Sashe 14
Hooriyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kuyi hakuri na tuba, Abeedah ki yafe min dan Allah" ta faɗa tana tasowa zuwa gurin Abeedah hannunta tazo kamawa zata riƙe Arshad ya buge shi
"Me kuma zaki yi mata" ya faɗa yana tsareta da ido Kwarjini taga yayi mata ƙasa tayi da kanta
"Haƙuri zan bata kawai"
"Ki bata daga inda kike ko wani abin zaki ƙara yi mata"
"A'a Arshad dan Allah ka bata hakuri wallahi nayi nadama"
Papi ne yayi gyaran Murya (𝒎𝒂𝒉𝒂𝒊𝒇𝒊𝒏 𝑨𝒎𝒎𝒊 𝒏𝒆) "duk abinda ya faru ya riga da ya faru Allah yasa bata yi kisan ba, Abeedah ki yafe mata munji Uzurin ta sai ayi mata Alfarma tunda bata kai ga aikata laifin ba, Allah ya yafe mana baki ɗaya"
"Alhaji dole ayi mata hukunci" cewar Hakimi
"Papi nakasar da Ammi da tayi kuma ya tafi a banza?" Cewar Arshad
"Duk wanda aka yi wa laifi kaga an bashi hakuri to an cuce shi ne, ba ga sakayya nan Allah ya mata ai bata Auri Abubakar ɗin da take so ba"
"Allah ya yafe mana baki ɗaya" cewar Ammi
Da Amin aka yi ta amsawa
Da kyar aka lallashi Hakimi ya haƙura ba sai anyi hukunci ba amma ya sake ta sai cewa yake sai anyi mata hukunci Ta inda yaji daɗi bashi da zuri'a ko ɗaya da ita. Kamar jira mutane suke su gama zaman zancen ya fara zagaye gidan Mutane sai Allah wadai suke yi mata, wadda ta riƙe ki amana tun shekaru da yawa ita zaki cuta.
🅩🅐🅐🅗🅔🅔🅓
Tunda Mommy'n su ta yanke wannan hukuncin yake jin ba daɗi Baya son Noor ko kaɗan kallon kwanwa yake yi mata Kulle kanshi yayi a ɗaki ya daina cin abinci dan Mommy'n ta gane baya son Noor Amma ta masa banza ta nuna bata san abinda yake ba ganin ba mafita bace yasa shi yanke shawarar tunkarar ta ya sanar mata shi baya sonta taje ta nemi dai-dai da ita. Bayan La'asar ya shirya ya nufi gidan su Noor yana zuwa ko ciki bai shiga ba yasa maigadin su yi masa sallama da ita ciki ya shiga a palour ya tarar da Mummy ita kaɗai gaishe ta yayi sannan yace
"Hajiya ana sallama da Noor a waje"
"Sallama kuma?, Su Waye? Basu san Gobe ne Auren ta ba"
"Ai Angon ne yazo yana waje" ya faɗa yana washe baki sai kace wanda aka bawa Kujerar Hajj😂💔
"Zaaheed ɗin mai yasa bai shigo ba"
"Hajiya cewa yayi sauri yake"
"Je kace masa gata nan zuwa"
"Tohm Hajiya Allah ya ƙara girma" ya faɗa da Sauri yana ficewa
Tashi tayi ta shiga ɗakin Noor tana zaune a kan gado waya take yi ganin Mom ne yasa ta katse kiran kana ganin ta kaga Amarya an fara gyaran jiki ta ƙara yin wani kyau ga kamshi sai tashi yake a jikin ta Mummy ce tace
"Kizo Zaaheed ne yazo yana jiran ki"
"Mummy Zaaheed ɗina, gani nan zuwa" ta faɗa tana tashi Drawer ta buɗe ta ɗauko Hijab sakawa tayi ta fice jikin ta sai rawa yake
𝐾𝑒𝑑𝑎 𝐴𝑛𝑔𝑜 𝑘𝑜 𝑎𝑚𝑖𝑛𝑐𝑒𝑤𝑎 𝑏𝑎𝑖𝑦𝑖 𝑏𝑎 𝑘𝑖𝑘𝑒 𝑔𝑦𝑎𝑟𝑎𝑛 𝑗𝑖𝑘𝑖 𝐻𝑎𝑏𝑎 𝑁𝑜𝑜𝑟 𝑑𝑖𝑛 𝑚𝑢 𝑦𝑎 𝑧𝑎𝑘𝑖 𝑏𝑎𝑑𝑎 𝑚𝑢🤣🤣🤣😂😂
A tsaye ta tarar da shi jikin Motar sa ransa a dagule tafiyarta ta gyara tana takun jan Aji Muryarta ta ƙaryar
"Yayana, Habiebie 🤍 yaushe kazo? Me yasa baka shiga daga ciki ba?"
A fusace ya ɗago yana Nuna ta da yatsa " Ke Noor Ba wannan ne ya kawo Ni ba ki dakata, zuwa nayi na faɗa miki ki sanar musu kar su sake su Ɗaura Auren nan dan sai kinyi dana sani tunda aka raba Ni da Hooriyah babu wata mace da zata same ni yanzu" ya faɗa yana watsa mata wani kallon banza tare da shigewa motar sa yayi tafiyar sa. Sagadee ta bishi da kallo zuciyar ta kamar zata fito Aa koma cikin gidan...
𝑯𝑶𝑶𝑹𝑰𝒀𝑨𝑯
A bangaren Hooriyah kuwa Depression ne mai tsanani ya kamata ba Abinda yake ɗaga mata hankali sai jin wai har ciki ta zubar shiyasa aka fasa Aure na farko ita da ko riƙe hannun namiji bata taɓa yi ba Indai ba Yayyun ta ba duk wanda yayi mata sharrin nan bazata yafe masa ba ya shafa mata tabon da ba zai taɓa goguwa ba. Bata tabbatar da tana son Zaaheed ba sai yanzu bata da aiki kullum tana cikin damuwa magana ma sai Sajeedah ta saka ta a gaba take yi ga kusan kullum sai ya kira ta Shiyasa ta kashe wayar tunda Auren shi saura kwana Uku. Tattarawa tayi take gida tayi musu kwana biyu ko zata samu sauƙin abinda take ji amma sai yafi da ƙaruwa dole ta dawo Gidan Sajeedah.
Anyi wa Abduljawwad Transfer zuwa Abuja a gurin aiki kuma dole a cikin satin zai koma Dan haka suka fara Shirin tafiya Hooriyah kuma ta shirya zata koma gida ganin halin da take ciki yasa yace zai ɗauke ta su tafi can ko zata manta da abinda ya faru bayan wani lokaci ta dawo. Da farko Daddy kin yarda yaso yi Mami da Aunty ne suka yi ta lallaɓa shi da kuma ganin halin da take ciki yasa ya amince suka tafi........................✍️
# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯
Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan
https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I
Follow My Pages
Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1
Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1
09047574404
WhatsApp Only
Comments & Share Fisabillah🥰👏
𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️
♡ ԋσσɾιყαԋ ♡
https://chat.whatsapp.com/InjFDl8g9KiCk5F8oos5Yz
𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽
𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷
тԋє ɯɾιтєɾ σϝ
*ʂιʅαɾ ɯαყα*
𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪
♡ ԋσσɾιყαԋ ♡
Follow My WhatsApp Channel

بسم الله الرحمن الرحيم
𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️
𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟓𝟏&𝟓𝟐
___________________________________________________________________________
Around 9:00 Pm
Cosgrove Smart Estate, Wuse, Abuja.
Anan aka sauke su gida ne Mai kyau da Bedrooms guda biyar sai palour da kitchen kowanne ɗaki da Toilet ɗin sa suna shiga kowa ɗaki ya nufa wanka da sallah Tayi tana kwanciya ta huta.
Washegari
Gyara gidan suka yi suka chanja abinda ba za'a rasa ba Su biyu suka yini sai gurin La'asar Sannan Yaya da yaran suka dawo bayan La'asar suma shiryawa suka yi zawa shopping da Park zaman gidan ba daɗi duk da a Kano ma ba fita suke ba.
💥💦
Duk da an hana yi mata Hukunci tana cikin wani yanayi Sashe aka ware mata a cikin gidan kowa tsoron zuwa gurin ta yake kar ta cutar da shi tunda wadda ta yarda da ita ma ta cutar da ita. Mutum ɗaya ce ta yarda zata iya zuwa kullum da safe tayi mata aiki ta dawo. Bata da aiki sai kukan nadama wanda ba abinda zai yi mata. Kwana Uku tayi a Sashe da safe wadda ke zuwa yi mata aiki tazo a kwance ta tarar da ita jijjiga tayi amma shiru hakan yasa ta fito da sauri. Da akwai Fadawa guda biyu a ƙofar sashen suna tsare ta. Ganin ta suka yi arikice
"Ta suma, kuzo ku gani ko zaku iya dubata"
"Ki yayyafa mata ruwa mana zata tashi" ɗaya daga cikin su ya faɗa
"Na yayyafa mata" itama ta Bashi amsa
"Sai ki haƙura ai" yace yana ɗauke kansa da cigaba da abinda yake
Wuce su kawai tayi cikin gidan ta nufa
"Ta suma kuzo ku taimake ni"
Yawan ci mutane sun firgita dajin zancen nata dan sun gane wa take nufi, Kowa tsoron shiga sashen yake "Wai ba zaku ƙara so ba ne kuga halin da take ciki?"
Da kyar aka samu mutum biyu suka bita suna zuwa ta raka su har ɗakin datake ɗaya ce ta duba ta salati suka ji ta saka tana cewa
"Kamar fa ta mutu"
"Ta mutu" wacce ke kula da ita ta maimata
"Ban tabbatar ba, Amma bari mu sanar a ciki"
Nan suka fita suka sanar a ciki. Likita ne yazo ya duba ta ya sanar musu ta mutu. Mutuwar ta doki mutane da yawa bayan Azahar aka kaita gidan ta na gaskiya. *Allah yasa mu cika da Imani, Amin*
Jikin Ammi ya ƙara warware wa tana jin sauƙi shirun da take yawan yi ne yake damun sa saka ta yayi dole sai ta shirya sun fita. A sirrance suka fice daga cikin gidan ko Mai martaba basu sanar wa ba hadiman tane kawai suka san sun fita suma sai da aka ja musu kunne kar a san sun fita.
✨💫
Jabi Lake Mall, ABUJA.
Tafe suke da Sajeedah
"Aunty Bari in duba ko akwai wani turare da nake ta nema ban samu ba"
"Ok sai kin dawo" Thom tace mata juyawa tayi tana nufar wurin Turaren. Duba su ta fara can ta gano wanda take nema "Yes shine" ta faɗa tana ɗan yin sauri zuwa gurin karo tayi da wani abu ɗagowa tayi dan ganin menene Mutum ta gani tsaye a gaban ta.
Tafe suke shida Ammi Hira yake ta yi mata kiran sa aka yi a waya ɗaga wa magana yake yana tafiyar ji yayi karo da wani abu a fusace ya ɗago Arba yayi da kyakkyawar Budurwa da sauri tace masa
"I'm sorry, I didn't know that would happened"
"Kamata yayi ki ringa kallon hanya in kina tafiya ba waige-waige ba"
"You should stop answering calls when you're walking sir" itama ta bashi amsa tana wucewar ta
Ammi Bata lura da abinda ya faru ba kawai giftawarta ta gani taɓa shi tayi
"Wace wannan kuma"
"Ammi ban san ta ba, bige Ni tayi"
"Ba abinda ya same ka dai" ta faɗa tana duba hannun sa
Hannun ta ya riƙe yana cewa"Ba komai Ammi"
🌟💕
Tunda suka koma gida yake wa Ammi zancen Yarinyar da suka haɗu dazu ta birge sa a nemo masa ita duk inda take. Hakan yasa Ammi ta sanar wa Sarki aka shiga neman ta da kyar aka samo information akan ta.
𝑍𝐴𝐴𝐻𝐸𝐸𝐷
A bangaren Zaaheed kuwa kamar yadda Mommy'n su ta sanar haka ne ya faru Ranar Juma'a bayan Idar da Sallah aka ɗaura masu Aure da Noor Kowa mamakin Auren yake ba sanarwa
Amarya Noor sai murna take ta mallaki Zaaheed ɗin ta shagalin su suka yi har dare lokacin da aka zo daukar amarya dan kukan da amarya take in za'a Kaita gidan miji Noor ko kwalla bata yi ba.
ABUJA