← Book details Hooriyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 17

Sashe 7

Hooriyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Knocking ƙofar akayi Kallon kofar yayi "Come in" ya maida kansa kan abinda yake yi. Wanda yake ƙwanƙwasa kofar ne ya shigo neman guri yayi ya zauna "Zaaheed kai dai ba zaka Chanja hali ba Koh"

"Me kuma nayi ne" ya faɗa ya ɗagowa

"Ya wuce, kasan menene"

"Ya za'a yi na sani, Ni da ba sanin gaibu nake ba"

"Matsala ta da kai kenan, Da gaske ne fa zancen da muka ji"

"Wanne daga ciki?"

"Na Ba'a yi Auren A'ishah Harith ba, yau ma har mun gaisa da ita"

"Dan kun gaisa da ita Shine yake nufin bata da Aure"

"A'a baka gama jin zancen ba, ai har jaje nayi mata dan na tabbatar" dafe kai yayi

"Wallahi Naseer ka shiga uku, gulma kamar mace"

"Ai dama kace haka, Ni da nake so kaima kayi Auren nan" "Dan Allah wannan lokacin Karka ƙi faɗa mata kana son ta karta suɓuce"

"Da ai kai kasa nace ina son nata Koh"

"A'a Ni dai shawara ce na baka, karka yi sake sai anjima"

Tinani ya shiga yi akan maganar tasa dan gaskiya tunda ya fara ganin ta yaji yana son ta bai taɓa kamu wa da ƙaunar wata ba sai ita, Dole ya nemi mafita kafin wannan damar ta ƙara kufce masa...

****

Zaune suke a cafeteria hira suke tabawa Khaleesat ce tayi tsaki Zee ce tace Lafiya "Waccan Banzar na gani wallahi"

"Kace kema kinyi mugun gani" inji zee

"Wai wace ne haka" cewar Hooriyah

"Wace wadda ta wuce Anisah mana" Ruky ta faɗa. Zaram ta miƙe "Ina zaki kuma" ba tare da tace komai ba ta fice. "Abinda na guda kenan shi yasa ban faɗa ba wallahi" "Bari inje inga ina tayi" Cewar Khaleesat, Karɓar Fadil tayi ta bita.

Can ta hango ta zaune a cikin Mota Karasa wa tayi ta buɗe shiga tayi sannan tace "Meyasa kika taho, ai bai ka mata ki taho ba"

"Me zanyi in ban tashi ba nayi Wa kaina Alkawarin babu Ni babu ita, ko inuwa ɗaya bana son mu zauna"

"Abin ba daɗi amma da baki nuna kin ganta ba"

"Ai bata isa zuwa inda nake ba"

"Allah ya Kyauta" "Ameen". Hira ta ringa janta da shi har ta saki jiki Bayan wasu mintina suka fito suna da wata lecture.....

✰✰✰

𝐸𝑚𝑖𝑟'𝑠 𝑃𝑎𝑙𝑎𝑐𝑒 𝑨𝒃𝒖𝒋𝒂.

Motoci ne suke shigo wa cikin masarautar a tsare suke tafiya basu tsaya ko ina ba sai baƙin fada nan suka yi parking Buɗe kofar Motar ba faɗe yazo yayi "Allah ya ja zamanin yarima Barka da dawowa yarima" shine abinda fadawan suke ta faɗa Kusan minti ɗaya sannan Aka zuro ƙafa sai da ta ɗau wasu seconds sannan aka sako ɗayar kafar fito wa yayi gaba ɗaya Tunda ga Kallon Kafar sa Kaɗai Kasan Mamamlakin ta ya haɗu dogone ba shi da ƙiba sosai Kyakkyawa ne abin farko in ka gansa zaka yi tunanin Balarabe ne ya haɗu, ɗaga musu hannu kawai yayi ba tare da yace komai ba Cikin fadar suka shiga cikin takun izza...

**** **** ****

Zaune take akan kilishi ta kishingiɗe a cikin ɗaki ita kadai Kofar aka ƙwanƙwasa izinin shigowa ta bayar buɗe wa akayi aka shigo Amintacciyar Hadima ta ce zube wa tayi a ƙasa "Ranki ya daɗe Barka da Rana"

"Barka kadai" tace cike da izza

"Me yake faruwa a cikin gidan"

"Ranki ya daɗe ʏᴀʀɪᴍᴀ mai jiran gado ne ya dawo, daga gani kuma ya samu lafiya"

A zabure ta mike "Mai kike nufi da ya dawo, Jiya ma sai da muka yi magana da mai Martaba amma bai Sanar mun da dawowar sa ba".............✍️

𝐄𝐧𝐝 𝐎𝐟 𝐁𝐨𝐨𝐤 σɳҽ

Alhamdulillah Anan na kawo ƙarshen Book One sai mun haɗu a Book Two zan tafi hutu sai bayan sallah Idan Allah SWT ya Kaimu bayan Sallah Zamu cigaba.

Tafiyar mai nisa ce..

Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya duba wannan WhatsApp channel ɗin

https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I

Follow My Pages

Arewa Books: fatimaintisar1

Wattpad: fatimaintisar1

#𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯

Please Share & Comments 🙏

𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ✍️
[5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡

https://chat.whatsapp.com/CmyP8hlqbHtGyhdQ7FVc2w

𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽

𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷

тԋє ɯɾιтєɾ σϝ

*ʂιʅαɾ ɯαყα*

𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466

Follow My WhatsApp Channel

https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I

Ina yiwa ƴan uwa musulmai Barka da sallah da Fatan munyi Sallah Lafiya Allah ya karɓi ibadun mu yasa muna cikin ƴantattun bayi Ameen

بسم الله الرحمن الرحيم

𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️

𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟐𝟐&𝟐𝟑

————————————————————————————————————————

*Gidan Amarya*

Soyayyar su suke zuba wa basu da damuwar komai tun tana jin ɗari-ɗari har ta saki jiki da shi zaman su suke lafiya ƙalau.

Buɗe motar tayi ta fito cikin gidan ta shiga tass yake ba abinda yake tashi sai kamshi ba kowa a cikin palour sama ta haura. Zaune yake a palour aiki yake yi a system, a hankali ta fara tafiya har ta isa inda yake baiji shigowar ta ba. Rufe masa ido tayi,dafe idon yayi "Be cika min ido mana aiki nake fa"
Dariya ta ƙyalƙyale da ita
"Ya akayi ka gane Ni ce"
"Ai nasan babu mai wannan aikin sai ke"
Dariyar ta cigaba da yi tana dawowa kusa da shi zama tayi a jikin sa
"Kin tsorata Ni da yawa Habibty"
"Sorry Noory, Har ka dawo"
"Eh, Babie ya makarantar"
"Alhamdulillah duk ba daɗi ina ta kewar ka"
"Ba gashi kin dawo ba, fatan babu abinda ya faru"
"A'a babu komai, Kasan yau na haɗu dasu Hooriyah"
"Amma dai baki kula su ba Koh, dan nasan suna ta jin haushin mu"
"Ban kula su ba, in na kula su ai sai suyi min duka ko zasu hu ce Haushin"
"Innnnnnaaaaaa dako munyi Shari'a dasu kawai su dakar min mata, Ni fa ko sunan su bana son kina ambata haushi nake ji"
"An dai na daga yau ranka ya daɗe" anan ta cigaba da zama tana kallon sa yana aiki kiran sallah ne ya tashe su ɗaki suka yi yayi alwala ya fice ita Kuma ta shiga wanka tana fito wa tayi sallah ta tashi zata fice Wayar tace tayi ƙara dawowa tayi ta ɗauka ganin Ummanta ce take kira
"Umma na ina wuni"
"Fatan kuna zauna lafiya ba wata matsala"
"Babu Matsalar komai wallahi, lafiya ƙalau muke zaune"
"Masha Allah haka nake son jin, dan Allah ki bishi sau da ƙafa kar a samu matsala"
"Babu abinda zai faru Umma, yana sona fa"
"Allah yasa dai" "Ameen" nan suka cigaba da hirar su cikin nishaɗi da walwala.

*To dama ina za'a samu saɓa ni tunda yanzu kuka yi auren, har yanzu amarya ce fa😌*

★★★

Bata dawo gida ba sai Kusan Magariba Sajeedah ce kaɗai a palourn duk yaran basa nan neman guri tayi ta zauna tana yi mata ya gida ta amsa da lafiya lau
"My Only Anty Ina su Fudail"
"Yau kuma shakiyanci kike ji kenan sun fita da Abban su"
"Ba shakiyanci bane ba, kin san babu ya ke Babu ke ba kishiya, Shine basu jirani ba"
"Ai ko shi in ya faɗan haka nasan zolaya ce, Kun fi kusa da shi ai"
"Shikenan sa wasa, kin san in na faɗi Abu kamar shi ya faɗa Koh"
Nan take bata labarin abinda su Khaleesat suka yi ranar biki da suka je gidan su Anisah
"Kai amma basu kyauta min ba da sun sanar da Ni zasu ai sai nayi abinda yafi nasu" galala tayi tana kallon ta
"Ke dana kawo wa ƙara in sunzo kiyi musu faɗa"
"Wane irin faɗa za'a yi musu, ai kamata yayi da suka je sunci ubanta, ko ta gane Shayi ba Ruwa bane"
"Chabbbbb Ni dai banji daɗi ba wallahi, in tani ne ma da basu je ba"
"Ni Ko sun min dai-dai, da sun sanar dani dana raka su, dan Duka zamuyi mata wallahi"
"Abin naki babba ne gwanda da baki sani ba"Bari in tafi ɗaki.
Tashi tayi ta shige ɗaki bata fito ba sai da taji hayaniyar yaran sun dawo. Fito wa tayi ta ringa yi masa mita bai jira ta dawo sun tafi tare ba. Hakuri ya bata yana ce mata baisan zata ba da ya jira ta amma ta bari next time sai suje da kyar ta yarda. Zaman cin abincin suka yi bayan sun gama gurin yaran ta koma tana ta yi musu wasa sai gurin shabiyu ta fito shima dan Sajeedah ta saka yaran suyi bacci ta koma ɗakin ta sallah daren ta tayi tun lokacin sai ta dau Kur'ani ta fara tilawa bata kwanta ba sai gurin uku.

♥♥♥

Zaune suke a cikin fada tsitt ba ka jin komai sai ƙarar AC hayaniya ce ta fara tashi daga waje wani bafade ne ya fita dan dubawa bai jima ba sai gashi ya dawo "Allah ya taimake ka Yarima ne dawo" yayi mamakin jin Yarima ne ya dawo Jiya ma fa sunyi waya amma bai sanar da shi ba, ɗazu ma yayi waya da likitan sa shi ma bai faɗa masa ya taho ba *"Me kake jira da ba zaka shigo da shi ba" da sauri ya miƙe zai fita sai gashi ya shigo fadawa suna ta masa kirari

Gurin Sarki yazo ya gaishe shi tare da mutanen Fada bai daɗe ba ya tashi yayi musu sallama yana ficewa daga fadar.

⍟⍟⍟⍟ ⍟⍟⍟⍟ ⍟⍟⍟⍟

"Tabbas Ranki ya daɗe ya dawo chan na hange shi ya shiga Fada"

"Bai mutu ba kenan" Shiru ɗakin yayi na yan Mintina Wata Harara ta wurga wa Hadimar da sauri ta mike jikin ta na ɓari "A huta Lafiya" tace ta fice da Sauri tsaki taja tashi tayi ta fara zaga ɗakin magana ta fara

"Yanzu yaron nan bai mutu ba kenan, yana raye, kuma ya dawo Fada"

"Dole ya koma inda ya fito tunda bai mutu ba"......✍️

# 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯

Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan

https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I

Follow My Pages

Arewa Books: https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1

Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1

Comments & Share Fisabillah🥰👏

𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️
[5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡

https://chat.whatsapp.com/CmyP8hlqbHtGyhdQ7FVc2w

𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽

𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷

тԋє ɯɾιтєɾ σϝ

*ʂιʅαɾ ɯαყα*

𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪

♡ ԋσσɾιყαԋ ♡

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
We shine all over the world

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466

Follow My WhatsApp Channel

https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I

بسم الله الرحمن الرحيم

𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️

𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟐𝟒&𝟐𝟓

————————————————————————————————————————
Chapter 7 · 0% Book details