Sashe 8
Hamshaƙiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washe gari na tashi cikin shirin zuwa gida.
Naje gaida Hajiya tace "Ga akwatuna nan an kawo na tsaraba, na kwana biyu banyi tsaraba ba in naje Ummara ko aikin Hajji.
Nace sannu da ƙoƙari. Tace "Yanzu sai ki buɗe ki raba." Nace Hajiya zan iya kuwa? Bata amsa ba dan haka sai na buɗe akwatunnan na dinga ɗaga wa ina kallo zannuwan gado, dardumai, kayan yara da dai sauransu. Na cire wa su Anisa riguna yaran su Maman Umar kowa ɗanta ɗaya ya samu. Dogayen riguna Jallabiyu. Na cire wa Azima guda biyu su Juma hijabai. Shamaki wata Jallabiya bulu ta yi kyau na ce wannan dai tamuce, masu gadi dama nasan adadin su tun a biyan albashi, na cire musu dardumai da carbi. Nace Hajiya gashi na cire na waɗan da na sani. Na lissafa mata, tace "Bari in zana miki sauran tana ta fiɗi ina cirewa aka gama. Tace ina nawa. Nace ai ko ban ɗauka ba babu komai. Ta ce shike nan tunda baki so cirewa Ummar ki. Na ciri Hijabi irin na su Juma. Abbanmu kuma carbi da dardumai. Tace shike nan aba kowa na shi a kai mata sauran stor.
Hajiya tace in bari sai ƙarfe goma sannan in tafi. Tace me zanje dashi ina cincin da nama ko haka zanje hannu rabbana? Nace ai gida ne ko ban kai komai ba babu wata matsala. Tace "To da aka fitar da zakkar fidda kai an kai masu?" Nace gaskiya bansani ba dai domin shi ya raba. Ta ɗauki waya ta kira shi, yana waje Shamsu ya yi sallama da shi. Tace "Ankai zakkar fidda kai gidan su matar ka?" Yace baki faɗa min cewa za a kai ba. Na bayar ne a guraren da aka saba kaiwa.
Tace "Ya Salam! Ban ji daɗin wannan lamarin ba sam. To yanzu me zata kai gidan su? Yace duk abinda ki ka ce .
Hajiya ta kashe waya sannan ta dube ni. Kira Juma. Na kirata. Tace Juma A samu manyan ledoji a zubo dambun kajin nan,sai kuma na naman shanu, wata ledar a zubo cincin,aka kawo gabanmu, tace Juma ki sa rabe ya fitar da lemo kat an goma ya saka a mota akai waɗannan ledojin." Ta duba ni, kije ɗaki na kija wannan durowar da kika gama bince su ki ɗakko sabbin 'yan ɗari biyu ki riƙe saboda taɓawa yara. Nace "To. Amma jikina ya yi sanyi da jin kalma durowar da ki ka bincika. Na ɗakko na fito. Tace in gaishe su,sannan kuma Shamaki zai zo ya ɗakko ni daga nan sai ya gaishe su,,ko hakan bai yi ba?" Nace ya yi na gode sosai.
🖊️🖊️🖊️
Gida ya kaure da murnar zuwana. Direba ya na ta shigo da kayan lemo na saka yaran maƙotanmu su taya shi ɗakkowa. maƙota harda leƙe ance Baby ta zo.
Wani abu da ya ɗaure min kai shine yadda naga buhunan shinkafa guda biyu a ƙofar ɗakin Umma. Nace wannan fa? Tace "Wadda mijinki ya kawo mana ce ta salla buhu biyar muka rabawa dangi da maƙota guda biyu, Abban su Zuhra kuwa muka bashi rabin buhu, rabin ce muke dafawa, sai sauran biyun sune kin gansu nan." Nace Kuma ni sam bai faɗa min ba, Hajiya ma bana zaton ta sani. Domin ta tambaye shi ko ya kawo muku zakkar fidda kai, yace a a. Umma tace "Ikon Allah wato su dai mutanen kirki haka suke, to kaji goman ma bai faɗa miki ba kenan?" Na saki murmushi nace Allah ya saka masa da alkhairi, kuma sam bai faɗa ba. Daɗi ya lulluɓe ni, take wani son shi ya ƙaru a zuciya ta.
Tsakar gida muka shinfiɗa tabarma aka baje muka zube kayan da na kawo. Abba ya shigo muka gaidasa cikin murna yana ta sawa Shamaki albarka da ni. Yara masu shigo da lemo suka gama Umma ta basu ɗai ɗai suka tafi suna murna.
direba ya tambaya ƙarfe nawa zai dawo ? Nace ba sai ya dawo ba Shamakin ne zai zo mu tafi.
Nan Umma ta shiga rabon lemo Jafar da Habu suna miƙawa maƙota, tana cewa kowa dai ya lasa, domin duk wanda ya ci shi kaɗai tofa shi kaɗai zai mutu. Muka sa dariya. Jamila tace Umma in ka ba wasu tare zaku mutu? Umma tace "Ba haka ake nufi ba, abin nufi shine zaku mutu ne da ladan abinda ka bayar, in kuwa ka ci kai kaɗai tofa babu maganar wani lada da zai bika kabari." Ni kai na sai yanzu na san ma'anar wannan Hausar. Nace gaskiya ne. Allah ya bamu ikon aikata alkhairi. Gidansu Zuhra kuwa sai aka kai katan ɗaya. Sai kuma ake ta shigowa godiya, nasan da biyu ne dan a ganni kuma aga me na kawo. Umma dai sai ta koma duk wanda ya shigo sai ta basu cincin da naman da na zo da shi.
Muka baje munata hira ina yi wa Umma mitar su Jamila basu zo min ba. Jamila tace Abba ya hana mu kuma ga aikin gida. Umma Tace "Yaran gidan masu niƙa waɗanda su ka yi miki biki wai sunzo an hana su shiga." Nace basu faɗa muku bane lamba ta kawai duk wanda zai zo zai karɓa, ya kirani ya faɗa min cewa zai zo. Shikenan in faɗawa masu gadi. Duk wanda yazo zasu tambaye shi ne, gun wa kazo ko ka faɗa in sukace tasan zaka zo kace e, to zasu ce ka kirata a waya yanzu zata kira mu. In kuma kace bata sani ba,, kai tsaye zasu ce ka wuce ka tafi hazaka shiga ba. Umma t ace "To in kana da shi ne sai da tsaro rayuwar babu tabbas kana bacci wasu suna yi maka minshari."
Haka dai muka yita hira, sannan na tashi na shiga maƙota da 'yan uwa muka gaisa tsofaffi da ƙananan yara su na bai wa goron salla ta. Shamaki ya kirani muna ƙofar na'isa ni da Jamila gidan wata ƙanwar Abba. Yace sai dare zai zo mu tafi na yi murna. Har hankali na ya tashi ko dai sun shirya da wata ne za su haɗu, sai kuma na tuna yana Azumi. Take na sauke ajiyar zuciya tare da faɗin to sai ka zo. Zan je gidan wasu 'yan uwan mu a Fage. Yace "Dama kuna da 'yan 'uwa a Fage ne?" Nace E mana, ya ce "Shikenan gaida su. Ko in turo miki direba ya kai ku bana son matata a kekenapep?" Nace barshi kawai babban baƙo. Yace 'To don Allah ki ɗauki shata karki cakuɗu da mutane kuma daka kike ke kaɗai wani ya taya min mata ya zata budurwa ce. Nace ni da Jamila ne dama ko ni ɗaya ce drop zan ɗauka. Muka yi sallama akan sai ya zo. Jamila ta dube ni. Ke kuma ina ki ka samu dangi a Fage? Nace ke dai muje kya gansu.
Gidan gidan sama ne irin tsohon ginin nan na cikin Fage. Muka shiga cikin gidan benan tamkar sai faɗo ƙasa, muka yi sallama. Wadda ta zo karbar zakkar nan ce,tana ƙoƙarin hura gawayi. Ta taso da sauri ta tare mu tana faɗin Hajiya sannunku da zuwa.Muka amsa,tace "Kunzo gurin tsohuwa ne ko?" Nace Gurin ta muka zo. Tace tana sama muje in kai ku?" Muka shiga saman kamar zai faɗo nake ji.
Tana kwance akan wata tsohuwar katifa tayi fale fale cikin tsummuna.sai dai da alamu ana kula da ita in aka yi la'akari da ɗakin fes yana ƙamshin turaren tsike, sannan kayan jikinta da tsummunan duk suna wanke fes. Ta shimfiɗa mana tabarma a gaban tsohuwar tace mata Hajiya ce wadda ta bamu zakka yazo ta gaishe ki. Tsohuwar ta ɗan taƙarƙara ta tashi tana ɗan tari ƙutul ƙutul. Irin na tsufa. Nayi mamakin yadda na ganta a waya kuwa muryar tar kamar matashiya. Nace sannu Kaka. Tace "Sannu yarinya sannu da zuwa, matar Shamakin ce kokuwa dai cikin yayun nasa ne? Domin ba muryar Zeena bace, ina tiƙe da muryar Zeena Zeena adon kyawawa maganar cikin ƙasaita ta ke yin ta. Tana lafiya dai ko?"
Nace lafiya lau Kaka, matar Shamaki ce ni, na zo in gaishe ki gaisuwar salla, sannan muɗanyi hira irin ta jika da kaka in samu tarihi iyayena su Hajiya Zeena. Jikarta ta yi 'yar dariya tace kun kuwa same shi, domin ko mu radda abin ya motsa muna shan hirar gidan Alhaji Baita. Tsohuwa ta yi kaki ta ɗauki wani ɗan gwangwani ta tofa a ciki, sannan tace "To yarinya me ki ke son ki sani?" Nace. Hajiya tarihi nake som ji na Hajiya Gwamma. Tace "Allah sarki Duniya labari Gwamma da ke Hajiya uwar Ali Baita. Jikata duk inda ki ke neman mace mai kirki da mutunci in kika samu Gwamma zance ya ƙare. Hatta "yan aikin gidan Hajiya Gwamma suna zuwa aikin hajji. Ni nan banje ba,amma mai gidana yaje saboda shine direbanta kuma ita ce ta haɗa aurena da shi. Nace masha Allahu. To kinsan lokacin da aka yi auren Ali Baita kenan? Na tambaye ta. Tace sani kai, a gidan fa muke zaune da mai gidana. Na gyara zama nace ashe kinsan lokacin da aka auro Hajiya Zeena. Tace "Ƙwarai kuwa, Ni ce nan aka fara baiwa Zeena a matsayin mai dafa mata abinci, aka maidani kicin ɗinta. Jikata ban taɓa ganin soyayya ko jin labarin soyayya irinta Zeena da mijinta Ali Baita ba, kirarin da yake yi mata kullum shine Zeena adon kyawawa. Gata da gayu ban taɓa ganin mace 'yar gayu mai kula da miji tare da tattalinsa kamar wannan baiwar Allah ba.
Ta sake yin ɗan tarin ta sannan taci gaba da faɗin "Biyayya kuwa kinga.Ta ɗaga yatsun hannunta tana lissafi. Kiga ita ce ke girkawa Hajiya Gwamma abinci daga ranar da likita ya ce ta daina cin farin magi.