← Book details Hamshaƙiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 31

Sashe 22

Hamshaƙiya Uwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shine na fara bincikar wayar sa domin in samu tabbbain abinda naji. Anan na gano yadda suka shirya da wata yarinya zasu hadu a wani Hotal a ranar wata lahadi. Hajiya tace "To na fahimci cewa lahadin da ki ka yi karyar ciwo ce domin kar ya fita." Na jima ina tunanin dalilin wannan karyar. Na.
Ce yawwa haka ne, sai kuma ciwon duba wayar ya kamani wanda kullum na duba sai na ci karo da sabon bakin ciki wanda sai dai in shiga daki insha kuka na. Hajiya ta dube ni, ta girgiza kai, sannan tace "Wane matakin ki ka dau ka". Nace fatan shiriya nake ta yi masa a gurin Allah, kuma dai har zuwa lokacin da ya yi wa Azima ciki ina cike da tashin hankali game da zaman mu. Zubur Hajiya ta mike tsaye, ta tsura min ido, "Da wane lokacin ya yi wa Azima ciki.? "A raina nace kaji wani raining wayo. Sai nace. Ban san da wane lokaci bane amma doke zai zama a cikin lokutan da take zuwa dakin shi ne ko suke fita, bana zaton cewa ko su zasu iya sanin lokacin. Hajiya tace "Ke nan kinsan tana zuwa to kina matar shi ke kina ina? Nace Hajiya bansan tsawon lokacin da suka dauka suna yin abin su ba. Kilama kafin in zo ne, haka kuma ai suna fita Hotel kamar dai yadda ki ka datse yin hakan ta hanyar daura musu auren gaggawa. Hajiya ta zauna a bakin gado, sannan ta kure ni da kallo. "Wane kokari ki ke yi zuwa yanzu domin ganin ya bar duk wadannan dabi u.? " Na ce zuwa yanzu ya san na san komai, ban yi rigima da shi akan haka ba, kuma na fahimci Allah ne kawai zai rabashi da haka, saboda haka shi nake fadawa, ina saran zai shirya shi lokaci daya. Sannan ina kokari fita hakkin shi yadda ba zai zama cikin bukata ba sai dai wani abu na sharrin shaidan.
Hajiya ta kada kai cikin gamsuwa. Sannan tace, bazaki nemo wani taimako ba ga masana domin hana shi aikata duk irin wannan biye biyen? " Nace Hajiya Allah shine mafi girman mai bada taimako nasan zai yi haka, sannan bazan tauye shiba in yana da bukatar sake aure fa tunda na karanta a wani group cewa maganin hana maza su nemi mata wani sihiri ne sai dai su tsaya ga ke kadai in sunje gurin wata baza su iya yin komai da ira ba. Hajiya ta ce je ki hau gadonki ki kwanta zamu dora gobe,. Saura kwana uku jara bawarki. Kin yi kokari sauran tun a text suka fadi,. Na kalle ta, ba wannan ce Jarabawar ba? Tayi murmushi Ai kin san kafin Jarabawa ana yi Text ko? Ban iya amsawa ba har sai da na kai kofar fita na waiwayo nace sai da safe. A daki ina kwance in tunani in har wannan text ne to ya jarabawar zata kasance?

*💃🏻💃🏻💃🏻Masoya masu jiran littafin HAMSHAKIYAR UWA Complete Document,a yanzun haka ya kammala akwai document din HAMSHAKIYAR UWA Complete game bukata zai iya tura kudi kai tsaye ta wannan account number ₦600👇🏻*
*0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn*
*Phone 08140004302*
.....
Da safe bayan na yi salla na koma bacci saboda zaman cikin dare da muka yi da Hajiya Bacci mai nauyi ne ya sani na makara. Kwankwasa kofar da Juma ke yi shine ya farkar da ni, ashe wayar cikin gida ta jima tana ruri amma ban ji ba saboda bacci.

Na tashi da sauri na bude kofar Juma ce nace lafiya Juma na ganki da sassafe? Tace ni da matter gidan muka taho, Hajiya ta kira mu. " Nace har na zaci ko haihuwar ce. " ta ce a a, lafiya baki fito ba? Nace lafiya lau. Tace Hajiya tana neman ki, na shiga ban daki na yi fitsari sannan na fita. Hajiya bata falo na shiga dakin ta. Tana zaune akan kujera ta nuna min wani akwatin ga kayan ta a kusa da akwatin tace, " Shirya min kayan nan a cikin jakarnan. Yawanci dogayen riguna ne marasa nauyi, sai wani farin yadii wanda lokacin da na dago shi sai da gabana ya fadi, duk da cewa bansan likkafani sosai ba, ba shakka shine wannan. Sai wasu turaruka da kuma ganyan magarya. Na gama tsaf. Tace "Kin karya? Nace 'a 'a, tace kije ki karya sai ki zo. Nace Hajiya bana jin yunwa. Haka nan naji duk firgici ya kamani. Tace to inje in shirya kayana kamar kala biyar a karamin akwatina in zo. Na shiga uku, Hajiya kodai gida zata maidani ne! Ko yaya abin ya ke? Na tambayi kaina, amma bani da amsa.

Na yi yadda tace. Na dawo nace Hajiya na shirya. tace in kira Juma na kirata, tace in fita suka gama magana tukunna. Na fita Juma ta fito. Nace. Wai Juma ya na ganki a nan? Tace za kuyi tafiya ke da Hajiya. Ni da Azima ne muka dawo nan na fada miki tun dazu. " Mamaki ya kamani amma sai na yi shiru. Na koma dakin Hajiya. Tana rubuta wata takarda ta gama. Sannan ta amsa wayar da aka kira ta ana fada mata ce karfe daya jirginmu zai tashi, tace kije za a kai ki a yi miki passport yanzu ai kina da Karin zabe ko? Nace sai na dan kasa, tace duk daya kije dashi in kin dawo ki ci abinci kiyi wanka ni kuma zan dan saka kalle a kafa da hannu kafin lokacin. Ki kira Ummarki ki fada mata zamuje India baifi muyi kwana bakwai ba. Nace to. Muka fita da direba zuwa Immigration office, wanda mukaje gurinshi ya ce, maimakon Hajiya ta turo aje ayi miki har guda. Nace ba damuwa ai duk daya ne. ko a wa daya banyi ba na dawo da ID card dina na fita kasashen duniya, wanda ni ban ma san wai dai anyi shi sannan za a fita wata kasa ba.

Na ci abinci sama sama, ina ta yin tufka da warwara, domin bansani ba ko jarabawar acan za a yi ta . Na shirya tsaf sannan na kira Umma na fada mata zamuyi tafiya zuwa kasar India da Hajiya. Ta yi addu'a Allah ya sa mu je lafiya mu dawo lafiya.
Na samu Juma a kicin nace wai ni abinda ya daure min kai, naga Hajiya ta saka likkafani da gayan magarya a jar tafiyar ta. Juma tayi dariya, tace to ai ita Hajiya ko Zamfara zataje sai ta tafi da wannan guzirin nata, tun muna tunanin in ta tafi bazata dawo ba har muka saba muka dai. Na sauke Ajiyar zuciya nace har na tada hankali na wallahi. Tace "Dan tafiya bata taba hada ku lokaci daya bane.

Na sake shiga gurin Hajiy sai yanzu ta fara saka lalle Tace ani naki ya yi sauri,. " Nace haka ne, na amshi lalle ina saka mata. Tace inyi mata sukuf gaba daya, nace tsohuwa ta fada kwanta da na miki irin lallben da ki ke yi. Tace "Kayya zamu bata lokaci kinsan jirgi baya jiran kowa. " Nace to shikenan,
Tace amma baki sanar da mijinki cewa zamu yi tafiya ba ko?"

Nace ai baki ce in fada masa ba ne shiyasa. Tace Yawwa ina jin dadin yadda baki da gaggawa da rawar kai. bana son ya sani har sai mun dawo." Nace kuma ba laifi inna tafi babu izninsa ko? Hajiya ta dube ni,. "Har yanzu baki yarda cewa kai da kaya duk mallakar wuya bane kenan? " Nace na yarda mana.

Karfe daya saura mukayi salla, Hajiya ta sa aka kira kowa kamar yadda ta yi lokacin da za su tafi aikin Hajji. Ta shafa kan kowa tace na yafe muku kuma ku yafe ni. Duk aka yafi juna nima nace a yayyafe. Daireba ya jamu zuwa filin firgi. Mun samu wasu mutane guda biyu wadanda nake zato ko lauyoyin ta ne, amma ba wadanda na sani bane masu zuwa gida, ko kuma sune ban gane su bane oho.

Tare da su muka hau jirgi zuwa
Legas daga can muka rabu da su bayan sun yi wata ganawa ta musamma da Hajiya na misali minti talatin zuwa. dare aka kwashe mu zuwa India. Duk a tsorace nake domin ban taba hawa Jirgi ba, daga Kano ma da zamu ta so sai da na kama hannunuwan Hajiya na kankame, ji nayi kamar hanjin cikina ne zai koma kirji. Salati kuwa da na kama sai da Hajiya ta girgiza min kai tana fadin ki samu nutsuwa addu'a a hankali ake yinta. To da zai tashi daga legos kuma sai naji kamar zanyi amai kafin daga bisani na daina ji sai kuma fargaba da tsoron Allah. A zuciyata nace ganin damar Allah ne faya sa jirgin nan ya fadi da mu, gaskiya Ubangiji yana son bayinsa. Na shiga istigfari ga shi na shigo duniya bada iznin mijina ba. Koda yake mahaifiyar sa ce ta gayyace ni. Naji an kama hannuna a hankali na daga ido na kalli Hajiya wadda ta tsura min ido, tace Rabi 'atu tsoro ki ke ji ne? Nayi dan murmushi nace Tsoron Allah ne ya yake ratsa zuciya ta. Tace kar ki damu haka duk wanda bai saba hawa jirgi ba ya ke fuskanta. Ki kwantar da hankali. Ta sake sauke ajiyar zuciya, sannan tace, "Zan dora miki wani nauyi wanda Allah shine ka dai wanda zai taya miki. " Na ce na am! Hajiya cikin mamaki da fargaba nayi maganar, tace "Zan baki amanar Aliyuna. Na ma manta waye Aliyu. Nace waye kuma Aliyu? Tace "Shamaki nake nufi. Na zaro ido, tace na baki amanar 'ya'yan Shamaki."
Nace me yasa zaki bani amanar su banyan muna nan tare da ke su kuma suna gida? Tace "Zan baki dama ki min tambaya amma sai mun isa can zaki tambayi duk abinda ki ke so. Cikin tsanaki. Ta sake rike hannu na Na baki amanar Azima kar kiyi amfani da son da Shamaki yake miki ki cutar da ita ki yi mata adalaci kar ki bar kishi ya yi tasiri a zaman ku.
Chapter 22 · 0% Book details