← Book details Hamshaƙiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 31

Sashe 10

Hamshaƙiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Na Kali Jamila nace kinji kuma. Da alamu dai in zamu kwana ba zan daina jin sabbin abubuwa daga bakin tsohuwar nan ba. Tsohuwa tace "Kwarai kuwa. " Nace to wai Kaka Kina gidan Shamaki ya zama saurayi?
Tace "Yana dan makaranta lokacin da na bar gidan ana zancan za a fiddashi kasar waje." Na kada kai, da alamu dai bata da wata masaniya akan Shamaki sosai.

Nace Na gode Kaka dajin Wannan labari na bude jakata na ciro kudi ban kirga ba na kama hannunta na saka mata ina fadin Baba ga su nan a sai miki goro.

Tace "kuma dai ba a gajiya 'yannan Allah ya saka miki da albarka. Kuma naji dadi da wannan ziyara a san da kai ma acrayuwa Ai arziki ne."

Muka fito mukayi musu sallama muka wuce. Muna dansahu na kasa magana ina juya wannan lamari ace wai su Maman Iman ba Uban su daya da Shamaki ba. Jamila tace "Wai in tambaye ki? " Na sauke ajiyar zuciya nace ina jin ki. Tace "Me Wannan labarin zai amfane ki da shi.? "Nace Jamila bazaki gane ba, assignment na ke yi zan hada rahotanni ne tsayo shekara daya. Ta juyo tana kallona alamun bata gane ba. Nace bazaki gane ba. Lokacin da Hajiya Zeena ta juyo da ni zuwa gida da takarda ta ta zaki zaki fi dahimta. Ta zaro ido "Auren shekara daya ku ka yi? " Nace in har shekara ta cika ban san waye Shamaki ba, to zata sa ya sallame ni.

Jamila ta taba baki, wannan gida naku sai kace wani gidan gwamna ko na shugaban kasa."
Nace Ai gidanmu ya wuce nan, domin daga gwamnan har shugaban kasa suna girmama Zeena sun san abinda suke samu daga gareta.

Jamila tace "Wai ma dan ku kuma san hakan Allah ya kyauta."

Da dare Na shirya tsaf Jamila sai tsiya take min wai haka na zama sai wani kakale na ke yi akan miji. Umma ta shigar min tace barta ta yi aikin ladane, ke ai ba a san abinda zaki yi ba.

Bayan ishai sai ga kiran Shamaki wai ga shi a hanya. Dan wani salon da ya zo sai ya tsaya a kofar gida wai in fara fitowa,

Nace ka shigo kai tsaye.
Ya ce fara fitowa mana. Na saka mayafina na fita, yana tsaye a inda ya saba tsaya lokacin da yake zuwa zance. Na gane cewa yana son tuna baya ne, dan haka nima sai naje gurin da nasaba zama na zauna. Nace sannu da zuwa dan samari,. Yace yawwa 'yan mata dazu na ganki ke da wata kanwarki kuma dai na fada sonki irin ta ka dinnan, ya miko tafin hannhu sa, shin ko zaki bani soyayyarki? " Na dora tafin hannu na ina fadin na baka ya kai wannana kyakykkyawan basarake ina fata zaka rike ni amana bazaka sake ni ba.. Ka sani babu wata mace wadda zaka yi mata tayin soyayyarka ta kauda kai. Ina sonka. Sai ya janwo ni jikinsa yana fadin nima ina sonki yake wannan yarinya mai kyau da iya kalami.

Sai duk muka sa dariya ya sake ni tare da fadin muje in gaida su Umma. " Muka nufi cikin gida. Tuni an shinfida masa shinfida, suka gaisa daga nan sai Abba da Umma suka yi masa godiyar sako. Ya ce babu komi ya dada ciro kadi ya aje wa Umma sannan ya aje wa Abbbanmu. Suka sake yin godiya, sannan Abba yace kuje ki raka shi ya gaida Abban su Zuhra kafin ku wuce ko?" Nace to. Muka fita yace mu taka a kafa muje." Abarandar da suke salla muka same shi, shida wasu makotan su. Muka durkusa muka gaida su, yace Uwata ce sannunku muka gaisa ya ciro kudi ya ba Abban su Zuhra, sannan suma na zaune ya ciro ya basu.
Suna ta saka albarka, daga nan muka koma mota, muna shiga ya rungume yana neman bakina, na biye shi na tsawon lokaci kafin daga baya na zame nace atiti muke ya sake kamoni, my Baby mu bivu ne anan ba mai ganinmu. Ya yamutsani son ransa, da kyar na lallabashi. Ya figi mota da gudu. Ni dashi babu wanda ya iya furta wata kalma. Kaina na jingina sa a bayan kujera na lumshe ido kamar mai bacci. Duk ya saukar min kasala, gashi yanzu in munje gida gurin Hajiya zamu yada zango. Shims nasan damuwar kenan.

Koda ya yi hon har aka bude mana gate ban iya dago kaina ba. Sai da ya tsaya ya sa hannu ya shafi wuyana,sannan ya daga wayarsa ya soma magana cikin harshen turanci, duk da banajin sosai kunsan karatunmu na Kano in ba makarantar kudi ka yi ba sai a hankali na tsinci kalma biyu. My wife sai kuma da ya gama maganar naji yace ok. Na tashi da niyyar fita sai na ga ashe ba gida muka zo ba. Nace Babban bako ina ne nan? Yace karanta can ya nuna min wasu rubutu masu kawo wuta. Hotel din ne ya dauki hankali na ba sunan Hotel din ba.
Na dubeshi da sauri, Subahanallahi Auzu billahi minasshaidanin rajim! Me zamuyi a Hotel da mutuncinmu da komai! Me zan gani Shamaki? Yace "Me ake yi kuma me ake gani a Hotel din da zaki gigice haka? "

Nace 'Yan iska ke zuwa Hotel yin iskanci. Yace "Muma iskancin muka zo muyi." Na zaro idanu har zuciyata zunubi ne zuwanmu gurin nan dan haka na bata rai nayi shiru. Ya daga wayar shi sai naji ya sake furta ok. Ya bude mota, fito muje." Na ki motsi ya fita ya zagayo ya bude yace fito mana baby." Na soma zubo hawaye domin take zuciyata take fada min wai inda yake zuwa da matan banzan shi ne. Ya katse ni, ina miki magana kina jina? Da alama ya soma fusata. Cikin kuka, nace yanzu fisabililllahi in wani ya gammu yaje ya fadawa Abbanmu cewa ya ganni a Hotel tsine min zai yi fa. Ya saka hannu ya dakko ni ya rike ni kamar wata jinjira, sannan ya rufe motar ya sabani a kafa yace a haka kinga baby bawanda zai ganeki. inata wutsil wutsil ina dan kuka. Muka shiga,. Mutum daya ne a Reception na rufe ido da bayan shi wai kar yaga fuskata. Ina ta dukan bayan Shamaki, wani yana tsaye bakin wata kofa shine ya bude mana kofa sannan suka sake yin magana ya shiga ya rufe kofar ya zube ni kan gado. Na diro da sauri nace nifa bazan tsaya ba, ni ba karuwa bace. Kalmar ta fusata shi da alama. Yace karki fusata ni Baby. Nace nafison ka fusata din ko ka kai ni gida. Hajiya ma nasan yanzu tana jiranka kuma zan shafa mata maganinta a kafa.

Ya turani na fada gadon ta baya, na san a raina ni dai bazan yarda ya kwanta da ni a Hotel ba, domin hakan zunubi ne.
Ya cire kayansa ina ta kuka, ya fizgo ni, rigata ma da ta bashi matsala yagata yayi. Karfi ya nuna min ko ince Shamaki fyade ya yi min kuma har saida ya min rauni. Na kasa tashi, shi kuma juya min baya ya yi ya kama bacci. Nima dai bansan lokacin da baccin ya yi gaba dani ba. Farkawa na yi na ganshi yana salla. Na tashi zaune da sauri, sai lokacin na ke karewa dakin kallo, ya yi matukar kyau, kamata ya yi ace wannan dakin a gidan sure yake. Na tashi na sauka ina dingishin iskanci waini amin fyade, duk da ina jin zafi amma bai kai yadda na dauki abin ba. Na dube shi Nace ko isha'i bai yi ba ashe amma ya iya kawo ni Hotel Allah dai ya sani kuma bazai rubuta min zunubi ba.

Na zauna baki gado ina mitar gashi duk an jima mutum ciwo. Bini da kallo yana murmushin mugunta.
Sannan yace in kin gama mitar sai ki tashi kiyi sallar asbahi tunda kin ja mana makara gashi nan yanzu har shida ta yi. Na mike da sauri na dafa kirji nace wai kana nufin gari ya waye!? Yace "Ina wayar ki tana mota da kin duba lokaci yawwa kali agogo gashi nan. Na kalli bangon da ya nuna da sauri, take na rikice nace na soma kukan gaske da hawaye masu dumi, nace Shamaki ka kashe ni, yanzu me zan fadawa Hajiya fisabililllahi! Yace ke ki ka ja komai da kin tsaya awa daya kacal ko biyu zamu tafi, kina ta wani ihu wai ke ba karuwa bace, shikenan dan karuwanci aka gida Hotel ke ma kina cikin sahun mutane marasa fahimta, to ko a Saudiya ki ka je ina zaki sauka in ba Hotel ba?"

Na kalle shi a makka ba gidaje bane na dama kowa ya zo zai kama bide ya shiga?

Ya yi dan murmushi waye ya fada miki wannan din to a Hotel ake sauka, zaki je ki gani wa idon ki.

Sannan kuma ni mijin ki ne dan munzo nan mu dan huta sai kawai mu samu zunubi, irin ladan da muka samu a dakina ko naki irinshi ne dai zamu samu a nan.
Chapter 10 · 0% Book details