← Book details Hamshaƙiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 31

Sashe 28

Hamshaƙiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

''Yan uwanshi kuwa komai ina shawara da su wanda ya shafi su sani, abinda kuma ba hurumin su ba, ni da Shamaki zamu kashe shi mu rufe.

Bana bukatar sai an fada min Shamaki ya daina neman mata, domin mutuwar Hajiya ta saka Shamaki a tashin hankali ya kuma hankalta, macen sunna ma sai da ya manta yadda zai kusance ta bare ta banza.

Sai dai sannu a hankali sai naga ya shiga wani yanayi na damuwa, sannan yakan kebe yana waya in ya ganni sai ya maza ya kashe, wani lokacin sai inga ya zuba tagumi. Na tambaye shi in da wata damuwa ya fada min amma yace shi dai babu komai. Araina nece Dan Adam yana da mantuwa bari dai in sake caje wayar bawan Allah nan na gano ko ya koma ruwa ne.

Sakna naga an rubuta a lambar da suka yi chat, nabi chat din na karanta.

Sanka ta fara da yi masa ta a ziyyar Mahifiyarsa, sanna ta ce masa "Dama jira nayi ka dawo cikin hankalinka daga mayen mutuwar mahaifiyar ka. Zan turo maka wani Video ka daure ka kalla in yaso sai ka nemeni in kana da magana.

Sai kuwa ga Video Na bude. Na girgiza sosai har na saki wayar Allah ya sa a kan gado nake zaune bata kai ƙasa ba. Jiki na bari yake na sake dauka ina kallon yadda Shamaki yake haihuwar Uwarsa ga fuskarshi da komai yana saduwa da yarinyar. Na aje masa wayar dama ya fita motsa jiki ne,na koma daki ina tunanin wane mataki ya kamata in dauka domin fidda shi a wannan damuwar. Tunda na duba shi rokonta ya ke yi tare da fada mata cewa ta fadi duk abinda take so zai bata ta goge wannan Video kar matarsa da a halinsa su gani. Ita kuma tace "Ai ba matar ka ba,Duniya ma sai ta gani,dan bayan naturawa matarka sai kuma in tura a Internet.

Sannan tace ita shi take bukaƙa su ci gaba da soyayya. Shikuma ya fada mata cewa ya dai yin duk wani abu na sabo domin shi ba zai yi abinda za a tada Hajiya ace ta kalli abinda tabari a baya ba.
To ta bashi kwana talatin kodai ya yarda su ci gaba da Soyayya ko kuma nan da kwana talatin ya tsinci Video su yana yawo.

Dole ta tashi ta share masa wannan hawayen domin kuwa yanzu ita garkuwar shi....
.....
Gama wannan tunanin ke da wuya na tashi na kira Hassan yaron Kantin Shamaki da yake yanzu sun saba da ni, ina kira ina tambayar Shamaki ya ci abin ci kodai wani abu kamar dai yadda Hajiya kanyi, sannan Shamaki yana aiko su su kawo wani abun in ya siya kamar Zuma da dai sauran su.

Nace masa ina son ganinsa. Ya kuwa zo cikin sa`a , Shamaki ya fita. Muka zauna a falo. Nace Hassan dan Allah so nake ka kaini guri 'yan sanda zan shigar da ƙara ne. "Karan wa za ki kai kuma?" Ya tambaya cike da mamaki. Nace wata mata ce zata takura min. Yace "Anty matsayin ki a kasar nan ai kin girgimi ki je karamin ofishin 'yan sanda. Kina da kimar da zaki daga waya ki kira kwamishina ki fada masa bukatarki, yanzu dai ki fadawa maigida zai iya kiran kwamishina yana da wannan alfarmar."
Nace aiko labarin bana son yaji, yanzu dai ya ka ke ganin za a yi so nake ma ka tafi kafin ya shigo. Yace "In kuma kina son ´yan sandan farin kaya ina da wani aboki Dss ne zan baki lambarshi sai ki kira shi ki fada masa kece matar Aliyu Baita, kudi kawai za su yi aiki. Nace to ba matsala. Muka yi sallama ya tafi. Domin yanzu bani da wata damuwa akan kudi saboda ya bude min account dina kuma ya bude na harkokin gida kamar dai lokacin Hajiya. Washe gari Hassan ya turo min Number. Sai da Shamaki ya fita sannan na kira Nace masa nice matar Aliyu Ali Baita. Yace . " Ranki ya dade Hassan ya fada min zaki kira ni." Nace Yawwa wata ce take yi wa maigidana barazana zata saki wani Video na batanci a gurin sa, to ina son batare da ita da shi sun sani ba, ina dakatar da abin, Hassan yace in maka magana. Yace "Ranki ya dade maigida da kanshi kuma yabarta araye? Nace yanzu ma ba zata zan yi mishi domin shi yana nan yana lallashinta a karbi kudi to gara ku kuci kudi. Yace Angama Haiiya zan je in hadaki da oganmu yanzu."
Ya hadamu da shi nayi masa karin bayanin komai, nace masa abin da ya faru tun can baya ne yanzu baya tare da ita. Ita Kuma ga bukatar ta yanzu wai sai sun koma soyayya shi kuma yace ya ma daina gaba daya. Ogan yace "Ki turo min da Number dinta da kuma hoton ta. Take na tura masa duka saboda na ga hoton ta akan dp din ta na whatsapp na kira shi yace ya gani in jira zai neme ni.

Shamaki ya shigo dakina ya same ni muna Homework yace "Wai ina malamar Lesson din yaran nan ne ki ke ta fama da lesson?" Na ce ta bada uzri wai yau zata je wata gaisuwa shine nace ba matsala zan kula da su yau. Yace "Ya yi kyau. in an gama da su ki sameni a dakina."
Na barsu na nufi gurin shi dama akwai hanyar da ta hada ni da shi haka ma Azima ta cikin Falonmu. Na same shi yana kokarin kunna talbijin. Ya wai wayo yace " Au wai dama kina baye da ni ne? " Na ce to me zan jira in ban amsa kiran sanyin zuciyata ba. Ya yi Murmushi ya zauna, "Zonan" ya fada yana kallo na. Naje na zau a kan cinyarsa domin nasan nufinsa ke nan. Ya sulmiyo da ni ya dora hancinsa a kan nawa. "Mota zamuje ki zaba yanzu." Da sauri na zuba kwayar idanuna cikin nasa. Mota fa! Yace " To menene a cikin mota Allah na tuba. Na rungumeshi na sunbaci kirjin shi, zaka kai ni in zaba, to kuma wa zai koya min?
Yace "Samu ya fi iyawa Baby zan koya miki kafin sati kin kware. Sai muna fita dasafe a ranar asabar da lahadi. Na sake kankame shi cikin kauna.

Naje na sako Jallabiya da mayafinta nace wa su Meema Dady zai sai min mota yanzu zamuje.Suka kwashi murna nace da Juma bari mu dawo.

pShi na baiwa zabi ya darzarmin mai kyau fara kal kirar Yaris sabuwar zubi. Muka dawo gida yara sai murna duk yawan motocin gidan amma sai fadi suke Mommy zaki kaimu makaranta gobe? Nace Sai na koya.

Muna zaune da Shamaki kira ya shigo waya ta. Na tashi da sauri na fita zuwa tsakar gida. Yace Ranki ya dade zaku iya zuwa yanzu mun kama wannan matar. Nace Inane Office din? Ya yi min kwatance' nace zamu zo yanzu. Na koma na shiga na same shi, ya bini da kallo ya ga na yi abinda ban saba ba nafita waje na daga waya. Nace taso muje. Yace "Yace ina kuma da wannan daren?" Nace Yanzu zamu dawo. Ya taso yana fadin Baby bazan yi miki musu bane amma bana son fita yanzu. Na kama hannunshi yi hakuri. Kai zaka jamu bazamu fita da direba ba. Saida muka hau titi nace Office din Dss zamuje. "Mu yi me?" Ya da sauri, nace taimako? Yayi shiru har muka isa,. Shugaban yana ta kallona yana mamaki wai dashi muka yi waya,ya sa rai zaiga wata babbar mace. Nace ni ce Shamaki tunda suka gaisa sai naga ya kame guri daya,da alama bai son wannan tattaunawar da muke yi da dansandan farin kayan ko ince kishi ne ya sa shi daure fuska.
Dansandan yace Hajiya kinsan a ina aka kama matar nan? Nace a a Yace a Kaduna tunda muka sa layinta a trak muka gano tana Abuja yaranmu sun kama hanya sai kuma muka ganta a Kaduna. A Hotel aka kamata sun sha ita da saurayin ta sun bugu. wayar muka fara karba yanzu kuma sai abinda megida yace za a yi, ya dubi Shamaki yace Ranka ya dade. Shamaki wanda ya kasa gane me muke nufi ya ce "Kunsani a duhu."
Dansanda ya daga waya yace ku kawo wannan "yar iskar. Shamaki ya mike tsaye da sauri yana kallon ta. Ya nuna ta da yatsa yace Sakna. Wata zuciya ta zo wa Shamaki wuya ya daga hannu ya falla mata mari sannan ya kalle ni ida nunsa suka kawo hawaye. Na girgiza kai, nace wannan ba wata damuwa. Na kalli Dansandan nace ina wayarta? Ya miko min wayar tare da fadin ta cire cord din wayar. Na ba Shamaki nace ka yi yadda ka ke so. Yace a bata ta l goge Video da hannun ta. Nan take ta goge Sannan Shamaki yace ku bata layinta ne kawai shima in kunga dama amma ku rike wayar domin ni ne na saye ta. Sannan kar ta bar nan sai ta tabbatar muku cewa tafita harka ta. Ogan Cikin son tsorata ta yace ai kasar nan zata bari ba ta ce ita ba 'yar Najeriya bace wai 'yar Nijar ce. Na karya ta ke yi domin 'yan Nijar sun san karamci da mutunci ta dai fadi daga inda ta fito. Yace koma dai daga ina take ko dai ta koma can, ko kuma mu kashe banza mu ba karnukanmu namanta su cinye.
Shamaki yace na gode
sannan ka tura lambar asusunka zan baka sako kai da yaranka. Dansanda ya yi godiya sannan yace ka kara rike madam sosai domin a sanin da nayi wa halin mata a wannan lokacin da wahala matar ka ta ga wannan abin ta yi shiru sai ta yada ka a gurin kawayenta da 'yan gidan su, sannan ta ce ka sake ta. Shamaki yace Na gode zan kula sosai. Ya rako mu har mota.
Chapter 28 · 0% Book details