai dai waya da kullum yake kiranta ba fashi duk da har yanzu cewa take bata sonsa amma tana ganin zata iya Auren sa. An saka Biki six Months ya kama bayan sunyi Graduation da wata biyu za'a yi bikin.

💕 ✿★ ❤️ ✿★💕

Shirye-shiryen exams suke duk sun zama busy itace last exam da zasu yi sun gama makaranta basa son su samu matsala ga bikin Hooriyah da yake ta matsowa saura Three months. Sun yi exams lafiya suka gama lafiya anyi Graduating sai jiran results kuma.

⋇⋆✦⋆⋇ 💫 ⋇⋆✦⋆⋇ 

𝗡𝗢𝗢𝗥

Tana barin gidan bata nufi ko ina ba sai gidan yayar ta Khairat ta nufa ɗaki ta nufa ta ajiye jakar ta ɗakin Khairat ta shiga ta same ta tana waya jira tayi ta gama sannan tace

"Ya gida Yaaya, ina su Hidaya naji gidan shiru"

"Suna islamiyya basu taso ba" ta bata answer tana Hararar ta

"Yanzu ke Noor ba zaki hakura da Zaaheed ba Kenan, ya nuna baya sonki amma kinki hakura. Yanzu muka gama waya da Mommy tace kiyi zaman ki Anan har sai ta nemi ki"tsaki taja tana tashi

"Haba Yaaya ya zaki ce haka shi ya fara nuna yana sona tun muna yara amma kawai yanzu yace ya fasa Bacin yasan irin yadda nake son shi"

Tsawa ta daka mata har sai da ta firgita "rufe min baki Shashasha wadda bata kishin kanta kawai" ta ce tana shiga Toilet Anan tayi ta zama har ta fito ta fice daga ɗakin ba tare da ta kalle taba. Sai da ta gaji dan kanta Sannan ta fito ta bata hakuri. A gidan tayi zaman ta bata zuwa ko ina sai makaranta.

Tunda taji ankai kuɗin Zaaheed hankalin ta yake a tashe ta rasa inda zata saka kanta tana matuƙar kaunar sa gani take in ba shi ba zata iya rayuwa ba kullum Neman Hanyar da zata Raba Auren take kafin ayi mutane ta ɗauka ayi mata bincike akan Hooriyah amma sun kasa samun wani naƙasu na ta kowa yabon ta yake tana cikin wannan yanayin ta samu Labarin an taɓa fasa Auren ta ranar ɗaurin Aure ango yace ya fasa......✍️

🏃💨 Anya burin Noor zai cika na mallakar Zaaheed?

👻💕 Ya Rayuwar Anisah take kuwa?

👀📝 Hooriyah zata Auri Zaaheed?

Duk waɗannan Answers ɗin suna nan tafe...

# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯

Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan

https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I

Follow My Pages

Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1

Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1

09047574404
WhatsApp Only

Comments & Share Fisabillah🥰👏

𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️
[5/17, 9:48 AM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡

https://chat.whatsapp.com/InjFDl8g9KiCk5F8oos5Yz

𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽

𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷

тԋє ɯɾιтєɾ σϝ

*ʂιʅαɾ ɯαყα*

𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡

Follow My WhatsApp Channel

https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I

بسم الله الرحمن الرحيم

𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️

𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟑𝟕&𝟑𝟖

____________💅_____________

Dole ta nace wa wadda ta sanar mata an fasa Auren Hooriyah sai ta raka ta gidan matar data sanar da ita da kyar da siɗin goshi ta amince tace su shirya suje gobe.

Washegari Da sassafe ta tashi ta shirya saboda kar ta makara Shaɗaya nayi ta fice ko sanar da Yaayar ta bata yi ba tayi tafiyar ta lokacin da taje gidan su ko tashi bata yi ba nan tayi ta lallaɓa ta tashirya suka tafi sai mita take ta fiya azarbaɓi
Bayan sun gaisa ta ɗora da cewa
"Hajiya wannan da kika ga munzo da ita ita ce da zata Auri Zaaheed ƴar uwar sa ce wanda zai Auri Hooriyah yanzu amma ya yaudare ta"

"Ayyaahhh ashe ke zai Aura da" cewar matar
Jinjina mata kai kawai tayi sai wani kallon banza take watsa wa gidan tana ɓata fuska. Matar ce ta cigaba da cewa

"Uhmmmmm, Ni nan da kike gani na ƙanwar mahaifin ta ce, ɗana naso ta Aura amma ubanta yace ba zata aure shi ba, shiyasa nace duk inda naji zata yi aure sai na ɓata Auren don ɗana kaɗai ya dace ta aura tun tana yarinya nayi masa tanadi sai yanzu da ta girma ace ba za'a bashi ba ba zai taɓa yiyuwa ba"

Ido Noor ta zaro "ƙanwar mahaifin ta fa kika ce"

"Ehhhhhh ko baki ga kama bane"
Chapter 10 · 0% Book details